Sashe 190
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A Cikin Rayuwa Book 2 is ₦500 for the Regular WhatsApp Group and ₦800 for the Special Telegram Group. Payment via Sterling Bank (0121797114, Zainab Bature) Send payment evidence to WhatsApp: 09013804524, 08169856268 or Telegram: 08032811442. Message only, no calls please.
✨A CIKIN RAYUWA✨
BY ZAINAB BATURE
ZEELALUH
Labarin na tafe da sabon salo mai matuƙar ban mamaki, kada ku bari a ba ku labari🔥
Page 59
Washe gari bayan sun gama yin break fast, wurin ƙarfe sha biyu saura suka shirya zuwa gidan hajiyan ambasada, aunty ta ci gayu da Abaya mai kyau, ta yi rolling veil ɗinta, fuskarta ta saka glasses da ta riga ta yi sabo da sakawa, Salma ma ta saka doguwar rigar atamfa, har da innarsu za a je itama ta saka doguwar rigar atamfa, lokacin da suka isa falon hajiya tana zaune bata daɗe da fitowa ba, bayan Balaraba ta gama gyara falon, sai ƙamshi ke tashi, hajiya ta ɗaga kai tana amsa masu sallama da ɗan murmushi, bayan sun ƙarasa ciki ta yi masu maraba tana kallon su ta nuna masu wurin zama, cikin girmamawa su aunty suka gaishe da ita ta amsa tana ta murmushi, sai da ta ɗaura idonta akan Salma da ke gaishe da ita sannan ta gane ta, ta ce "Ashe amaryarmu ce..." Ta yi maganar tare da miƙa ma Salma hannu, Salma ta taso ta iso gabanta kanta a ƙasa tana murmushi, hajiya ta zaunar da ita gefenta tana kallon ta ta yi mata an zo lafiya, Salma ta amsa da lafiya lau still kanta na a ƙasa, ɗagowa hajiya ta yi ta kalli innarsu Salma ta ce, "Ai farko ban gane ku ba sai da na ga Salma, duk ya yaran." Innarsu ta amsa da suna nan lafiya lau, hajiya ta ce masha Allah kafin ta ɗaura idonta akan aunty Kubra da ta cire glasses ɗin fuskarta tun shigowarsu, "Ita wannan ban gane ta ba." Hajiya ta faɗa tana ta murmushi, innarsu Salma ta ce ƴar'uwarta ce ita ce Salma ke wurinta a Kaduna, hajiya ta ɗaga kai tare da furta, "Allah Sarki, an zo lafiya." Aunty ta amsa mata da lafiya lau da murmushi, hajiya ta maida kallon ta kan Salma ta ce, "Ƴar kunya muka koma ne Salma da aka kasa kallo na, bayan kin saye mani zuciyar miji sannan zaki zo kina kunya ta" Duk su aunty suka yi dariya, ta ƙara cewa, "Ya Kadunan?" A hankali Salma ta ce lafiya lau, ɗan shiru suka yi kafin hajiya ta ce, "An tsaida lokaci kuma, Allah Ya sa alkhairi Ya nuna mana." Aunty ce ta amsa da Amin Ya Rabb, kafin a nutse ta sake cewa, "Dama zuwa muka yi mu yi godiya hajiya kan hakan da kuma abun arziki da aka yi mana na cewa ba a buƙatar kayan ɗaki, mun gode ƙwarai, Allah Ya saka da alkhairi Ya ƙara girma da arziƙi." Murmushi ne akan fuskar hajiya ta amsa da Amin, ta ce, "Ai ba wani abu bane, dama shi angon ne ya ce baya buƙatar komai, don da an ɗaura aure zai tafi da ita can in da yake, anan kuma gidan shi da zasu rinƙa sauka idan sun zo akwai komai, to babu wani amfanin yin kayan ɗakin." Duk suka jinjina kai, bayan ɗan shiru hajiya ta kalli aunty da murmushi ta ce, "Ke a Kaduna kike zaune ke nan, duk ya yara da maigida." A hankali aunty ta ce, "Eh a can nike aiki.." Daga haka ta yi shiru, innarsu Salma ta ce, "Da yake Allah bai bata haihuwa ba." Hajiya ta ɗan girgiza kai da ɗan nuna jimami ta ce, "Allah Sarki, komai lokaci ne, in da rabo za a samu in sha Allah." Innarsu Salma ta ce, "Haka ne...saboda matsalan ma ba auren yanzu." Hajiya ta hau girgiza kai tana kallon aunty da kanta ke a ƙasa, duk da bata ɗago kai ba kana kallon ta zaka gane maganar innarsu Salma ta saka ta a damuwa, cikin kwantar da murya hajiya ta ce, "Haka Allah yake ikonSa, idan ya so sai ya jarabi bawa ta kowacce hanya, ba don kuma baya son sa ba sai don ya jaraba imaninsa. Ki ci gaba da haƙuri, in sha Allah a gaba zaki haɗu da rabon da Allah Ya tanadar maki sakamakon imani da kika yi da ƙaddaran da ya aiko maki." A hankali innarsu Salma ta ce in sha Allah, aunty ta ɗago kai da ɗan murmushi ta ce, "Nagode sosai hajiya." Hajiya ta ce ba komai kafin ta ce an bar su ba a kawo masu ko ruwa ba, innar su Salma ta ce ai da yake ma rana bata yi ba sosai, hajiya ta ƙwala ma Balaraba kira, bayan ta fito bakin kitchen hajiya ta ce ta kawo ma baƙi ruwa da lemu ta amsa da to tare da juyawa, dawowa ta yi hannunta riƙe da tray ta ɗauro bottle water guda biyu da lemuna sai cups, sai da ta ƙaraso cikin falon suka haɗa ido da Salma da ta ɗago tana kallon ta da murmushi, bayan ta ɗaura tray ɗin a saman table ta ɗago tana kallon Salma da faffaɗan murmushi ta ce, "Salma an dawo.." Hajiya ta juyo tana kallon Salma ta ce, "Amaryar mu ce ta zo gaishe da kishiyarta da ta ƙwace ma miji." Salma ta sunne kai tana dariya, itama Balaraba dariyar ta yi ta ce ma Salma an zo lafiya ta amsa mata, "Ma sha Allah, sai na ga har ta canza." Balaraba ta faɗa tana ta kallon Salma, hajiya ta ce, "Eh, ba laifi har girma ta ɗan ƙara tubarkalla, gashi da gani auntyn tata kayan daɗi take bata, sai sheƙi take yi tun ma ba a ɗaura auren ba, wannan idan ban yi da gaske ba sai ta raba ni da shi gaba ɗaya." Duk suka yi dariya aunty na faɗin a'a baza ta yi haka ba don duk aje a dawo da tsohuwar zuma ake magani, Balaraba ta zuzzuba masu lemu, bayan ta ɗago hajiya ta tambaye ta ta gama abinci ne, ta ce a'a ta dai kusa, kallon Salma ta yi ta ce, "Salma an saka rana kuma, Allah Ya nuna mana." Salma ta yi shiru tare da sauke kai ƙasa, su aunty suka amsa da Amin daga haka ta nufi komawa kitchen, hajiya ta ce, "Haka Allah ke ikonSa, a nan gidan suka fara haɗuwa, gashi soyayya ta ƙullu har ana maganar aure." Duk suka yi murmushi, "Ya kuke da ita auntyn tata?" Hajiya ta tambaya idonta akan innarsu Salma, innar ta gane aunty Kubra take nufi, ta ce, "Da babanta da nawa uwa ɗaya uba ɗaya suke." hajiya ta jinjina kai ta ce alaƙa ce ma ta kusa sosai, ta sake cewa, "Ke nan itama ƴar nan ce?" Innar su Salma ta ce, "Eh a nan aka haife ta, amman iyayenta a Kaduna suke zaune, a can mahaifinta ya yi aiki, mahaifiyarta kuma Allah Ya yi mata rasuwa, sai itama yanzu nurse ce tana aiki a can Kaduna." Hajiya ta jinjina kai tare da furta, "Ma sha Allah, Allah Ya ƙara taimako Ya jikan mahaifiyar tata." Duk suka amsa da Amin, bayan ɗan lokaci hajiya ta ce, "Gashi muna ta magana ban san sunan ki ba." Aunty dake murmushi ta ce sunanta Khadija amman Kubra ake kiranta, hajiya ta ɗan jinjina kai ta ce, "Ki ce mai babban suna ce, sunan mahaifiyata ke nan Allah Ya jiƙan rai." Duk suka haɗa baki wurin cewa Amin tare da yin addu'ar rahama a gare ta, daga haka suka yi mata sallama za su tafi, ta ce ba za su tsaya su ci abinci ba an kusa gamawa, duk suka ce sun gode, kallon Salma ta yi cikin wasa ta ce, "To ke kin zo ke nan ko, ba sai an sha wahalan kawo mana ke ba." Salma ta sunne kai tana murmushi, miƙewa hajiya ta yi ta ce masu tana zuwa ta nufi hanyar ɗakinta, bada jimawa ba ta dawo hannunta riƙe da wata ƴar babbar leda, ta miƙa ma innar su Salma ta ce gashi nan a ba mamanta ta yi amfani da su, suka haɗa baki wurin yi mata godiya ta ce ba komai ai an zama ɗaya, daga haka suka yi sallama suka miƙe za su tafi, hajiya ta tambayi Salma ta zo ke nan har biki ko zata koma, aunty ta ce eh zata barta anan amman zata koma Kadunan kafin bikin sai ta dawo idan lokacin ya yi, hajiya ta jinjina kai ta ce to Allah Ya kai su lokacin da rai da lafiya, duk suka amsa daga haka suka tafi, hajiya ta bi aunty Kubra da kallo yayin da suka nufi ƙofa, a ranta take raya in baya ga wulaƙancin wasu mazan yanzu wannan koda bata haihuwa ai mutum ya zauna da ita yadda take tubarkalla mace har mace sai dai daman wasu basu iya samun dama ba. Bayan sun koma suka duba abun da hajiya ta ba aunty kubra, suka ga tsadaddan lace da kuma atamfa ne, sosai aunty Kubra ta ji daɗin kyautar ta kuma yaba da kirkin hajiya. Ranar lahadi aunty Kubra ta shirya komawa Kaduna, sosai ta ji zata yi kewan babynta don ba tare za su koma ba kamar yadda ta sanar da hajiya, sai bikin ya matso zata je can ta ƙara shirya ta, duk da ta faɗa ma innarsu bata buƙatar wasu magungunan gyara sosai saboda shekarunta, amman ta taho mata da maganin sanyi mai kyau da zata rinƙa sha, duk da ba wai ya bayyana tana da shi bane, sai dai a cewar aunty wani lokacin ba a gane yarinya tana ɗauke da shi sai bayan an yi aure, a zo ai ta fuskantar matsala a mu'amala daga yin aure, sannan kuma ta ce ma innar su a rinƙa bata abinci mai kyau da kayan itatuwa, itama Salma sosai ta ji har ta fara kewan auntyn tata.