← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 197

Sashe 122

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read

ta kai hannu zata tura ƙofar sai ta ji ta a kulle, dama tun da Leemarh ta ji hajiya ta ce zata yi magana da su ta rufe ƙofar sanin abun da zai iya biyo baya, buga kofar ta shiga yi tana ce ma Leemarh ta san tana jin ta ta buɗe ƙofar idan ba haka ba ranta sai ya 6aci, Leemarh dake kwance saman gadonta tana tura baki a ranta take faɗin Allah bazata buɗe ba, ƙarshe mom da ta gaji da knocking ta yi ƙwafa da ƙarfi ta furta, "Zamu haɗu ne!" Daga haka ta bar wurin, sosai ranta ya 6aci don bata ƙaunar Leemarh ta je Funtua don ta san har da saboda Fahad ya sa ta tsiri cewa zata je hutu can.....
Chapter 122 · 0% Book details