Sashe 147
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read
Aunty Kubra na duba abubuwan da Dr ya kawo ma Salma bayan ta shiga cikin gida, leda ta farko kayan ciye-ciye ne har da manyan chocolates masu kyau kana ganin su za su yi tsada, ɗayan ledan kuma kayan shafe shafe ne da manyan turarurruka suma dai da gani duk masu tsada ne, ita dai Salma tana zaune gefe tana bin kayan da kallo, aunty ta ɗago ta kalle ta da ɗan murmushi ta ce, "Lalle Dr da gaske yake, su baby an fara samun alkhairin saurayi." Kauda kai Salma ta yi tana ɗan murmushi tare da ɗan tura baki, aunty ta ce, "Ko a can akwai saurayin da ya taba kawo maki abu irin haka?" Salma ta juyo ta kalle ta a hankali ta ce, "Ai ban saurarar su ma, amman dai Aliyu yana aiko mani da ƴan abubuwa, da ban amsa ma innarmu ce take cewa in amsa." Aunty ta tambaye ta waye Aliyu, ta ce abokin Sageer ne, wani kallo aunty ta yi mata ta ce, "Ana maganar samarin kirki, abokin Sagir ai daga ji ba wani saurayin kirki bane tun da shima Sagir ɗin ya yake." Dariya Salma ta saka, itama aunty dariyar take ta ce da yana kusa ta faɗi hakan da sai ya masu tijara, "Ya ku ka yi da shi Dr ɗin?" Ta tambaya tana kallonta, dan shiru Salma ta yi kafin ta ce, "Kawai ya tambaye ni wai ra'ayina akan shi, to ni dai rasa yadda zan ce masa na yi, shine ya ce ko ya bani lokaci in yi shawara na ce eh." Aunty ta jinjina kai ta ce hakan ya yi sai ta natsu ta yi shawara da zuciyarta ko mi ta yanke ta sanar mata Allah Ya za6a abun da ya fi zama alkhairi. Bayan Salma ta gama yin shirin kwanciya tana sanye da rigan bacci daidai gwiwa ta hau gado, ɗan lallatsa wayarta ta yi kafin ta ajiye ta gefe, bayan ta yi addu'a daga haka ta rufe ido, ringing ɗin da wayarta ta fara alamar shigowar kira ya sa ta buɗe ido da sauri ta fara tunanin waye ya kira a lokacin, bin baƙuwar lambar da ake kiran da ita ta yi da kallo, kamar bazata ɗaga ba can dai ta kai hannu ta yi picking tare da kara ta a kunne, daga ɗayan 6angaren ta ji an yi mata sallama nan take kuma ta gane muryar Dr Hisham ce, "Salmah..." Bayan ta amsa sallaman a hankali ta ji ya kira sunanta, "Hope kin gane mai magana." Ta amsa masa da eh, ya ce, "Dama tun da ba a kira ni aka ji ya na koma ba shine na ce ni bari na kira in ji ya kika shiga gida." Ɗan buɗa ido Salma ta yi sai kuma ta ɗan yi murmushi ta ce, "Ai bani da number ɗin ka ne." Ya ce, "Ai in an damu da aji ya na koma zaki amsa a wurin aunty kamar yadda nima na yi." Shiru ta ɗan yi sai kuma a hankali ta ce, "Ka yi haƙuri to" Da sauri ya ce, "No ai ba laifi kika yi ba, duk yadda kike so haka za a bi." Shiru ta yi kawai, can ta ji ya ce, "Ɗazun na tambaye ki kin bani labarin ƴan'uwanki har da business da kike yi, amman ni you didn't ask anything about me, ko baki son sanin komai akai na ne?" Salma ta ɗan yi shiru can ta ce, "Ai na san aunty Kubra ta san komai akan ka." Ya ce amman ai waƙa a bakin mai ita ya fi daɗi ko, ta dai yi shiru bata ce komai ba, sigh ya yi ya ce mi take yi ne yanzu, ta bashi da amsa da ta kwanta, ya ce ko har ta fara yin bacci ya tashe ta, ta ce, "Zan dai fara yin baccin ne ka kira." Ya ce, "Ok afuwan, bari in barki to ki yi baccin. Gud nyt, I love u" Ba shiri Salma ta runtse ido, jin bata ce komai ba ya kira sunanta, ta gane dalilin bata amsa masa abun da ya ce bane ya sa shi kiran nata, da ƙyar ta ce, "Na gode...." Tana jin sautin ɗan murmushin da ya yi daga haka ya kashe wayan, bin screen ɗin wayan ta yi da kallo bayan ta gama na ɗan lokaci, ajiye wayan ta yi tana niyyar rufe idonta ta ji ƙarar shigowar saƙo a wayar, airtime na dubu biyar ta ga ya turo mata, Salma ta yi shiru gaba ɗaya ta rasa ma tunanin da zata yi, wata zuciyar ta bata ta kira sa ta yi masa godiya, a sanyaye ta kira layinsa sai dai har kiran ya katse bai ɗaga ba, ƙyale sa ta yi bata sake kira ba, tunanin mi zata yi da kati har haka ta shiga yi, a haka tana ta tunane-tunane har bacci ya yi awon gaba da ita. Washe gari suna zaune suna yin breakfast da aunty, tunanin ta sanar da ita game da katin da Dr ya turo mata ya zo ranta, bayan sun gama kamar ko yaushe ta kwashe kayan ta kai kitchen, sai da ta wanke komai sannan ta dawo cikin falon ta zauna a kujerar kusa da wadda aunty ke zaune, "Baby ya aka yi ne?" Aunty ta tambaya tana ɗan murmushi ganin kamar Salman na son yin magana, "Dama zan faɗa maki Dr ɗin nan jiya bayan na kwanta ya kira shine har ya tura mani airtime na 5k." Aunty ta ɗan yi murmushi ta ce, "Dr ke nan kin gode, dama shi haka yake da son yin alkhairi, ko nan asibiti yana taimakon patients sosai, wani lokacin har kuɗin aiki yana biya ma wasu wanda suka kasa biya, haka idan azumi ya zo ma kullum ne sai ya saka an yi ma patients da masu jinyar su sadakar abun buɗe baki, hatta mu abokan aikinsa duk yana mana alkhairi lokaci lokaci, da yake dai bayan aikinsa suna da arzaƙi gaskiya, kuma babansa senator ne nan Kaduna." Ita dai Salma ta yi shiru tana saurarar ta, "Kin yi masa godiya ko?" Salma ta ce lokacin da ya turo ta kira ta yi godiyar amman bai ɗaga ba, Aunty ta ɗaga kai ta ce, " Shike nan daga baya kya masa godiyan." Salma ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "To ni aunty ya zan yi da kati har na dubu biyar." aunty na dariya ta ce ta yi amfani da shi mana, ta ce, "To ai ni idan zan yi amfani da kati ina sakawa." Aunty ta ɗan ɗage gira ta ce, "Na fa manta ɗiyar tawa babbar yarinya ce mai kwasar salary, to yanzu da baki nan ma ya ake ciki da aikin?" Salma ta ce mata Sageer ne ya ci gaba da kula da komai, aunty ta ɗaga kai ta ce "To shi ɗan ball ɗin kuna magana da shi?" Salma ta ce mata ba sosai ba kawai sai idan da wani abu kan aikin da ya saka ta shine take masa magana, kuma shima yawanci saƙo ne take tura masa kuma wani saƙon sai a daɗe ma kafin ya duba, sai kuma wani lokacin tana tura masa saƙon gaisuwa, aunty ta yi shiru tana kallon Salma bayan ta gama maganar, haka nan daga yanayin da fuskar Salma ta nuna bayan ta kawo maganar Deen sai take ganin kamar da wani abu a ranta game da shi, aunty ta ji tana son ta san ko akwai wani abu a ranta game da Deen, cikin kwantar da murya ta ce, "Baby ko dai kin fara son shi?" Salma ta yi saurin kallon aunty, ɗan murmushi ta yi tana kikkafta idanu ta ce, "Aunty saboda mi zaki ce haka." ta ce mata haka nan ta tambaya, shiru Salma ta yi ita kanta ta kasa gane yanayin da take ji a zuciyarta game da shi, ganin yadda aunty ta kafe ta da ido ya sa ta ɗan yi murmushi wanda ya fi kama da na yaƙe ta ce, "A'a aunty...kuma wannan ma ai ya fi ƙarfi na da zan ce ina son shi." Aunty ta yi wani murmushi ta ce, "Ba wani fin ƙarfin ki da ya yi, yadda kike tubarkalla baby ba wani namiji da ba zaki iya siye zuciyarsa ba, ga dai misali nan kan Dr, ba ƙaramin son sa ƴan matan nurses da doctors ke yi ba, amman ke daga ganin ki ya kamu da son ki kuma son ma da aure." Ita dai Salma ɗan murmushi kawai take, "Allah Ya tabbatar mana da abun da ya fi zama alkhairi, rabon bawa baya ta6a wuce sa, idan shi ɗin rabon ki ne kina zaune zai furta maki so har ya aure ki idan shi ne mijin ki." Da sauri Salma ta ce, "Ni fa aunty ban ce son shi nike ba." Aunty na murmushi ta ce ai itama bata ce hakan ba, Salma ta sauke idonta ganin aunty nata murmushi, wayarta da ke gefe ta fara yin ringing ta kai hannu ta ɗauka, ganin yadda ta yi ɗan jimm aunty ta tambayi waye ke kiran ta, a hankali ta ce mata shine, aunty ta yi saurin cewa, "Ɗan ƙwallon?" har saida ta sa Salma yin ƴar dariya ta ce mata a'a Dr, aunty da itama murmushi ne akan fuskarta ta ce to ta ɗauka mana idan kuma kunya take ji ta tafi ɗaki, miƙewa ta yi jiki a sanyaye ta nufi hanyar ɗaki, aunty ta bi ta da kallo har ta shige. Tun Salma bata sakar ma Dr jiki a hankali har ta fara saki, akai akai yake kiran ta su yi waya, ko bai zo ba wasu lokuttan zai ba aunty idan ta je aiki saƙo ta kawo mata, katin waya da data kuwa har yawa suke mata a waya, haka idan aunty tana aikin kwana suka je tare asibiti indai shima lokacin yana duty to da ita yake ward rounds ko kuma su zauna office ɗin sa yana aikace aikacen sa sun yin hira, duk da ba sosai take sakin jiki ba, da ya gane tana son karatu sosai yawanci ya fi yi mata hira kan abun da ya shafi karatun nursing da take son yi ta hakan ne take sakar masa jiki sosai, amman har lokacin bata faɗa masa ra'ayinta game da shi ba, daga baya da ya matsa kan son jin ra'ayinta kan aurenta da yake son yi, sai ta samu aunty Kubra ta sanar da ita cewa ita gaskiya ba yanzu take son yin aure ba sai ta fara karatu koma ta gama, to itama aunty da yake ta 6angare guda tana jin zullumin auren nasu ba kamar da take ganin Salman ta yi ƙarama da kishiya, da kanta ta yi ma Dr magana kan ra'ayin Salma game da aure, ya nuna mata ba komai zai jira, tare da roƙon alfarmar ba sai ta gama karatun ba tana cikin yi sai ya aure ta ta kammala a gidansa, a haka aka bar maganar. Bayan Leemarh ta yi wata guda a Funtua mom Jameela ta takura mata kan ta dawo gida haka nan, ita kuma ta ce bazata koma ba har sai hutun su ya ƙare nan da sati biyu, har dad ɗinsu ta yi ma magana kan ya sa a je a ɗauko ta, shima koda ya yi mata magana kan dawowa ta nuna masa sai hutun ya ƙare zata dawo, da ya yi ma mom magana kan ta ƙyale ta ai sati biyun kaman gobe ne, haka ta ƙaraci fushinta akansa. A kwana a tashi har Salma ta yi sati shidda a Kaduna lokacin kuma hutun su ya ƙare har ta fara shirin komawa gida, ana saura kwanaki ta tafi Dr Hisham ya ɗauke ta ya kaita wani babban mall, ganin ta ƙi sakin jiki ta ɗauki kaya ya sa da kansa ya shiga ɗaukar mata, kaya masu yawa ya siya mata, duk da Salma ta marairaice masa kan sun yi yawa ya ce ai ba roƙon sa ta yi ba, ita kanta aunty Kubra sai da ta masa maganar yawan kayan bayan ya maida ta gida, ya ce mata ba komai ko ba wani abu tsakanin su ita tamkar ƙanwarsa ce, ƙarshe saidai suka yi masa godiya, a yadda ya so ma shi zai maida Salma Funtua, ya ce ma aunty yana son ya je ya gaishe da iyayenta ya gabatar masu da kansa, duk da dama sun riga sun san da maganarsa don aunty ta sanar masu, aunty Kubra ta ce masa tare take son su tafi ta maida ta sannan ta ɗan kwana biyu don ta jima bata je ba, ta ce ko ya bari daga baya sai ya je ya amince da hakan, ita kanta aunty sosai ta siya ma Salma kaya har da sababbin ɗinkuna ta yi mata kamar dai yadda dama ta saba yi mata idan ta je hutu.