← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 197

Sashe 39

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A bakin shi Jameela ta ji zancen, aikuwa cikin rawar jiki ta kira Ammin su da maganar ta nuna ita bata san ma da Sapnah ɗin na soyayya da shi ba, cike da zumuɗi Jameela ta ce mata ta tashi tsaye duk yadda za ai kada ta bari a samu matsalar da zata sa a fasa auren nan, in ba haka ba za su yi babbar asara don iyayen Maleek sun fi na Ibrahim kuɗi kuma shi kan shi Maleek din a yanzu yana da kuɗi sosai, kuma idan aka yi auren India zai tafi da Sapna ɗin, nan fa jikin Ammin ya kama rawa har tana faɗin wllh da a ce Naila ta girma da sai ta sa an juye al'amarin ya koma kanta don bata tunanin za su rinƙa samun wani abun arziƙi idan aka yi auren da Sapna tun da ita sakarya ce bata son su da arziƙi, anan Jameela ta shiga bata shawarar ta ja Sapna ɗin a jiki ta yi ƙoƙarin canza mata hali, idan bata canza ba bayan an yi auren kawai ta saka bokanta ya yi aikin da za a canza mata ra'ayi ta rinƙa yin abun da ake so, sosai Ammi ta ji daɗin shawarar ta ce haka kuwa za a yi. Bayan sun gama yin wayar haka ta rufe Sapnah da faɗan wai don me bazata sanar masu ba a yi mata shiri sosai yadda abun zai tabbata ba tare da wata matsala ba kamar yadda aka yi na Jameela, Sapna ta san abun da take nufi da a yi mata shiri don tasan tana biye biyen bokaye kuma ta tsani hakan, nan fa Ammin tasu ta shiga rawar jiki haka ma babansu bayan ta sanar mashi, har da cin alwashin zuwa wurin bokanta washe gari tana faɗin ba abun da zai sa a fasa auren, Sapna har nuna mata ta yi ita dai bata son ta saka a yi ma Maleek wani abu idan Allah Ya ƙaddara shi ɗin mijinta ne ba abun da zai hana ta aure shi, Ammin ta hau surfa mata masifa tana faɗin bata da wayau, yanzu waya faɗi mata abu irin wannan ana tsayawa wai a zura ido kowa tashi yake tsaye ya nemi taimako da sa'a, har da bata misali da ba ga ƴan mata nan ba da iyayen su suka lanƙwashe hannu basu nema masu taimako duk sun yi kwantai ba mazajen auren ba, ita dai Sapna duk da hakan ta nuna bata son ta je wani neman taimako.

A daren ranar hajiya ta sanar ma ambasada game da bincikin da ta yi da kuma abun da ta sani na halayen Sapna, shi kuma ya kira Alhaji Usman ya shaida mashi. Cikin dare Sapnah ta tashi ta yi nafilfili ta roƙi Allah kada ya ba Amminsu sa'a a duk abun da zata sa a yi, tana ƙwalla ta roƙi Allah Ya bata Maleek a matsayin miji idan tana da rabo. Ikon Allah, washe gari Ammin ta tashi bata jin daɗi, duk yadda ta so ta fita ta kasa ba don ta so ba ta bari sai ta samu sauƙi. Bayan dad ɗin Maleek ya ƙara sakawa an yi mashi bincike anan Kanon aka tabbatar masu da cewa Sapna tana da halayen kirki ta fita daban a yaran unguwar ma baki ɗaya, mahaifiyar Maleek ce ta so ta ƙi goyon bayan abun saboda wata ɗiyar ƙawarta take son ya aura, dad ɗinshi ya ce mata tun da ya nuna Sapna yake so kuma an yi bincike bata da wani hali mara kyau kawai su ƙyale shi ya aure ta, ya ce mata ta san yaran zamani in aka ce za a hana su abun da suke so ko aka ce za ai masu dole kan abun da basu so abu mara daɗi na iya faruwa, har ya bata misali da lokacin da aka hana Ibrahim auran yayarta abun da ya biyo baya. Bayan dad ɗin ya sanar da Maleek cewa ya faɗa ma yarinyar iyayensa za su zo su gana da nata iyayen, a daren ranar ya kira Sapna waya ya sanar mata, baiwar Allah tamkar ta zuba ruwa ƙasa ta sha saboda farin ciki har sujjadar godiya ga Allah ta yi, suma iyayenta sun yi farin ciki kamar me, duk da haka Ammin tasu bata haƙura da zuwa wurin bokan da ta yi niyya ba. Ana zuwa neman aure aka saka rana gaba ɗaya wata ukku masu zuwa.

Bayan Jameela ta yi arba'in har ta je Kano ta dawo ta yi ma Ibrahim zancen komawar su ƙasar waje don ta ci gaba da karatun ta, a nan yake sanar da ita baza su koma ba gaba ɗaya anan za su ci gaba da karatun shima zai yi master's degree ɗin shi kan political science don yana son fara yin siyasa, tubure mashi ta yi kan ita bata yarda ba gaskiya a can take son yin karatunta, ta ce idan ma shi anan zai yi to sai shi ya tsaya ita ta tafi, lalla6a ta ya shiga yi yana nuna mata manufar shi na su tsaya anan din ba don komai ba sai don su saba da mutane sosai yadda ba zai samu matsala a ƙi za6ar shi saboda ba zaune yake ba anan idan ya fito takara, ya nuna kuma dole sai itama ta tallafa mashi kan hakan 6angaren da ya shafi mata, ta ɗan ji tana goyon bayan shiga siyasar da yake son yi, sai dai ta wani 6angaren tana jin kishin yayan shi Sa'ad da matarshi dake a ƙasar waje ga kuma Sapna ma da an ɗaura auren su za su bar ƙasar, kasa 6oye abun da ke ranta ta yi ta ce mashi amman ita hakan ci baya ne a wurinta ga Amina can har ta yi degree ɗinta a ƙasar waje haka ma Sapna za ta je ta ci gaba da karatunta sai ita za a dankwafe ta anan ta ci gaba da karatu, nuna mata ya yi hakan duka na ɗan lokaci ne ai da zarar ya fito takara ya ci sai ƙasar da take so zata je, har ya bata misali da ai tana ganin yadda matan ƴan siyasa masu muƙamai suke fantamawa yadda ransu ke so, tana jin hakan ta ce mashi shike nan ta amince amman ta ya zata ci gaba da karatu a wannan ƙauyen garin, ya ce mata ta kwantar da hankalinta ya tsara masu komai, dad ɗinshi na da wani babban gidan gona a Zaria kuma akwai gida mai kyau a ciki can za su koma sai su ci gaba da karatun a ABU Zaria, cike da nuna gamsuwa ta ce mashi ta amince kuma zata taimaka mashi sosai a harkar siyasar shi amman sai ya yi mata alƙawarin idan ya fito takara ya samu duk abun da take so zai yi mata, yana murmushi ya ce mata ya yi mata alƙawarin hakan.

A kwana a tashi bayan watanni ukku aka yi bikin Sapna da Maleek ana gamawa suka wuce India, kamar yadda Ibrahim ya tsara masu haka aka yi suka koma Zaria a can suka ci gaba da karatu ya yin da ya shiga shirye-shiryen fara shiga siyasa. Bangaren iyayen Fahad duk bayan lokaci suna zuwa Funtua wani lokacin ma anan yake barin su shi ya koma daga baya sai su bi shi. A kwana a tashi bayan shekaru biyu da wasu watanni dad din Deen ya kammala karatun shi ya tsunduma harkar siyasa yayin da Jameela ke cikin yin karatun degree dinta, cikin sa'a ta ubangiji a karon farko da Ibrahim ya fito takarar kujerar majalissar jaha sai gashi ya ci, don ya samu farin jini a wurin mutane duk da nasarar ta shi na da nasaba da mahaifinshi wanda yake mutum ne mai kyautata ma mutane sosai, zo ka ga murna a wurin Jameela ganin haƙarta ta fara cimma ruwa an zama matar ɗan majalisa, haka ƴan'uwa da abokan arziƙi suka yi ta zuwa taya murna, bayan rantsar da su suka kama aiki, a lokacin dole ya raba ƙafa bai a Katsina bai a Funtua haka Zaria da har lokacin Jameela ke a cikin yin karatu. Abu na farko da ta fara buƙatar ya siya mata ita ce danƙareriyar mota, ba tare da ya gardama mata ba ya siya mata saboda ya san ta taka rawa sosai wurin ganin ya ci za6en, nan fa Jameela a ka fara fankama ba kama hannun yaro, bayan wani lokaci ta buƙaci ya siya ma iyayenta gida shima bai ƙi ba ya siya masu gida mai kyau a can Kano, a hankali ta fara saka shiririta a karatun ta duk da ta yi nisa ta fara mashi ƙorafin ya za ai tana matar ɗan majalissa ana ganin tana karatu hakan ma sai ya ja mata raini, ƙiri ƙiri ta aje karatun ta matsa sai dai ta koma ƙasar waje ta yi, hakan kuma aka yi sai dai ya rinƙa zuwa ko kuma in ta samu hutu su zo.

Suna gab da kammala tenure ɗin su ta farko Jameela ta gama karatunta ta dawo Nigeria, saidai ko da ta dawo matsa mashi ta yi kan sai ya siya masu gida a Abuja duk da a yadda ya so su koma Katsina da zama amman fir ta ƙi dole sai dai Abujar ya siya masu gida suka koma, son kai irin na Jameela a gabanta in dai ta ga zai yi ma dangin shi alkhairi sai ta yi ƙoƙarin hanawa, ta rinƙa ƙorafin shike nan don ya samu muƙami kowa ya dauƙo buƙatar shi sai ya kawo mashi ai koda aka za6e shi don ya yi ma al'umma aiki ne ba wai kowa ya zo da bukatarsa ba, amman kuma ita kullum cikin kawo mashi baƙatun da suka shafi danginta take.
Chapter 39 · 0% Book details