← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 169 OF 197

Sashe 169

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

babyn nata ke ciki, miƙewa Salma ta yi tare da ɗan kallon aunty ta ce mata sai da safe, aunty dake kallonta cike da kulawa ta ce ko ta kwanta a nan, Salma ta ce lafiya lau zata koma ɗakinta, sai da aunty ta rakata har ɗaki ta ƙara kwantar mata da hankali, bayan ta saka ta ta kwanta ta dawo ɗakinta duk itama ta shiga damuwa, a wannan daren bacci kusan ƙaurace ma Salma ya yi saboda damuwa da kuma zullumi da suka cika ta. Washe gari bayan sun yi breakfast aunty ta tafi aiki, haka Salma ta yi ayyukan gidan duk ta yi wani sukuku da ita. Wuraren la'asar aunty ta dawo, Salma ta tarbe ta tare da yi mata sannu da zuwa, a nan falo suka zauna aunty tana kallon ta da murmushi ta ce, "Sannu da gida baby." Salma ta amsa da ɗan murmushi, "Yau kin ga ban dawo da wuri ba ko, baƙi muka yi a asibitin namu, mai kama da ke tare da tawagar ta suka kawo mana ziyara shiyasa ban baro asibitin da wuri ba." Salma ta ɗan yi murmushi don ta gane matar gwamnan garin take nufi wato hajiya Aisha, ita ce ta ta6a bata kyautar kuɗi lokacin da ta gama primary a nan Kaduna, lokacin mijinta yana riƙe da muƙamin kwamishinan ilimi, yanzu kuma shine governor ɗin garin, ƙoƙarin miƙewa Salma ta fara tana faɗin bari ta kawo mata abinci, aunty ta ce, "Anya bar abincin nan, yanzu bana jin wani yunwa sosai sai dai ko anjima." Salma ta koma ta zauna tare da sauke kanta, kana ganin ta ka san tunani take dama daga jiya zuwa yau aikin da take ke nan, aunty ta bi ta da kallo, a hankali ta kira sunanta, Salma ta amsa tare da ɗagowa, "Har yanzu baki daina damuwan ba ko, ba na ce ki kwantar da hankalin ki ba." Salma ta ƙaƙalo ɗan murmushi a sanyaye ta ce, "Ba tunani nike ba aunty." Aunty ta yi shiru tana kallonta, tausayinta take ji a rai don ta fahimci son Deen ya yi mata mugun kamu, can ta miƙe tana faɗin bari ta je ta watsa ruwa, Salma ta ɗauki jakarta suka nufi ɗakinta, bayan ta kai mata jakan ta fito ta nufi ɗakinta, zama ta yi a saman gado ta yi shiru tana kallon wuri ɗaya, tun jiya ta kasa hawa social media saboda tana fargabar ta ga Deen da Basma, tana ta zaune can ta miƙe walking slowly ta nufi toilet, bata daɗe ba ta fito ta ji wayarta na ta ringing, gado ta nufo inda wayan take ajiye, sai dai kafin ta ƙaraso kiran ya yanke, zama ta yi ta kai hannu ta ɗauko wayar, kusan ƙamewa ta yi bayan da ta duba ta ga wanda ya kira ta, da gaske Deen ne ya kira ta ko kowa dai kiran nashi ne ke mata gizo, bata gama tantacewa ba sai ga wani kiran ya shigo, gabanta ne ya hau bugu ta bi kiran da kallo kaman ba zata ɗaga ba saboda zullumin da ya kama ta na abun da zai faɗa mata idan ta ɗaga, sai da kiran ya kusa katsewa ta kai hannu a ɗarare kaman mai jin tsoro ta ɗaga tare da kai wayar kunne, ta yi shiru ƙirjinta na bugawa da ƙarfi, saukar muryarsa ta ji ya yi mata sallama, ɗan runtse ido ta yi jin sautin daddaɗar muryar tasa a cikin kunnen ta, a hankali ta amsa sallaman ta ce, "Ya Deen ina yini." Bai amsa ba ta ji ya ce, "Salmerh." murya ƙasa ta amsa, ya ce mata, "How are you?" Ta amsa da lafiya lau, ɗan shiru ya yi sai kuma ta ji ya ce, "Is everything alright?" Ɗan yamutsa fuska ta yi lokaci guda ƙwalla suka fara taho mata, da ƙyar ta ce mashi eh, da alama ya fahimci wani abu daga muryarta ya ce, "Wani abu na damun ki ne?" Ta girgiza kai kamar yana ganinta sai kuma ta ce, "A'a, ba abun da ke damuna..." Ya furta ok, sai kuma ya ce, "I'm sorry bamu yi magana ba kaman yanda na ce, I have been so busy, na bari ne in samu natsuwa sosai." Ta ɗan jinjina kai har lokacin cike take da fargaba, a hankali ta ce mashi ba komai, ya ce, "Are you still in Kd?" Ta ce mashi eh, ta ji ya ce,"Ok, send me your address, zan zo in gan ki in two days" Ƙirjinta ya yi wani bugu da ƙarfi jin abun da bata yi zaton zata ji daga gare shi ba, da alamun mamaki ta ce, "Nan zaka zo?" Ya ce, "Yea, idan kina available." Ta yi shiru duk mamaki ya kama ta, "Ko baki so in zo ne?" Ta ji ya faɗa, da sauri ta ɗan girgiza kai ta ce, "A'a ya Deen...ina so." Calmly Ya ce, "Sai na zo. I love you." daga haka ya yanke kiran, Salma ta yi saurin rintse idanunta jin yadda kalmar I love you ɗin ta ratsa dukkan sassan jikinta, ciro wayar ta yi daga kunnenta, a hankali ta buɗe idanunta tana bin screen ɗin da kallo, ta rasa farin ciki zata yi ko kuwa, don still zullumin da take ji na nan, bata san idan ya zo mi zai ce mata ba, ko hakuri zai bata ya ce yana da wadda zai aura, wannan tunanin ya sa ta jin fargaba game da zuwan na shi, sai dai kuma ta wani bangaren tana jin farin cikin zuwan da zai yi, saukowa daga gadon ta yi ta nufi ƙofa don ta je ta faɗi ma aunty, lokacin da ta shiga cikin ɗakin, aunty na zaune a gaban dressing mirror ta gama sharce sumarta da ta kawo mata har ɗan wuce kafaɗa, ganin Salma ta dakata da ƙulle gashin tana kallon ta, Salma ta ƙaraso kusa da ita ta tsaya tana ɗan murmushi, aunty na ganin haka ta yi saurin cewa, "Ko ya kira ne?" Salma ta ɗan ɗaga mata kai, aunty ta washe baki dama tun da ta ga tana murmushi ta san bai wuce shine ya kira, "To ya ku ka yi da shi?" Ta tambaya tana kallon ta, Salma ta faɗi mata, aunty ta wani kalan zaro ido cike da mamaki ta ce, "Wai da gaske nan zai zo?" Salma ta ɗaga mata kai ta ce haka ya ce, aunty ta hau jinjina kai ta ce, "Lalle! Ki ce ban ga ta zama ba zamu yi babban baƙo haka, kika ce jibi ya ce zai zo?" Salma ta ɗaga mata kai, aunty ta ɗan yi shiru tana ta kallon Salma da itama ke kallon ta, "Kaina ma duk ya ƙulle na rasa da me zamu fara... miƙo mani wayana gata can saman gado." Bayan Salma ta kawo mata wayar, ta shiga latsa ta tana faɗin yakamata a yi mata gyaran jiki yau da gobe, kira ta yi ta kai wayar kunne, bayan an ɗauka tana murmushi ta ce, "Wa'alaikumus salam...sis Naja'atu ya gida ya su noor. Dama wai baby ce nike son zan kawo a yi mata gyaran jiki yau da gobe, ban san ko za a samu ba." ɗan saurarawa ta yi kafin ta ce ok lafiya lau suna hanya, bayan ta cire wayan ta kalli Salma ta ce, "Ai ba abun da kike yi yanzu ko?" Salma ta ce mata eh, aunty ta ce to ta shirya za su fita yanzu, Salma ta amsa har zata juya sai kuma ta dakata ta ce, "Aunty baki ci abincin ba, ko in zubo maki ki ci kafin mu tafi?" Aunty dake faffaɗan murmushi don ta ji daɗin kiran da Deen ya yi saboda Salma ta ce, "Ai bar abincin nan kawai baby, je ki dai ki shirya." Salma ta amsa da to tare da nufar kofa, itama aunty miƙewa ta yi don ta shirya. Bayan sun hau hanya aunty na a driver seat, Salma na zaune a front seat jikinta sanye da abaya, "Amman baby kaman mi kike ganin zamu yi na tarbar sa?Ina nufin abinci, ko kin san abinciccikan da ya ke so?" Salma ta kalli aunty da ta yi tambayar idanunta akan hanya, shiru ta dan yi tana kokarin tuna ko akwai abincin da ta san yana so, maganar da hajiya ta taba yi ta ce in dai ana cin abu ya yi masa dadi to zai ci, Salma ta ce, "Komai yana ci in dai ya yi masa dadi, haka na ji kakarsa hajiya ta ta6a faɗa...amman yana son awara sosai har da ma fara." Aunty ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "Wani irin fara kuma, shi ɗin ne yake cin fara?" Salma ta yi yar dariya ganin yadda aunty ta yi ta ce mata eh tare da bata labarin awara da fara da ta rinƙa kai masa lokacin a Funtua, ɗan kyabe baki aunty ta yi tana driving ta ce, "Amman dai ta ya za a tarbe shi da wani fara, har gara ma awaran....bari idan na ajiye ki gidan sis Naja'atun zan wuce kasuwa kawai in siyo abubuwan da za yi amfani na abinci, daga nan sai in haɗo da waken suyan." Salma ta ɗaga kai ta ce ita zata yi awaran, aunty ta ce, "Yadda idan ya zo zai ji kina ta ƙaurin murhu ko." Salma ta yi dariya ta ce ai ba ranan da zai zo za a yi ba sai a yi gobe a ajiye a fridge, "To ke nan ma gyaran jikin banza za a yi maki tun da zaki ƙare a bakin murhu," Salma na murmushi ta ce ai tun da ba wani mai yawa za a yi ba lafiya lau zata iya yi a gas, aunty ta ce mata ba wani aikin awaran da zata yi ta bari akwai matar da ke yi a nan unguwarsu lafiya lau tana da tsafta sai a bata ta yi. Bayan sun iso gidan sis Naja'atun, aunty ta ce ma Salma ta shiga ta faɗa mata ta wuce kasuwa sai ta dawo...wajen Magrib aunty ta koma gidan sis Naja'atu, bayan ta shiga a falo ta iske yarinyar sis a zaune tana kallo ta ce, "Aunty Kubra ina yini." aunty da ke murmushi ta ce, "Lafiya lou Noor my daughter, how's school?" Ta amsa
Chapter 169 · 0% Book details