← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 197

Sashe 20

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba wani dalili ya sa na zauna ba ni ke ra'ayin hakan, na tsaya yin wani abu, da kin zo bayan yanzu za ki iske ni a kwance ne." Daga yanayin yadda ya yi maganar ta fuskanci alamun bacin rai akan fuskar sa, ɗan ta6e baki ta yi ba tare da ta ce komai ba ta fara tafiya zata bar ɗakin, sai da ta yi taku biyu zuwa ukku ta dakata tare da juyowa ta kalli Deen da ya bita da kallo, cike da bada umarni ta furta, "Fallow me, I want to talk to u. " Daga haka ta ci gaba da tafiyarta, ɗan jim ya yi kaman ba zai tashi ba, kallon Fahad ya yi da har lokacin bai ɗago ba, shiru ya ɗan yi ya ma rasa mi zai ce mashi don duk da bai ga yanayin fuskarsa ba ya san dole maganar da mom ɗin ta yi ta 6ata masa rai, hannu ya kai ya ɗan ta6a ƙafar Fahad dake gefen sa ya furta, "Ina zuwa ya Fahad." Kai kawai Fahad ya jinjina masa ba tare da ya kalle shi ba, zuro gudar ƙafarsa ya yi ya sauka daga gadon ya bi bayanta. A hankali Fahad ya ɗago ya bi hanyar fita daga cikin ɗakin da kallo yanayin fuskar sa da ɗan alamun bacin rai, a cikin ransa yana jin ɗacin irin abubuwan da matar take mashi, shi dai ya san bai ta6a yi mata wani laifi da ya cancanci wannan tsanar ba daga gare ta, duk da ya san halinta ne bashi kaɗai take ma hakan ba amman nashi ya fi tsanani, sam bata son shi da Deen ga shi Allah Ya saka masu ƙaunar junan su kuma ga zumuncin da Allah Ya halarta a tsakanin su, ba don haka ba ai da tuni ya rabun mata da ɗa. Maida akalar tunaninsa ya yi kan Leemarh, daga abun da ya faru yau a wurin dinner ya tabbatar mashi da yarinyar son shi take kamar yadda yake hasashe, duk da shi bai ta6a tunanin ya yi soyayya da ita ba, amman in har ta bayyana mashi hakan to tabbas ba zai ƙi amince mata ba, duk da a yadda take ta yi mashi ƙaranta da kalar matar da yake son aura, a yadda yake so ya auri budurwa babba irin wadda ta gama karatun jami'a koma take aiki, amman duk da hakan yana jin zai iya auran Leemarh don tana da duk wani abu da namiji zai so a tare da mace, saidai ta ya hakan zai yuwu a tsakanin su a irin yadda mahaifiyarta ta tsane shi? Ana yin aure ne don samun farin ciki da natsuwa, amman baya tunanin hakan zai samu matuƙar aure ya kasance tsakanin shi da Leemarh, ƙarshe ya san madadin hakan ya ƙara masu danƙon zumunci yana iya lalata zumuncin wanda shi sam ba zai so hakan ba. Ahalin su babban family ne da suke da zumunci mai ƙarfi, suna da kyakkyawar alaƙa da kuma fahimta ba zai so a ce ta sanadiyyar auren su ba an zo an samu 6araka, don a yadda ya san rashin mutuncin mom Jameela to zata aikata abun da zai iya haddasa a samu babbar matsala matuƙar bata son hakan. Yin wannan tunanin ya sa shi fara tunanin hanyar da zai bi wurin ganin Leemarh bata furta mashi kalmar so ba duk da zai so a ce ya cika mata burinta, saidai baya tunanin hakan mai yuwuwa ne gara su haƙura kawai ko don a zauna lafiya. Bayan daukar ɗan lokaci yana tunane-tunane, saukowa ya yi daga saman gadon ya mike tsaye, cikin ɗakin ya nufa walking slowly, wurin da madaidaicin fridge yake ya nufa ya buɗe, bayan ya ɗauko lemu ya dawo cikin ɗakin riƙe da shi, a bakin gadon ya zauna har zai fara buɗe marfin lemun sai kuma ya dakata kamar yana ɗan tunani, wani abu yake son ɗaukowa a cikin motar shi sai dai yana tunanin ko su Deen na a cikin falon bai son ya je ya ratsa su suna magana, ɗan jimm yay can ya miƙe tare da ɗaura roban lemun a saman durowar gefen gadon, sai da ya buɗe durowan farko ya fiddo makullin mota kafin ya nufi ƙofar fita.

Cikin sa'a bai iske su a cikin falon ba, har ya nufi ƙofar fita ya tuna da akwai wata kofa ta cikin falon da zata fidda mutum ta bayan gidan ta fi sauƙi zuwa inda parking space yake, juyowa ya yi ya nufi ƙofar cikin sa'a da makulli a jikinta ya buɗe ya fita.

Lokacin da Deen ya fito ya yi tunanin zai ga mom ɗin ta shi a cikin falonsa amma sai ya ga akasin hakan, hanyar fita ya nufa da tunanin ko bangarenta ta koma, tsaye take ta ɗaura hannuwanta a saman ƙarfen bene idanunta na kallon cikin ƙaton falon na su dake a ƙasan bene ta haɗe rai,

"Mom..." Ya furta bayan ya ƙaraso ya tsaya daga gefenta, shiru bata amsa ba bata kuma juya ta kalle shi ba, "Kin ce kina son magana da ni." Ya sake faɗa yana mai kallon ta ta gefe, a hankali ta juyo da fuskarta ta kalle shi kafin ta ƙarasa juyowa gaba ɗaya tana fuskantar sa,

"Wai mike damun ka ne Deen?? Ta faɗa da amon bacin rai, ɗan buɗa idanunsa ya yi alamar rashin fahimta, ba tare da ta jira cewar sa ba ta ci gaba, "Har sai yaushe ne zaka dawo cikin hankalinka ne ka rinƙa yin abu yadda ya kamata?Yaushe ne zaka daina cutar kanka ka daina prioritizing buƙatun wasu fiye da naka? Yaushe zaka gane cewa wasu mutanen ba kamar yadda kake ɗaukar su bane, ba don Allah suke tare da kai ba face don amfanin kan su ba kamar saboda baiwar da Allah Ya yi maka, da zarar sun gama cin moriyar ka za su guje ka ne. I have been trying to make you understand all these things over and over again, but you just don't get it! Yakamata ka dawo cikin hankalinka, Deen!"

Idanunsa akanta har ta gama maganganun nata, sai dai shi sam ya rasa gane kan maganganun balle ya fahimci akan mi take faÉ—an,

"Mom, kina magana akan miye ne? I don't get u..."

A É—an fusace ta ce, "Dama ta ya zaka fahimce ni tun da an riga an makantar da kai, baka ji baka gani balle ka fahimta. Ina magana ne akan wancan mutumin mara tunani." Ta yi maganar tare da yin nuni da kofar part É—in sa, da yanayin mamaki ya ce, "You mean ya Fahad! Minene ya yi na rashin tunani?"

"Idan ba rashin tunanin ba ta ya yana ganin yau fa ka zo ƙasar nan, baka samu ka huta ba sosai maimakon ya taimaka maka ka kwanta ka huta amman shi ne a kwance a saman gadonka ɗare-ɗare ba ko kunya kai kuma bawansa a zaune!" Yanayin fuskarsa ne ya sauya zuwa yanayin bacin rai, bin ta ya yi da ido a ransa yana mai mamakin yanzu miye wani abu a cikin hakan da har zatai ta yin faɗa,

"Oh, baka da ma abun da zaka ce mani ke nan? ka wani bi ni da ido ga mahaukaciya na magana ko?"

Ɗan yamutsa fuska ya yi cikin alamun bacin rai ya ce, "To mi kike so in ce ne? Yanzu mom don Allah miye abun tashin hankali a ciki da zaki ta faɗa? I think i have already told you, ni ne ban kwanta ba na tsaya yin abu, ko kuwa ni ƙaramin yaro ne ban san ciwon kai na ba da sai wani ya faɗa mani in kwanta kafin na yi hakan? Idan shi yana buƙatar ya kwanta ya huta sai ya ƙi yin hakan saboda ni ban kwanta ba? Ko kuwa don yana gadona sai ya zama ya yi laifi don ya kwanta a sama? Dama abuna ba na shi bane, har akwai wani bambanci a tsakanin mu....?

Have you forgotten that he is my brother? A gidan nan fa ya taso da har zaki ce wai da wani dalili yake tare da ni, idan ya gama cin moriyata zai guje ni. Ok mu dauka ma haka ne, to me, it's fine, zan yi faran ciki a ce ina da abun da ɗan'uwana zai amfana, koda ni zan rasa hakan bai dame ni ba, what would really hurt me is if he ever turns his back on me...that’s what would matter." A hasale ta katse shi,

"Enough Deen! Saboda ina faÉ—a maka gaskiya zaka tsaya akai na kana mani wannan surutan! I'm your mother, dole na damu da kai na baka kulawa daga abun da nike ganin zai cuceka saboda tunanin mu ba É—aya bane kai ba zaka gane abun da nike hango maka bane, sannan sam ni bani son tarayyarka da shi don zai iya saka ka ka lalata rayuwarka kamar yadda ya lalata tashi rayuwar da shaye-shaye..." ÆŠan jujjuya kai ya yi jin abun da kuma zata fake da shi, yanayin idanunsa har sun É—an sauya kala, wllh ya gaji da wannan halin na mahaifiyarsa, son kanta ya yi yawa, bai san mi yasa ta tsani Fahad haka ba wanda sam hakan bai mashi daÉ—i don kuwa idan akwai mutumin da yake jin shi a cikin ransa bayan su iyayensa to kuwa Fahad ne,
Chapter 20 · 0% Book details