← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 197

Sashe 159

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bayan fitowar Sapna daga ɗakin Basma, 6angaren Maleek da ke nan sama ta nufa, ganin bata ganshi a nan ba ta fito ta sauka downstairs, part ɗinsa na nan ƙasa ta nufa bata gan shi a cikin falon ba, tana shiga bedroom ta iske shi a kwance saman gado, sai dai ba bacci yake ba don tana shiga suka haɗa idanu, yana dai kwance ne kawai duk abun duniya ya ishe shi, gaba ɗaya ji yake duniyar babu daɗi, farko a falo ya fara zama ya ji kamar yana akan ƙaya, shine ya taso ya dawo bedroom ya kwanta, itama dai kwanciyar ya yi ta ne kawai amman ba don yana jin daɗinta ba. A bakin gadon gefensa Sapna ta zauna suna kallon juna, yunƙurawa ya yi ya miƙe zaune cikin sanyin murya ya ce mata sannu ta ɗaga masa kai, shiru suka yi na ɗan lokaci, cikin raunin murya Sapna ta ce, "Na san wannan abu ne mara daɗi ya same mu da dole mu shiga damuwa, amman ba yadda zamu yi, mu ɗauke shi a matsayin ƙaddara..." Dakatawa ta yi tana share ƙwallan da suka zubo mata, hannunta guda Maleek ya kama ya ce, "I'm sorry da ban sanar maki ba tun farko, na yi gudun kada hakan ya ja ki faɗa mummunan hali, shiyasa na yi maki dubara ta yadda kema zaki saka mata ido, to ashe hakan ma duk a banza." Ɗan girgiza kai ta yi irin na takaici, sai dai tana jin inda tun farko ta sani to sai ta fi saka mata ido sosai, "Daga wurin babyn nike yanzu, mun yi magana da ita na tambaye ta ta faɗa mani gaskiyar yadda aka yi ta koya hakan...ta ce she just felt
like doing it, na tambaye ta duk abun da take so da zai sa ta daina aikata haka...ta ce mani aure take so a yi mata da Deen..." Tun da ta fara magana Maleek ke bin ta da idanunsa da sukai ja sosai, ta ci gaba, "I think she has a high se*ual drive...ina ganin tun da already dama akwai maganan auren a tsakanin su a yi mata auren kawai shine mafita." Ta ƙare maganar a sanyaye, Maleek kamar ba zai ce komai ba, can ya ɗan juyar da fuskarsa ya koma yana kallon wani 6angare daban, ita dai tana ta kallon shi...bayan ɗan lokacin ta ambaci sunan shi ya juyo ta ce why ya yi shiru, motsi bakinsa ya fara yi yana ɗan kikkafta idanu kafin ya fara magana, "...Ina ganin su biyun yanzu basu dace da auren juna ba...ko da ba tare nike yin rayuwa da Deen ko yaushe ba, ina da yaƙini kan sa cewa baya aikata duk wani abu da yake haramun, to taya zamu haɗa shi aure da ita mun san tana aikata wannan halin?" Ya ƙare maganar tare da kafe ta da ido, wani irin faɗuwa gaban Sapna ya yi jin abun da ya ce, fuska a jagule ta ce, "Amman honey... shi da ita duk matsayin yaran mu suke, kuma bada son ran mu hakan ya kasance ba, kawai ƙaddara ne Allah Ya aiko mana." Maleek ya ɗan ɗage gira ya ce, "Don yana matsayin ɗan mu sai mu cuce shi? Ki ɗauki kan ki a matsayin mahaifiyar da ta haifesa, sai kika ji yana neman auren yarinyar da take aikata irin halinta a zuwan ba ɗiyar ki ba, shin zaki amince ya auri yarinya irin haka?" Sapna ta yi shiru tare da haɗiyar wani busasshen yawu, cikin ƙoƙarin fahimtar da shi ta ce, "....amma honey wannan duk abu na gida ne, kuma ba don mu cuce shi zamu yi masa hakan ba, shi ɗin matsayin ɗan'uwanta yake, koda ya san da tana aikata hakan zai iya rufa mata asiri ya aure ta." Ɗan murmushin takaici Maleek ya yi ya ce, "Sai su yi wani irin zaman aure?" Sapna ta ɗan kikkafta idanu sai kuma ta ce ai yanzu ba sani ya yi ba, Maleek ya ce, "Idan kuma bayan auren ya zo ya gane tana aikata hakan fa?" Shiru ta ɗan yi kafin ta ce, "Honey zata bari, ita da kanta ta faɗi hakan." Ɗan girgiza kai ya yi ya ce, "Farko dana fara kama ta tana aikata hakan the same abun da ta faɗa ke nan cewa ta bari, ba irin alƙawarin da bata yi mani ba, but ta bari ɗin? A lokacin ma ke baki san da hakan ba, yadda ta nuna tsoron bata son ki sani I thought ko shi zai sa ta daina aikata haka. We should not be selfish Sapna, ana yin aure don samun kwanciyar hankali, za mu cuci Deen idan muka aura masa ita ya zo ya san tana aikata hakan, wani hali kike tunanin zai shiga sanin wace irin mata ya aura? sannan auren ta da Deen ba lalle ya zama mafita ba, saboda yanayin career ɗinsa da ba kowane lokaci zai rinƙa kasancewa da ita ba, ƙarshe hakan zai rinƙa bata dama ne tun da gashi just sati ɗaya da bana a gidan ta samu daman aikata haka, to ina kuma ga Deen da sana'arsa ta yawan yin tafiya tafiye ce." Ya ƙarasa tare da rufe idanunsa ya ɗan ɗage kansa, idanun Sapna suka cicciko da ƙwalla, ita ba don wani abu take son auren nasu ba sai don hango masu mafita, kuma ba don tana son su cuci Deen bane, kawai tana ganin hakan matsayin ƙaddara, kuma tun da Deen ɗin ba sani ya yi ba a ganinta lafiya lau za su haɗa su auren, ta sigar rarrashi ta ce, "Honey..ka fahimce ni, ni ina ganin hakan ne kawai mafita... tun da dama shine zata aura kuma bai sani ba lafiya lau zamu iya masu aure." Shiru kamar ba zai tanka mata ba still idanunsa na a rufe tana ta kallon shi cikin marairaicewa, ba tare da ya buɗe idon ba ya ce, "Ke kike ganin hakan a mafita, amman ko an yi masu aure abubuwa ne za su ƙara lalacewa indai bata bar wannan halin ba..." Slowly ya buɗe idanunsa suka shiga cikin na Sapna, on a serious note ya ci gaba, "....In dai bata bar wannan halin ba ba zan ta6a goyon bayan ta auri Deen ba, don haka sai na tabbatar cewa ta daina ko zan amince ma auren su." Yana gama faɗin hakan ya zura ƙafafunsa ya sauka daga saman gadon ya nufi toilet ya shige, Sapna ta bi sa da ido gabanta na faɗuwa sosai, bayan ɗan lokaci ya fito fuskarsa duk ruwa da alama wanke ta ya yi, wurin side drawer ya nufa ya buɗe, hanky ya fiddo tare da makullin mota, bayan ya ɗauki wayarsa ya ɗan kalli Sapna ya ce mata ya fita daga haka ya wuce, ita dai da ido kawai take ta bin sa har ya fita daga ɗakin, ƙwallan da suka tarun mata ne suka fara zubowa, sam bata yi tunanin Maleek zai ƙi amincewa da maganar auren nasu ba, gashi ta san shi wani lokacin kaifi ɗaya ne a magana, yadda ya yi maganar ta hango har cikin ransa ne, yanzu ita ya zata yi? haka ta yi zaune a wurin kamar an dasa ta tana ta tunane tunane, da ƙyar daga baya ta yi ƙarfin halin miƙewa ta nufi ƙofa tana jan ƙafafu don tuni har zazza6i ya rufe ta.
Chapter 159 · 0% Book details