Sashe 68
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sai kuma ta ɗaga mata kai alamar eh, still murmushi ne akan fuskar innarsu ta ce mata ai da yake sumar tata bata danƙarewa idan an barta a kwance ta sha gayun ta, dariya Salma ta yi ta ce, "Ke yaushe zan taya ki ki kwance naki?" Hannun hagunta ta kai ta kamo jelar kitson kanta guda ta ce ma Salma ya tsufa ko ta ɗaga mata kai alamar eh, innarsu ta ce, "To ni ai gashi na ba wani mai uban yawa bane zama ɗaya ma sai in kwance." Salma ta ce, "Duk da haka kema innnarmu kina da gashi tunda idan kika kwance har wuce kafaɗarki yake, kuma kema da za a yi maki wash and set ɗin ko saloon na san zai ƙara tsawo sosai." Innarsu ta ce, "Kai ni kyiwur zuwa shago nike a wanke mani kai, kuma nima bana yin saloon, ina ga sau ɗaya na ta6a ƙona sumata tun lokacin bikina da baban ku shima soda ce aka saka mani duk da lokacin gashina ya fi haka tsawo." Dariya Salma ta guntse jin ta ce tun bikinta da abbansu, itama innar tasu dariya take ta ce mata ta je ta kai mata yamma na yi ta gaishe mata da hajiya ta amsa da to tare da miƙewa, innarsu ta bita da kallo ya yin da ta nufi ƙofa har ta fita. Bayan Salma ta shiga cikin gidan, a cikin harabar daga can gefe ta hango Balaraba a bakin famfo tana wanke wasu manyan robobi, nufar inda take ta yi bayan ta isa kusa da ita ta ce, "Aunty Balaraba ina wuni." Balaraba da ta ɗago tana kallonta da murmushi ta ce, "Lafiya lau Salma, ya su innar ku?" Ta amsa mata da suna lafiya, "Ma sha Allah Salma kin yi kyau." Balaraba dake ta kallonta ta sake faɗa, tana murmushi ta ce mata ta gode kafin ta kai hannu cikin ledan ta fiddo roba guda ta fara ta ce mata ga shi, goge lemar hannunta ta yi ta amsa tana faɗin farar ce har ta soya, buɗewa ta yi ta ɗan de6o ta kai baki, bayan ta cinye ta ce, "Salma kin iya soya fara, ta yi daɗi sosai wllh." Salma dake murmushi ta ce mata ta gode, tambayarta ta yi ko hajiya na nan ta bata amsa da eh tana cikin gida ta shiga, tana shiga cikin falon ta ja ta tsaya sakamakon hango Deen da ta yi a zaune yau ma ya maƙala headphones a kunnansa hannunsa riƙe da controller da alama yau ma game ɗin yake yi, kasa shiga ciki ta yi saboda ganinsa da ta yi ba riga jikinsa sai wani neck scarf da ya rataya a wuyansa ha6ar ta rufe masa gefe da gefen ƙirjinsa sai wando 3-quarter, haka nan ta ji nauyin ta ƙarasa tana niyyar juyowa ta fito kawai ta ga ya juyo fuskarsa inda take suka haɗa ido, bin ta da ido ya yi ta shiga ƴan kame kame, ba yadda ta iya haka ta ƙarasa shiga cikin falon ta tsaya daga ɗan nesa da shi tana sauke idonta ƙasa, a hankali ta ɗan ɗaga ido ta ce masa ina wuni ya ɗaga mata kai, shiru ta yi batare da ta ƙara cewa komai ba idonta na kallon gefe, "Hajiya?" Nutsattsiyar muryarsa ta sauka a kunnanta, kallonsa ta yi tare da ɗaga masa kai, idonsa a cikin nata ya ce, "So you want to turn me into the one who has to call Hajiya every time you come, right?†Ya yi maganar tare da ɗage mata gira, rass ta ji gabanta ya faɗi da tunanin ko ya fara gajiya da zuwan da take yi gidan, cikin ƴar rawar murya ta ce, "Ka yi haƙuri, bari in tafi ko anjima idan ta fito na dawo." Tana faɗin hakan da sauri ta juya zata nufi kofa, "Hey..." Ya dakatar da ita ta juyo suka haɗa ido, ɗan murmushi ta ga ya yi calmly ya ce, "Just kidding...let me call her for u." Daga haka ya miƙe idonta akansa, yana juya bayansa zai nufi part ɗin hajiya ta yi saurin janye idonta don muscular jikinsa tsoro yake bata, ba a jima ba ya dawo tana jin dawowarsa bata kalle sa ba, ya koma wurin da ya tashi zai zauna ta ji ya ce hajiya tana toilet sannan ta ɗaga ido ta kalle sa tare da ɗaga masa kai, ci gaba da yin game ɗinsa ya yi after some seconds ya juyo suka haɗa ido ya ce mata ta zauna a hankali ta matsa kujeran kusa da ita ta zauna, kallon game ɗin ta ci gaba da yi tun bata fahimta har ta ɗan fara gane kan game ɗin daga yanayin da Deen ke nunawa akan fuskarsa idan ya yi winning, after some minutes hajiya ta shigo cikin falon, a kujeran da ta saba zama ta zauna Salma na kallonta ta ce, "Hajiya ina wuni." Fuska sake hajiya ta ce, "Lafiya lau Salam, ya ƴan'uwanki?" Ta amsa mata suna lafiya, ta ɗaga mata kai kafin ta kai idonta kan game ɗin da Deen ke yi, hannu Salma ta kai cikin ledan da take riƙe da, robar fara ta fiddo da ɗan murmushi ta miƙa ma hajiya ta ce, "Gashi hajiya." Kallon abun da ta miƙo mata ta yi ta ce, "To..mi na samu haka?" Salma ta ce, "Fara ce na kawo ma aunty Balaraba, shine kuma na kawo maku." Hajiya tana murmushi idonta akan robar farar ta ce, "To na gode, sai dai bansan ma yanzu ko zan iya cin fara ba saboda haƙora ba ƙwari abu kaɗan sai su fara ciwo." Ta yi maganar tana ƙoƙarin buɗe robar, ƙamshin faran ne ya bugi hancin ta ta ce, "Ma sha Allah, tun ban ci ba ma na san ta yi daɗi." Ta faɗa tana murmushi, kai da gangar jiki na farar ta fara ɗauka tana ci ta ce bazata ci cinya ba kada ta soke ta, Salma dake kallonta murmushi ne akan fuskarta na jin daɗin ganin tana cin faran, ruƙus-ruƙus ɗin tauna farar da hajiya ke yi da kuma yadda take ta yaba daɗinta su suka jawo hankalin Deen ya ɗan juyo ya kalle ta, tana kallon sa ta ce, "Ko zaka ci ne?" Ta ɗaga robar tana nuna masa, bin robar faran ya yi da kallo kamar bai fahimci abun da hajiyan ta ce ba, miƙa ma Salma robar ta yi ta ce ta kai masa, tana ɗan murmushi ta ce mata ai shima ta kawo masa hajiya ta ce to ta kai masa a ga in zai iya ci, miƙewa ta yi ta isa gabansa ta kai hannu cikin ledan ta fiddo wata robar fara ta miƙa masa tana murmushi, bin robar da take bashi ya yi da kallo kafin ya ɗaga ido ya kalle ta alamar bai fahimta ba, ta sake ce masa fara ce soyayya ta kawo masa, hannu ya kawo ya amshi robar ya buɗe, hajiya dake kallon Deen dariya ce akan fuskarta ganin yadda ya yi duruduru yana kallon farar kamar wanda ya ga wani abun tsoro, ta ce, "Spicy fried grasshoppers ce ka ci." Ɗagowa ya yi ya kalli hajiya da idanunsa tubarkalla, "Dama ana cin shi?" Ya jefa mata tambaya, still da dariya akan fuskarta ta ce, "Eh mana, da ba a ci zaka ga nima na ci, kuma tana da amfani sosai a jiki." Shiru ya yi ya maida idonsa kan farar yayin da ƙamshinta ke ta bugun hancinsa, kuma ƙamshin ya yi masa daɗi, ɗago ido ya yi ya kalli Salma da har lokacin take a tsaye tana murmushi, slowly ya ce mata ya gode ta ɗaga kai ta dawo inda ta tashi ta zauna, tana ta kallon shi don ganin ko zai ci farar da ya riƙe shi bai fara ci ba bai kuma rufe ba, after some seconds ya kai hannu ya ɗauko part guda na faran ya riƙe yana kallo kamar mai jin shakkar ci can dai ya kai baki, slowly ya fara taunawa har ya haɗiye, hannu ya ƙara kaiwa ya ƙara ɗaukowa ya sa baki, Salma dake kallonsa murmushin daɗi ne ya su6uce mata ganin yana ci, "Ka maida mana kallo tun da mu ba fahimtar game ɗin muke ba." Hajiya ta faɗa idonta akan tv, after a while Salma dake kallo ta ji hajiya ta ɗan ta6a mata hannu da sauri ta kai idonta kan hajiyar, tana ɗan murmushi da hannu ta yi mata nuni da Deen ta yi ƙasa da murya ta ce, "Kalli mutumin ki da kamar ba zai ci farar ba." Kallon saitin shi Salma ta yi ta ga yana ta cin farar a nutse kuma da alama ta yi masa daɗi, maido idonta ta yi kan hajiya tana murmushi ta ce ita bata ma yi zaton zai iya ci ba, hajiya dake ƴar dariya ta ce, "Wanccan hamburum burum ɗin, ai in dai ana cin abu kuma ya yi masa daɗi to zai ci." Faffaɗan murmushi Salma ta yi, sosai ta ji daɗin cin farar da ya yi, Balaraba ce ta shigo cikin falon ta nufo inda suke, hajiya ta ce, "Balaraba kin ganni ina cin fara Salma ta kawo mani." Tana murmushi ta ce, "Nima mun haɗu a waje ta bani." Kai hajiya ta ɗaga ta sake cewa, "Kuma ta yi daɗi sosai, komai ya yi daidai daidai har yajin bata cika ba, ga Deeni nan ma da bai ta6a cinta ba yana ci alamar ta yi masa daɗi." Balaraba ta ce, "Eh wllh, nima ta yi mani daɗi don kasa haƙura na yi a can bakin famfo na samu wuri na zauna ina ta ci." Duk suka ɗan yi dariya, kuɗin da ta ruƙo a hannunta ta miƙa ma Salma ta ce mata ga kuɗin farar, tana kallon Balarabar da murmushi ta ce mata ta ɗari biyar ce ta kawo mata sauran ala koro ne ta ƙara mata, Balaraba ta ce, "Ahh, ya za a yi haka kuma Salma?" Ta ce mata Allah kuwa suma su hajiya ala koron ta kawo masu." Hajiya ta ce, "To kuma in ana haka Salma ta ya za a maida kuɗi har a samu riba?" Ita dai murmushi kawai take ta ce ma hajiya ai duk da haka zata samu riba,