Sashe 44
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ba ki ji ina kiran ki! ga Aliyu nan shine ke son magana da ke." Wani irin 6acin rai ta ƙara ji ya kama ta, Aliyun abokin shi ne yake haɗa ta da shi wai son ta yake, ita kuma ta ƙi kula shi don harkar samari bata a gabanta karatunta ta saka a gaba, bama Aliyun kaɗai ba ana yawan cewa ana son ta amman bata sauraran wani saurayi, burinta ta gama makaranta ta wuce ta yi karatun nursing ta zama kamar auntynta Kubra, kuma har da ita Kubran ta yi mata huɗubar kar ta biye ma samari ta maida hankali kan karatun ta don in dai tana son zama nurse sai ta yi karatu sosai. Bata iske kowa ba a tsakar gidan bayan ta shiga, kai tsaye hanyar banɗaki ta nufa, a bakin rijiya ta ɗauki buta wadda ke da ruwa a cikinta, ƙarar motsin da innarsu ta jiyo ya sa ta ɗaga murya daga cikin ɗaki tana tambayar waye anan ta bata amsa da ita ce,
"Salma kin dawo?" Ta ce mata eh, tana ƙoƙarin shigewa cikin banɗakin daidai innar ta fito sai dai ta ga shigewar ta, tana shiga ciki ta yi tsaye tare da jingina da bango zuciyarta ta shiga dawo mata da abun da ya faru, ƙwalla ne suka shiga zubo mata ta fara yin kuka a hankali, bata ta6a dana sanin abu kamar wannan ba, maida akalar tunaninta ta yi kan Deen, yanzu ta gane shine ɗan ƙwallon da su Sagir ke maganar shi, ita sam bata san shi ba, ko Fahad bata ta6a gani ba, dama bata fi shekara biyar da ta dawo garin ba daga Kaduna, kuma basu daɗe da suka fara yin hulɗa da hajiyar ambasada ba sanadin Balaraba da ke kawo a yi masu awara, kuma ba kasafai ta cika zuwa gidan ba don wani lokacin idan aka gama Balaraba ce ke zuwa ta amsa ko kuma a aika su Imran su kai, ita zuwanta gidan ma za a iya ƙirga shi, fuskar Deen ce ta shiga dawo mata, ita kanta ta gasgata kyawunsa sosai, ga shi komai nasa mai burgewa ne, ba ƙaramin daɗi maganar shi ke yi mata ba,
_"Kina ma wa kuka? Ko wani ya sa ki ne ki yi mashi rashin kunya....."_ Maganar da ya yi mata ta tuno, a ranta ta ayyana yanzu shike nan kallon mara kunya suke mata, idanuwanta ne suka cicciko da ƙwalla ta ƙura ma wuri ɗaya ido, ta ɗauki mintuna a haka kafin ta duƙa ta wanke fuskanta da ruwan cikin butar da ta shigo da ita, dama ba wani abu za ta yi a banɗakin ba kawai bata so innar su ta fahimci wani abu ne. Lokacin da ta fito daidai innar su itama ta fito daga cikin kicin, tsayawa ta yi da murmushi tana jiran ƙarasowar ta, daga gefe Salma ta tsaya ta ce mata hajiyar ta ce zata aiko da robar da kuma saƙo innarsu ta ce to, shiru suka ɗan yi Salmar tana kallon gefe,
"Salma..." Har saida gabanta ya bada rass jin yadda ta kira sunan ta, juyowa ta yi suka haɗa ido, "Ya aka yi ne?" Ƙaƙalo murmushi ta yi ta ce mata ba komai,
"Ah saidai idan abun da baki yi mani zaki fara, amman daga ganin fuskar ki akwai abun da ke damun ki, kamar ma har kuka kika yi ko?" Shiru ta yi tana kikkafta ido, tunowa ta yi da gargadin da hajiya ta yi mata kuma ko ba haka bama bata jin zata sanar da ita abun da ya faru don ta san itama ta yi ba daidai ba abun da ta yin, dabara ce ta faÉ—o mata cikin É—an yamutsa fuska ta ce, "Ba wanccan Sagir É—in bane." Tana jin Æ´ar ajiyar zuciyar da innar tasu ta sauke alamar hankalinta ya kwanta, "To mi kuma ya haÉ—a ki da shi ku da baku gajiya?"
"Wai yanzu na taho zan shigo shine ya kama yi mani maganar wannan Aliyu, kuma ya san na ce mashi ya daina haɗa ni da shi ban so amman ya ƙi dainawa." Yar dariya innar tasu ta yi ta ce to in banda abun ta miye laifin wanda ya nuna yana son ka, cikin tura baki ta ce ita dai bata so kuma ma ba aunty Kubra ta hana ta yin wata soyayya ba ta ce ta maida hankali akan karatu,
"Haka ne, shike nan ki bari zan gargaɗi Sagir ɗin kan hakan. Kin ma tuna mani da baki nan mamar taki Kubra ta kira waya tana tambayar ki na ce mata kin fita idan kin dawo kya kira ta." Lokaci guda ta washe baki jin maganar, Allah Ya sani tana son Aunty Kubra sosai saboda itama tana nuna mata ƙauna, wani lokacin har mamaki Salma ke yi yadda take tsananin ƙaunarta, duk da dalilin hakan kusan a bayyane yake bai rasa nasaba da rashin haihuwar da Allah bai bata ba, tambayar innar tasu ta yi ina wayar ta kira ta ta ce mata tana cikin ɗaki, ta wuce da sauri don ta je ta kira ta.
Bayan sallar magrib su Deen suka fito cikin falo don tafiya gidan su Fahad, yana sanye cikin ƙananun kaya farar t-shirt sai overshirt ja irin riga da ake ɗaurawa a saman wata mai budaddan gaba da ana ganin ta ciki, wandon jikinsa dark-washed jeans ne sai ƙafafunshi ya sanya takalma fararen gucci ace, hannun shi haɗaɗɗan agogo ce mai duhu da ta hau da kalan wandon jikinshi, ya yi kyau har ya gaji sai faman baza ƙamshi yake, shi kuma Fahad ƙananun kayan da ya canza ɗazun ne a jikin shi, gaba ɗaya falon ya karaɗe da kamshin jikinsu, hajiya dake zaune ta kalle su da murmushi ta ce sun fito Fahad ya amsa mata, Balaraba ta ƙwala ma kira ta fito, umarnin ta ɗauko saƙon ta bata ta amsa da to kafin ta juya ta koma cikin kicin, fitowa ta sake yi hannunta riƙe da wani ɗan madaidaicin kwando kalan na ƴan gayu a cikin shi warmer ne guda biyu yar madaidaiciya sai mai bi mata,
"An ce so so ne, amman dai son kai ya fi, gashi nan ku kai ma baban naku." Murmushi suka yi gaba É—aya, Fahad ya ce amman dai ta san zata haÉ—a rigima ne, tana dariya ta ce ai ta san zai samma su, Fahad ya ce ma Balaraba ta je ta kai basket É—in wurin motar shi ta amsa mashi da to cikin ladabi duk da da gani ta girme mashi, sallama suka yi ma hajiya ta ce su gaishe mata da kowa. A motar Fahad da suka zo da ita suka fita, lokacin da suka fito wajen gate É—in akwai wasu mutane a tsaye da alama Deen suke son gani ba a basu dama ba,
"Mutanen nan fa baza su ƙyale ka ba, duk da ka faɗa masu baza ka samu ganin su ba ka ga still suna nan." Deen ya ce Allah ma ya sa basu san yana a motan ba ya san har biyo su suna iya yi, ya ce zai yi ƙoƙari ya samu isasshen time ya gan su. Bayan wasu mintuna suka ƙaraso gidan su Fahad dake a bakin babban titi wanda babban gida ne na gaske, karya kan motar Fahad ya yi ya tunkari tangamemen gate ɗin gidan, yana yin horn maigadi ya leƙo ta ƙaramar ƙofa, yana ganin motar da sauri ya koma ciki ya fara buɗe masu, ciki suka shige mai gadin na ɗaga ma motar hannu duk a tunanin shi Fahad ne kawai, bayan sun shiga cikin harabar gidan mai girman gaske kai tsaye katafaren ginin gidan motar ta tunkara basu nufi inda parking space yake ba, a bakin entryhall motan ta tsaya a tare suka fito, maigadi dake can bakin gate yana ganin sun fito su biyu ya ƙara ware ido a ranshi ya shiga ayyana ko dai tare suke da Deen, nufo su ya yi da ɗan sauri yana ƙara wara ido don ya tabbatar ma kan shi ko Deen ne, tun kafin ya ƙaraso ya gane shi ɗin ne saboda hasken dake akwai a wurin, washe baki ya shiga yi bayan ya iso ya shiga faɗin, "Barka da zuwa yalla6ai...barka da zuwa, dama sai da na yi tunanin ko kai ne wllh." Sam ya kasa rufe baki sai kace yaro ya tsinci haƙori, amsa mashi Deen ya yi ya ce mashi ya aiki, da sauri maigadin ya ce, "Aiki Alhamdulillahi gashi muna akan shi muna ta ƙoƙari. Yallabai ya naku aikin ai kaima gaskiya ba ƙaramin ƙoƙari kake ba wllh muna matuƙar yaba maka, da yake nima ɗan club ɗin ku ne duk wani wasa da zaku yi sai na kalla, da a wayata nake kallo lokacin ina da andiroyin kafin ta lalace in koma mai madannai, amman duk da haka duk idan za a yi ƙwallon ku akwai wani ɗan ƙauyen mu da ke anan shi nake sawa ya zo ya tsare gate ɗin in je gidan kallo in kalla. Wllh ai duk muna yin ka yalla6ai..." Sai faman washe baki yake kai ka ce wanda aka ma albishir da gidan aljanna, murmushi ne akan fuskan Deen ya yi mashi godiya, Fahad da ya fara gajiya da tsayuwa ya ce mashi an gode daga haka ya kama hannun Deen suka wuce, maigadin nata hargowa yana faɗin a fito lafiya yallabai, ɗan ɗaga mashi hannu Deen ya yi ya ce zai ganshi da sauri ya amsa mashi da to, nufar komawa bakin gate ya yi a ranshi yake ayyana ina ma wayan shi andiroyin bata lalace ba da sai ya roƙe shi sun yi hoto ya watsa a fesbuk, a yanzu ma ɗin ma alla alla yake ya je ya fara kiran abokansa da suke kallon ƙwallo tare ya yaɗa masu labarin zuwan shi,