Sashe 163
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Salma na kwance a saman gadonta jikinta sanye da doguwar rigar bacci, wani irin farin ciki take ji yana ratsa zuciyarta sakamakon nasarar da su Deen suka yi, sai dai kuma a wani 6angare na zuciyarta tana jin tsananin son yin magana da shi, ta damu sosai da abun da ya same shi ɗazun, shiyasa take jin ina ma zata samu yin magana da shi don ta yi masa ya jiki, duk da tun bayan kammala gasar ta tura masa saƙon taya murna...sam ta kasa yin bacci sai faman juyi take, akai akai take ɗaukar wayarta ta duba saƙon da ta tura masa ko ya shiga, wani lokacin kuma ta shiga social media da gasar tasu ta karaɗe ko ina, mutane nata murnar nasarar da suka yi, ko ina hotuna da videos ɗin Deen na gasar ne ke ta trending ana ta yabon ƙwazon da ya nuna, hakan kuma ke ƙara ma Salma jin son yin magana da shi...a haka har dare ya raba Salma na abu ɗaya, bacci ba mai nauyi ba ke ɗan ɗaukar ta, kuma da ta fara sai ta farka ta jawo waya ta duba wai ko zata ga ya hau online, ƙarshe dai ta fidda rai dama ita kanta ta san ba lalle ta samu yin magana da shi ba a wannan lokacin, haka nan ma da ba lokacin gasa irin haka ba idan ta tura masa saƙo sai a daɗe bai duba ba, balle kuma yau da ta san dole bai da lokacin kan sa, tuna hakan ya sa ta haƙura, dama kawai zuciyarta ce ta ƙwallafa mata son yin magana da shi, ajiye wayar ta yi ta rufe ido, after some minutes ta sake buɗe idanun, sam bacci mai nauyi ya ƙi ya ɗauke ta, duk ta rasa mike mata daɗi, kallon wayarta ta yi kamar kar ta ɗauka sai kuma ta kai hannu ta ɗauko ta, power ta latsa haske ya bayyana, a sanyaye ta kai hannu ta buɗe whatsApp, bayan ta shiga bin contact ɗin Deen da ke a sama ta yi da kallo saboda shine mutum na ƙarshe da ta tura ma saƙo yau, ta yi shiru tana ta kallon saƙon da har lokacin tick ɗaya ya nuna alamar bai shiga ba, har zata fita daga whatsApp din kawai sai gani ta yi tick ɗin saƙon nata ya koma biyu alamar ya shiga amman bata san lalle idan an buɗe ba, wani daɗi Salma ta ji ya ziyarce ta, hannunta har ɗan rawa yake ta buɗe chat ɗin, shiru ta yi tana dakon wai ko zata ga ya yi alamar ya karanta, har bayan wani ɗan lokaci tana a haka, ranta ne ya bata ta san dole yau yana da tarin saƙonni ƙilan nata ma yana a can ƙasa ba lalle ya duba ba, tunanin ko ta sake tura masa wani saƙo yadda idan ma nata yana ƙasan zai dawo sama ya gani, cike da shakkun ko ta yi hakan ta kai hannu a ɗarare ta yi typing, "Ya Deen." iya abun da ta rubuta ke nan ta tura masa, fita ta yi daga chat ɗin ta bi contact ɗin nasa da kallo gabanta har ɗan faɗuwa yake, after few minutes sai gani ta yi ya turo mata sako...da sauri ta buɗe, "Salmerh." Shima abun da ya turo mata ke nan, wani kalan murmushi ne ya su6uce mata, ta sake tura masa, "Na'am, ya Deen ina yini." Sai da aka ɗan ɗauki lokaci ya maido mata, "Baki yi bacci ba?" Ta tura masa, "Eh.." Ba a ɗau lokaci ba ya maido mata, "Why?" Ɗan jim ta yi kafin ta maida mashi amsa, "Saboda kai, ina son in taya ka murna." Ya ce, "Ai na ga kin tura mani message, zan gani, da kin baccin ki." Ɗan jim Salma ta yi sai kuma ta sake tura masa, "Dama kawai na damu ne da abun da ya same ka da kuna yin ƙwallo, shi ne nike son in maka ya jiki idan ka hau online." Shiru bata ga ya maido mata reply ba kuma ta ga ya karanta....lokaci ɗaya Salma ta ɗan zaro ido ganin ya kira ta video call, mamakin da gaske shi ke kiranta video call ɗin ya cika ta, da sauri ta tashi daga kwancen da take, tunani ta yi ai ba zai ganta ba idan ta ɗauka saboda duhu, ɗan miƙewa ta yi ta kai hannu ta kunna fitilun ɗakin haske sosai ya gauraye ko ina, ɗaukar kiran ta yi gabanta nata ɗan faɗuwa, shiru ta yi tana kallon Deen da ɗan murmushi akan fuskarta, yana kwance a saman wani lafiyayyen gado, jikinsa yana sanye da farar riga yayin da rabin jikinsa ke lullu6e da farin lallausan bargo, shima bedsheet da pillow case din gadon da yake kwance duk farare ne tas, sumarsa na a sake ta tarwatse a saman pillow da alama ya kwance kitson kansa, kana ganin shi ka san har lokacin akwai alamun gajiya a tattare da shi, sai ɗan lumshe ido yake, a hankali Salma ta ce, "Ya Deen sannu..." Kai ya ɗan jinjina mata, kamar ba zai yi magana ba, a hankali ya buɗe ido ya kalle ta ya ce, "Miyasa zaki hana kan ki yin bacci har wannan lokacin, yanzu nan ba 3am ya yi ba?" Ta ɗaga mashi kai tare da fadi mashi karfe ukku da rabi a nan, shiru bai ce komai ba ita kuma tana ta ɗan murmushi, gani take abun kamar ba gaske ba, mutumin da yau duk duniya ake magana akan shi shine take magana da shi haka, "Ya Deen na taya ka murna sosai." Yana kallonta da ɗan murmushi ya ce mata ya gode, sai kuma ta ji ya ce amman basu suka yi nasaran ɗaukan cup ɗin ba, da sauri ta ce, "Ai kuma kun yi nasara yaya Deen, tun da na ji an ce Nigeria bata taba kai wa wannan matakin ba." Slowly ya furta, "Haka ne." ta ce, "Ya jiki?" Hannu ya kai ya ɗan shafi kan shi da murmushi ya ce mata ya samu sauƙi, ta ce mashi Allah Ya ƙara sauƙi ya tsare gaba ya amsa....tana ta kallon shi ganin yadda idanun shi ke ta lumshewa ta yi tunanin kada ta takura masa ko bacci yake ji, ta ce, "Yaya Deen ko bacci ka ke ji kada in takura maka." Buɗe idanun shi ya ɗan yi sosai yana kallon ta ya ce no bata takura masa ba ai shi ya kira ta, ya ce ya yi bacci sosai yanzu ma sallan asuba ya gama, kawai maganin da ya sha ne bai gama sakin shi ba, Salma ta ɗaga kai alamar fahimta, sosai take jin daɗin muryarsa tana jin kamar kar su daina yin maganan.
"Ya school?" ta ji ya tambaya,
Ta É—an buÉ—a ido tana murmushi ta ce, "Ai na gama." Ya ce, "When?"
"Kusan wata ukku ke nan." ta bashi amsa, idanun shi akanta ya ce,"Mi yasa baki sanar mani ba?"
Tana ta ɗan murmushi ta ce, "Kawai na ga lokacin ka yi busy sosai saboda shirye shiryen wannan gasan." Ya ɗaga kai, sai kuma ya ce amman ai ya bata number din da zata riƙa reaching nasa out miyasa bata amfani da shi, ta ce haka nan kawai kada ta rinƙa takura ma manager ɗin nasa, kuma ta ga ta wannan number ɗin ma idan tana son yi mashi magana tana amfani da ita lafiya lau, shiru ya ɗan yi still yana ta kallonta, da alama zumuɗin kiran ta da ya yi yasa ta manta a yadda take, kanta a buɗe don tuni da tana juye juyen dakon shi a waya hulan ta ta cire, kanta na a kwance ba kitso ta yi fakin gashin ta nade shi a wuya, daga gaban kanta sumar wurin a kwance luff luff,
"Ya school?" ta ji ya tambaya,
Ta É—an buÉ—a ido tana murmushi ta ce, "Ai na gama." Ya ce, "When?"
"Kusan wata ukku ke nan." ta bashi amsa, idanun shi akanta ya ce,"Mi yasa baki sanar mani ba?"
Tana ta ɗan murmushi ta ce, "Kawai na ga lokacin ka yi busy sosai saboda shirye shiryen wannan gasan." Ya ɗaga kai, sai kuma ya ce amman ai ya bata number din da zata riƙa reaching nasa out miyasa bata amfani da shi, ta ce haka nan kawai kada ta rinƙa takura ma manager ɗin nasa, kuma ta ga ta wannan number ɗin ma idan tana son yi mashi magana tana amfani da ita lafiya lau, shiru ya ɗan yi still yana ta kallonta, da alama zumuɗin kiran ta da ya yi yasa ta manta a yadda take, kanta a buɗe don tuni da tana juye juyen dakon shi a waya hulan ta ta cire, kanta na a kwance ba kitso ta yi fakin gashin ta nade shi a wuya, daga gaban kanta sumar wurin a kwance luff luff,