← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 197

Sashe 131

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sun fito daga gida sun hau hanya, Basma na ganin hanyar da suka bi ƙirjinta ya shiga bugawa don ta fahimci gidan su Huda suka nufa, bayan tafiyar mintoci suka ƙaraso unguwar su Huda, cikin harabar katafaren ginin suka shiga, babban ginin bene ne mai hawa da yawa, wurin da aka tanada don ajiye motoci ya nufa ya parker motar, babban ginin na ɗauke da apartment da dama na mutane masu matsakaicin ƙarfi, kasantuwar ranar hutun ƙarshen mako ce, a kowane wurin da aka tanada don ajiye motoci na ɗauke da motoci, bayan ya kashe motar fiddo wayansa dake a cikin aljihun jallabiyarsa ya yi ya fara latsa ta, kai wayar ya yi kunne sai da ya yi ƙoƙarin daidaita natsuwarsa kafin ya fara magana, gaisawa suka yi da wadda ya kira wato mahaifiyar Huda ya tambaye ta ko Hudan na nan, bayan ta bashi amsa ya ce mata ta turo ta suna nan a waje shi da Basma, tambayar mi ya sa ba za su shigo ciki ta yi ba, yana ɗan murmushi ya bata amsa da yana sauri ne dama hanya ce ta biyo da su shine Basma tasa su tsaya ta gaisa da Huda, bayan sun gama yin wayar ya ajiye ta gefe tare da jingina kansa jikin seat ya ɗan lumshe ido, Basma dai na zaune a baya gabanta na ci gaba da bugawa tamkar ana mata luguden ta6are, after some few minutes Huda ɗin ta fito daga cikin ginin tana sanye da doguwar riga ta ɗaura ɗan mayafi a saman kai, kana ganin yanayin fuskarta kasan ba a nutse take ba, don tun da mummynta ta sanar da ita game da zuwan su kuma ba za su shigo ba ta san zuwan na da nasaba da abun da ya faru jiya, Maleek da idonsa na akan ginin ya ga lokacin da ta fito, ya kai hannu ya buɗe ƙofar motar ya fita yadda zata gan su, tana hango shi gabanta ya tsananta bugu, tamkar wadda aka zare ma laka ta nufo su, tana kusa ƙarasowa wurin motar Maleek ya yi mata alamar ta shiga baya ba tare da ya kalle ta ba ya koma cikin motan, hannunta har ɗan rawa yake ta kama handle ɗin kofan baya, tana buɗe ƙofar zata shiga suka haɗa ido da Basma, tana ganin yanayin Basman ta sha jinin jikinta tare da sauke idanunta ƙasa, jiki a sanyaye ta zauna saman seat ba tare da Maleek ya kalle ta ba ya ce ta rufo ƙofar, shiru suka ɗan yi cike da ƙarfin hali murya na ɗan rawa Huda ta ce, "Goo..d...after..noon daddy.." Shiru bai amsa ba idanunsa na kallon waje ta glass ɗin motan, ɗan jim ta yi da tunanin ko bai ji ta ba, ƙara gaishe sa ta yi still bata ji ya amsa ba, a hankali ta ɗago ido da niyyar ta saci kallonsa suka haɗa ido ta madubin motan, da sauri ta sauke idanunta ƙasa gabanta na ci gaba da faɗuwa don ta gane yana jinta ya yi mata shiru, a kausashe ta ji ya ce, "I'm very disappointed in you Hudah!" Gabanta ne ya buga da ƙarfi ta ƙara sunne kanta ƙasa, "Dama abun da kuke aikatawa ke nan ke da Basma?" Ta ji ya jefo mata tambayar, kasa ce masa komai ta yi kuma bata ɗago ta kalle sa ba, "Mun yi tunanin kuna tarayya da juna da gaskiya, kuna ƙaunar juna tsakani da Allah ashe ba haka bane mummunan abun da kuke aikatawa ke nan?" Dukkan su idanunsu na a ƙasa suna ƴar shesshekar kuka, tambayar Huda ya yi tun yaushe suke aikata hakan kuma waye ya koya masu, kamar yadda Basma ta faɗa mashi itama irin amsar ta bashi, ya sake tambayarta su nawa suke yi ta ce masa su biyun ne kawai, "Do your parents know about this?" Kanta a ƙasa ta girgiza masa kai alamar a'a, ɗan shiru ya yi idanunsa na kallon gaba, sigh ya yi ya ce, "Then I have no choice but to inform them..." Tun kafin ya ƙarasa rufe baki a kiɗime Huda ta ɗago ta zaro idanunta da suka jiƙe da ƙwalla, ta shiga girgiza mashi kai cikin rawar murya ta ce, "No dad.. Pls don't tell them, idan suka ji za su shiga damuwa, mummy zata kashe ni..." Gaba ɗaya ta gigice don ta san mummy ɗinta tsaye take a kanta, duk da ƙaunar ta da take sosai bata wasa kan abun da ya shafi tarbiyyarta, Maleek ya ɗan jinjina kai tare da juyowa ya kalle ta ba alamun sassauci akan fuskar sa ya ce sun san suna tsoron a sani amman suke aikatawa, a tare suka haɗa baki suna roƙon shi kan ya yi haƙuri sun yi alƙawarin ba za su sake ba, Maleek ya ɗan lumshe idonsa, gaba ɗaya kan sa ya ɗaure ya rasa ta inama zai 6ullo ma al'amarin, ya san tabbas iyayen Huda suka ji dole su shiga tsananin tashin hankali, sai dai kuma ba daidai bane idan ya 6oye masu ko don su ɗauki matakin da ya dace don magance matsalan, tunanin mafita ya shiga yi a cikin ransa, after a while ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, a nutse ya shiga yi masu nasiha tare da nuna masu illar abun da suke aikatawa, ya ce wannan ba ɗabi'ar mutanen kirki ba ce kuma idan suka ci gaba da aikatawa sun ɗauki hanyar lalata rayuwar su ne, kuma matuƙar suka mutu suna aikata hakan tabbas za su haɗu da azabar Allah, daga baya ya yi masu faɗa sosai tare da saka su su yi masa alƙawarin ba za su sake aikata hakan ba, ya ɗaukar masu alwashin matuƙar ya gano ba su bari ba zai ɗauki mummunan matakin da ba su ta6a zato ba akan su, kuma zai sanar da iyayen Huda da mom ɗin Basma duk su sani, Huda kuka sosai take yi don nasihar da ya yi mata ta shige ta sosai, cikin kuka ta yi masa godiya tare da yi masa alƙawarin ta daina, ya jinjina kai tare da cewa, "May Allah guide you all." Duk suka amsa da amin, ya sake ce masu kowannen su idan ya yi salla ya riƙa yi ma kansa addu'ar neman shiriya kan hakan dama duk wani sa6on Allah suka amsa mashi, tissue ya ciro ya miƙa ma Huda ya ce ta goge fuskarta don kada idan ta koma gida a gane ta yi kuka, hannunta na rawa ta amsa tana gogewa, gaba ɗaya tausayin yaran da su kansu iyayensu ya kama shi don wannan musiba ce ta same su, bayan ta gama ya ce ta koma gida, bayan ta fito a parking space ɗin Huda ta saƙe jikin motan mummynta ta shiga yin wani sabon kuka, duk sai ta ji ta tsani kanta da ya kama su suna aikata hakan, dama ita tun farko ranta baya so Basma ce ta koya mata, lokacin da ta fara ƙoƙarin saka ta a hanyar sai da ta nuna mata abu ne mara kyau baza ta yi ba, amman haka tai ta faman ƙoƙarin jan ra'ayinta tana kashe mata kuɗaɗe a haka har saida ta yi nasara a kanta, maganar da suka faɗa ma Maleek cewa cousin ɗinta ce ta koya masu ba gaskiya ba ce, tun jiya Basma ta kira ta ta tsara mata hakan. Akan hanyar komawar su gida sai da Maleek ya ƙara yi ma Basma nasiha sosai, ta nuna masa ta yi masa alƙawari ba zata sake aikata hakan ba, bayan sun iso gida cikin sa'a har lokacin Sapna tana bacci don jiya bata samu ta yi isasshen bacci ba saboda halin ciwon da su biyun suke ciki. Sosai Maleek ya yi ƙarfin hali wurin ci gaba da yin harkokinsa kamar ba wani abu, sai dai a can ƙasan ransa abun na damunsa sosai duk da ya ɗauki hakan a matsayin ƙaddara, sannan ya saka ma Basma ido sosai tare da yi masu addu'oin neman shiriya, duk da suna pretending kamar ba abun da ya faru sam su biyun sun kasa sakar ma juna jiki kamar yadda suke a da, amman ba su bari Sapna ta fahimci wani canji a tsakanin su ba, Basma ce ma ke ɗan shan jinin jikinta idan suna tare gaba ɗayansu amman shi Maleek yana ƙoƙarin sake ma Basma ɗin kamar yadda ya saba, wani lokacin har ta yi ta masa kallon mamaki. Bayan kwanaki da faruwan hakan, da daddare Sapna na kwance saman gadon Maleek ta tada kanta da ƙafafunsa, yayin da shima yake a kishingiɗe hannunsa guda a cikin sumarta, magana yake son yi mata da ta shafi Basma amman yana zullumin kada ta yi tunanin wani abu, sai dai ganin maganar na da muhimmanci kuma zata taimaka wurin ƙara saka mata ido ya sa shi tattaro ƙwarin gwiwa a nutse ya ce, "My love...ina son zamu yi magana da ke ne da ta shafi Basma." Ɗago fararen idanunta ta yi ta kalle shi tare da furta ok, dan jimm ya yi kafin ya ci gaba, "I think...kaman kuɗi da muke bata suna yawa, so yakamata mu rage idan so samu ne ma gaba ɗaya a daina bata kuɗi in dai ba da wani ƙwakkwaran dalili ba." Zuba masa ido Sapna ta yi da ɗan alamun mamaki akan fuskarta, "Wani abu ya faru ne?" Ta tambaya tana ta kallonsa, da sauri ya ce, "No, ba wani abun da ya faru, kawai dai na yi nazari ne duba da tana yawan kawo mana buƙatar kuɗi kuma wasu lokuttan muna bata ba tare da sanin mi take yi da su ba, kin san kuɗi suna saurin yin tasiri wurin canza mutum, wannan dalilin ne ya sa na ga ya dace mu saka kula kan hakan ba kamar yadda yanzu rayuwar ta lalace, kana ma yaron ka tarbiya wani abun sai ya zo ya 6ata hakan." Shiru ta yi tana ta kallon sa, can ta yunƙura ta miƙe zaune jikinta sanye da wata hadaddan rigar bacci iya gwiwa, zama ta yi saitin sa da yanayin shakku ta ce, "Honey ko dai akwai abun da kake 6oye mani? Basma ta aikata wani abu ne? Pls tell me.." Da sauri ya kamo hannunta cikin ƙoƙarin kwantar mata da hankali yana murmushi ya ce, "Ba wani abu kar
Chapter 131 · 0% Book details