← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 197

Sashe 77

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Daga gidan rasuwan muke muka yo ma iyayen yaron gaisuwa. Mutane ana cikin hali, irin wannan ba sani mutum ke yi ba idan ba an zo an faɗa ba, ko yaya ne idan an zo in faɗa halin da ake ciki ba a rasa taimakon da za a yi, duk da ya ce ya zo nan gida wuri na har sau biyu bai samu gani na ba, saboda mutanen da ke zuwa yanzu sun yi yawa saboda zuwan Deeni." Gyara zama baban su Salma ya yi ya ce wllh al'amurra yanzu sai godiyar Allah, nan ya shiga faɗa mata halin da mahaifin Habu da iyalinsa suke ciki duk sanadiyyar rashin yi masa sallamar kirki bayan aje aiki, bayan ya gama innarsu Salma ma ta ɗora da faɗin abubuwan da ta sani har da zuwan da Habu ke yi gidan da yadda wasu lokuttan Salma ke bashi abincinta su je su ci da ƴan'uwansa da sauran alkhairai, har da yadda ta sa a basu kuɗi a cikin wanda Deen ya basu don a mayar da yaran makaranta, ashe ba rabon shi Habun ya koma, hajiya da ke ta ɗan murmushi ta ce, "Maa sha Allah, hakan abu ne mai kyau, yadda take tausayi da kyautata ma mutane itama in sha Allahu Allah zai tausaya mata Ya kyautata rayuwarta." Duk suka amsa da Amin, innarsu Salma ce ta miƙe da sauri tana faɗin su yi haƙuri sun zo an barsu ba a kawo masu ko ruwa ba, dakatar da ita hajiya ta yi ta ce mata ba sai ta kawo ba ai safiya ne, sallama ta yi masu ta ce tun da an gaisa, Deen ya fara miƙewa suna ƙara yi masa godiya ya nufi hanyar fita Sagir na daga gefensa. Bayan sun koma gida Deen ya zauna da hajiya kan taimakon da yake son yi ma baban Habu, sannan ya nemi shawararta kan wani aiki da ya yanke yana son ba Salma a ƙarƙashin foundation ɗin shi, bayan ya bayyana ma hajiya aikin wanda abinci ne yake son za su nemo mutane da za su rinƙa dafawa ana raba ma mutane, ita Salma so yake ya ɗaura ta akan abun wato ta rinƙa kula da komai sannan ta rinƙa bincika masa mutanen da ta ji suna cikin buƙatar taimako sosai, hajiya ta goyi bayan hakan ta ce sadakar abinci yana da falala sosai duk da dama suna yi cikin azumi, ta ce kuma aikin dafa abincin zai taimaka ma matan da za su rinƙa yi tun da albashi za a rinƙa biyan su, har ta bada shawarar a saka wata daga cikin matan baban Habu a aikin idan suna so hakan zai taimaka masu sosai, sai dai a yadda ya bayyana mata kowacce rana za a rinƙa yin abincin ta bada shawarar a rinƙa yi sau biyu ko ukku a sati don yi kullum ɗin zai iya kashe ma wasu zuciya musamman magidanta, sannan ta nuna mashi akwai wasu buƙatun da ake taimaka ma mutane da su, daga baya ta tambaye shi aikin da yake son Salma ta yi yana ganin ba zai ta6a karatunta ba gashi an ce tana son karatu sosai kada a takura mata, ya ce yana ganin ba zai shafi karatunta ba tun da ita hajiya zata rinƙa providing masu komai na yin abinci ita Salma kamar zata saka ido ne kan yadda komai ke gudana kuma ita zata rinƙa zuwa wurinta tana amsar ma masu aikin abubuwan da ake buƙata, hajiya ta ce ta fahimta lafiya lau ya yi magana da Salma ta tuntun6i mahaifiyarta sai a ji idan suna son aikin, ya ce ok zuwa anjima ta sa a kira mashi Salmar tun da bai da lokaci sosai ya kusa tafiya. Wuraren azahar hajiya ta kira innarsu Salma ta tambayi ta dawo daga makaranta innar ta ce a'a ta dai kusa, hajiya ta ce mata to idan ta dawo ta huta zuwa anjima tana nemanta, bayan Salma ta dawo sosai ta yi mamakin jin hajiya ta zo nan gidansu kuma har da Deen, bayan ta ci abinci innarsu ta saka ta ta yi wanka don ta tafi kiran da hajiya take mata, shiryawa ta yi ta saka riga da skirt na atamfa glitter da ta yi mata kyau sosai, ta yi ɗaurin kallabi mai steps, bayan ta gama ta ɗauko mayafi wanda dama mahaɗin kayan ne ta yafa, lokacin da ta fito innarsu na a zaune tsakar gida da su Imrana, nan suka hau cewa ta yi kyau, tana ɗan murmushi ta ce ma innarsu ita da ba wata kwalliya ta yi ba ko powder bata shafa ba kawai puff ɗin powder ne ta goge fuskarta sai ɗan lip gloss da ta shafa, innar su ta ce, "To ai ke dama fatar ki kalar powder ɗin ce, ko baki shafa ba sai fuskar ki ta yi kaman kin shafa." Dan murmushi ta yi kawai ta ce mata sai ta dawo daga haka ta tafi. Balaraba ta fito daga kitchen jin ana sallama, ganin Salma ta yi murmushi ta ce, "Salma ce.." Ta amsa mata tare da gaishe da ita, bayan ta amsa Salma ta tambaye ta hajiya na nan ta ce eh tana ɗaki bari ta yi mata magana, bada jimawa ba ta fito ta ce mata tana bedroom ta ce ta shiga, Balaraba ta yi mata jagora zuwa ɗakin hajiya wanda yau ne karon farko da zata fara shiga, bin ɗakin Salma ta yi da kallo bayan sun shiga wanda babban ɗaki ne da ya tsaru da lafiyayyun furniture kai ka ce ba ɗakin tsohuwa ba, Salma taita kallon gadon hajiyan na alfarma, ba abun da ya faɗo mata a rai sai ranan nan da Deen ya ce kuɗin wandonsa zai siya gadon, a ranta ta shiga raya ko da wasa yake ganin katafaren gadon, suna shigowa hajiya dake a kwance saman gado ta yunƙura ta tashi zaune tana ɗan murmushi, nufar wurin gadon ta yi ta duƙa daga gefe tare da gaishe da hajiya ta amsa mata, wayarta da ke ajiye gefe ta kai hannu ta ɗauka ta fara latsawa kafin ta kai kunne, kusan sau ukku tana yin kira da alama ba a amsawa, ƙoƙarin sake yin kiran ta yi still ba a yi picking ba, a fili ta ce, "Ina Deeni ya shige ne...ina ta kiran waya baya ɗagawa." Kallon Salma ta yi ta tambaye ta lokacin da ta shigo ko ta ga Deeni? Salma ta ce mata a'a, ta sake tambayarta ta ga Sule dirabanta a harabar gidan Salma ta ce shima bata gansa ba, shiru hajiya ta ɗan yi alamar tunani can ta ce, "Ina tunanin yana a can part ɗin su don ɗazun da ya gama cin abinci ya ce mani jikinsa ya yi nauyi zai je can ya motsa don a can yake da kayan motsa jikin, ƙilan shi ya sa baya ɗaga kiran." Ita dai Salma shiru ta yi tana kallonta, "Dama shine yake neman ki, ko zaki je ki duba shi a can?" Da alamar rashin fahimta Salma ta tambaye ta ina zata je, kwatancen part ɗin su ta yi mata ta ce idan ta je sai ta ƙwanƙwasa kofar ta ga idan yana can ta san ma bai wuce yana can ɗin, amsawa Salma ta yi da to tare da miƙewa, tana tafiya a ranta tana tunanin ko neman mi yake mata, tun kafin ta ƙarasa part ɗin a ranta take yaba haɗuwar shi, a bakin tangamemiyar kofar part ɗin ta tsaya gabanta har ɗan faɗuwa yake, a ɗarare ta kai hannu ta fara knocking, tun tana yi a hankali har ta koma tana yi da ƙarfi, jin shiru ba a buɗe ba ya sa ta fara tunanin ko bai a part ɗin, bayan ta ɗan ƙara ƙwanƙwasawa ta yanke ƙilan baya nan, tana niyyar juyawa zuciyarta ta bata ta murɗa handle ɗin kofar ƙilan a buɗe take, kama handle ɗin ta yi ta murɗa daidai lokacin ta ji an ja kofar ta ciki, gaba ɗaya ta tafi sakamakon jan kofar da aka yi da ɗan ƙarfi, da sauri Deen ya kai hannuwansa ya tare ta ta hanyar dafe shoulders ɗinta, still ya yi yana kallon fuskar Salma da ta runtse idanu jikinta na ɗan rawa ya yin da idanunta ke ɗan motsawa daga gani ta tsorata sosai, a hankali ta fara buɗe idanunta suka shiga cikin na Deen dake ta kallonta, bugun da ƙirjinta ke yi ne ya ƙaru ganin a yadda yake daga shi sai wando 3 quarter ba riga, daga gani cikin motsa jikin yake don duk fatar jikinsa ta jiƙe da zufa, sumarsa ta manne masa a wuya, ya rataya ɗan madaidaicin farin towel, da sauri ta janye idanunta daga barin kallon shi, a hankali ya ɗauke hannayensa daga saman shoulders ɗin ta, daga yanayinta ya fahimci tsoro a tattare da ita calmly ya ce, "I'm sorry, kin ji tsoro?" Ɗan motsa baki ta yi ba tare da ta kalle shi ba a hankali ta ce, "Da na zo inata yin knocking ba a buɗe ba, na yi tunanin ko kofan a buɗe take shine na murɗa." Idonsa a kanta ya ce bai ji knocking ɗin bane saboda headphones da ya saka sai daga baya, ta ɗaga kai kawai, tana niyyar ƙara yin magana ya riga ta cewa hajiya ta turo ta? Lokacin ta ɗan ɗaga ido ta kalle sa ta ce mashi eh tana ta kiran shi a waya bai ɗauka ba, kai ya ɗaga kafin ya ce mata ta je daga can gefen part ɗin akwai rumfa a wurin ta zauna yana zuwa, a hankali ta ce masa to tare da juyawa ta nufi inda ya nuna mata still gabanta na ɗan faɗuwa saboda abun da ya faru....

*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*

_New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_

ZAINAB BATURE

28
Chapter 77 · 0% Book details