← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 197

Sashe 135

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sageer tsaye a tsakar gida idanunsa akan wayarsa yana latsa ta ya ci gayu da shadda ruwan ƙasa, ya saka hula da takalma har da agogo ya yi tsaf da shi, bayan ɗan lokaci ya ɗago kai a ɗan harzuƙe ya ce, "Da Allah malama kina 6ata ma mutane lokaci, wllh idan baki fito ba zan yi tafiya ta in barki...." Innarsu dake tsaye a bakin baranda tana murmushi ta ce, "Aikuwa da Kubra ta maido ka tun da dai dama ita ce ƙarfin tafiyar." Ƙwafa Sageer ya yi ya ce, "Wllh ba don ina son zuwa Kadunan ba da zan ƙyale ta ne ta tafi ita kaɗai ai tana iya zuwa." Innarsu na yar dariya ta ce tun da dai shi aka ce ya kaita dole taren za su tafi, fitowa Salma ta yi daga cikin ɗakinta hannunta guda riƙe da trolley, tana sanye da riga da skirt na lace ta yafa gyale da ya hau da kayan, kafafunta ta saka takalma half cover masu ɗan tsini, ɗayan hannun ta riƙe yar madaidaiciyar jaka da ta hau da takalmanta, sosai ta ƙara kyau a cikin shigar, nufo su ta yi idanunta akan Sageer da ya tamke mata fuska dama duk tana jin abubuwan da yake faɗa, daga gefen shi ta tsaya tare da ajiye trolley ɗin tana ƴar dariya ta ce, "Man Sagir gani na fito." Ya wurga mata harara, Imrana dake tsaye sukuku da shi yana kallon ta ya ce, "Yaya Salma sai yaushe zaki dawo?" Hannu ta kai tana murmushi ta dafa shoulder ɗinsa ta ce, "Ai dai yanzu ba makaranta tun da an yi hutu balle ka damu da ba mai yi maka assignment, da hutun ya ƙare ai zan dawo." Fuska a yamutse ya ce, "Ni ai ban son ki tafi wllh, gashi innarmu ta ƙi bari a je da ni." Ya ƙarasa yana ɗan kallon innar tasu, tana ƴar dariya ta ce aikuwa ba za a je da shi ba ai a yi abu na hankali mana sai su kwasa har su ukku su tafi, "Dalla malama ki wuce mu tafi ko so kike mu yi dare a hanya, dama ga hanya ba kyau salon ki ja aje a ƙwamushe mutum." Dariya Salma ta saka ta ce, "Kada ka damu idan ma an ɗauke ka zan tara kuɗin fansar ka." Hannu ya kai zai ranƙwashe ta yana faɗin, "Shegiya dama ai na san ba ƙauna ta kike ba." Innarsu dake ta dariya ta ce, "In sha Allahu ma lafiya za ku isa." Hannu Salma ta kai ta dafa kan Hamza ta ce masa sai ta dawo shima duk ya yi sukuku ya ɗaga mata kai, kuɗi ta fiddo a cikin jakarta ta basu innarsu na ta kyale su ko jiya ba ta basu ba, tana dariya ta ce ai daga yau kuma sai ta dawo, Sageer ya kalli innarsu ya ce mata sun tafi, tana ɗan murmushi ta shiga yi masu addu'oin Allah Ya tsare ya kai su lafiya, Salma ta kalle ta tana murmushi ta ce mata sai ta dawo, "To Salmata Allah Ya kiyaye hanya." Salma ta amsa da Amin, ta kama trolley ɗin innarsu ta ɗauki wata babbar leda da ke ajiye suka nufi ƙofar fita gaba ɗayan su, bayan Sageer ya dauko jakar shi a ɗaki ya fito, suna fitowa waje wani napep ya zo wucewa Sageer ya tsayar masu, Salma nata ɗaga ma innarsu da su Imrana hannu ta shiga cikin napep ɗin, Imrana da Hamza na ganin za su tafi suka fara kuka, jikin Salma duk ya yi sanyi tana ta kallon innarsu, lokacin da mai napep ɗin zai ja ta ɗan ɗaga murya ta ce, "Innata, Imrana, Hamza, I will miss you all." innarsu ta ɗan girgiza kai kawai tana dan murmushi, a can ƙasan ranta kuwa tuni har ta fara jin kewar ɗiyar tata. Suna kan hanyan zuwa tasha Salma ta ce ma Sageer don Allah su tsaya garejin su babansu dake a kan hanya ta ƙara yin bankwana da shi da Auwalu duk da sun yi da safe, suna zuwa daidai wurin Sageer ya ce ma mai napep ɗin ya ɗan tsaya da su, fitowa Salma ta yi tana kallon baban su dake cikin yin aiki, cikin ɗan ɗaga murya ta kira shi, yana ganinta ya ajiye abun da yake yi ya yi ma Auwalu magana a tare suka nufo inda suke, Salma nata masu murmushi bayan sun ƙaraso baban su ya ce, "Mamana za a tafi?" ta ɗaga masa kai, addu'oin Allah ya kiyaye hanya ya shiga yi masu haka shima Auwalu, babansu ya kalli Sageer dake tsaye ya ce, "Don Allah Sageer ka kula da ita sosai." Yana murmushi ya ce, "To ni kuma wa zai kula da ni baba?" Duk suka ɗan yi dariya, baban ya ce ai shi kamar matsayin jagoranta ne a tafiya, sallama babansu ya yi masu ya ce su tafi kada dare ya yi masu, kuɗi ya fiddo daga cikin aljihunsa ya miƙa ma Salma ya ce su sha ruwa a hanya, tana murmushi ta ce ya bar su akwai kudi a wurinta, ya ce duk da haka dai ta amsa, bayan ta kar6a ta yi masa godiya daga haka suka koma cikin napep ɗin, suna ta ɗaga ma juna hannu har suka tafi, bayan sun iso motor park cikin sa'a suka samu motan dake lodin Kaduna kuma mutum ukku suka rage yanzu saura passenger ɗaya kawai su tafi, bayan an shiga da kayan su Salma ta shiga ta zauna, tunawa ta yi da idan ta ɗan daɗe bata yi tafiya ba wani lokacin tana yin amai, ta windown motan ta leƙa ta kira Sageer da bai shiga cikin motan ba yana tsaye yana latsa waya, waigowa ya yi kafin ya matso saitin ta ya tambayi ya aka yi, kuɗin hannunta da babansu ya bata ta miƙa masa ta ce, "Don Allah na ga mai lemu a bakin tashan ka ɗan siyo mani, ka san idan na daɗe ban yi tafiya ba wani lokacin ina yin amai." Wani kallo ya yi mata ya ɗan yamutsa fuska ya ce, "In an gan ki dai kamar wata wayayya amman ƴar ƙauye ce mai yin amai a mota." Salma ta ɗan ɗaure fuska ta ce, "To ai dai lalura ce kuma ba kaina farau ba." Ya ce to bai siyo lemun, daga haka ya bar wurin ba tare da ya amsa kuɗin ba, komawa ta yi cikin motan tana tunanin ko ta fita da kanta ta siyo duk da ba lalle ta yi aman ba amman lemun zai taimaka mata saboda tashin zuciya, muryar Sagir ta ji ya kira sunanta ta juya ta kalle shi ta windown motan, ledar lemu ya miƙo mata ta amsa tare da yin murmushi ta ce, Thank you my bro, I love u" ɗan harararta ya yi ba tare da ya ce komai ba, bada jimawa ba aka samu cikon passenger guda ba 6ata lokaci suka hau hanya sai fatan Allah Ya sauke su lafiya. Da sallama daddy Sa'ad ya shigo cikin falon, hajiya ta juya tana amsawa ganin su ta shiga yin murmushi, dad Ibrahim yana riƙe da wayar hajiya yana yin waya da ƙanwarsu hajiya Murja bayan ta kira hajiya shine aka bashi suke magana, ya ɗaga ido da murmushi yana kallon yayan nasa dake ƙarasowa ciki, daga gefen hajiya alhaji Sa'ad ya ɗan rankwafa ya gaishe da ita tare da yi mata barka da juma'a, fuskarta da murmushi ta amsa masa, kallon su Sadeeq ta yi tana amsa gaisuwar da suke yi mata ta kai hannu ta kamo Ayden zuwa jikinta tana tambayarsa ana ta shan hutu ba school ko yana murmushi ya ɗaga mata kai, daidai lokacin da daddy Sa'ad ya miƙe dad ya gama yin wayar, miƙewa ya yi da faffaɗan murmushi ya miƙa ma yayan nasa hannu yana gaishe da shi, da fara'a dad Sa'ad yake amsa masa tare da yi mashi an zo lafiya, a saman kujerar da yake ya zauna shima dad ya koma ya zauna, dad Sa'ad ya tambayi iyalinsa ya amsa masa da duk suna lafiya suna gaishe da su, Sadeeq ya matsa ya ce, "Daddyn Abuja ina wuni, an zo lafiya." Dad ya miƙa masa hannu ya ce, "Sadeeq my boy, lafiya lau, ya school koda yake an yi hutu ko?" Sadeeq ya ɗaga masa kai, kallon Ayden dad ya yi ya miƙa masa hannu yana cewa ya zo su gaisa hajiya ta ce masa ya je, shima Ayden ya gaishe shi dad ya kama hannunsa da faffadan murmushi ya ce masa ana ta hutun school ko ya ce masa eh. "Sai ku ka ga ƴar hutu." Hajiya ta faɗa idanunta akan daddy Sa'ad, da murmushi ya ce, "Haleematu, aikuwa suna can ita da ƴan'uwan suna ta farin cikin ganin juna." Hajiya ta ce, "Allah Sarki, an kwana biyu ai ba su ga juna ba." Hira daddy Sa'ad da dad suka shi ga yi, hajiya nata kallon su fuskarta cike da ƙauna, tana jin daɗin ganin yaran nata a tare, Balaraba ce ta shigo cikin falon, ta ɗan rankwafa da gaishe da daddy Sa'ad ya amsa mata cikin sakin fuska, wurin hajiya ta nufa cikin ladabi ta sanar da ita ta shirya abinci a table, hajiya ta jinjina mata kai, kallon su ta yi ta ce masu ga abinci can an shirya, ganin sun yi shiru ta ce ko sai sun dawo daga salla, daddy Sa'ad ya duba agogon wrist ɗin sa ya ce ai lokacin sallan ma ya yi, dad ya ce ko a bari sai sun dawo daga sallan hajiya ta ce to.
Chapter 135 · 0% Book details