Sashe 58
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
"Ai ba a gama ba gaba ɗaya, na san sai daga ƙarshe zamu samu kyaututtuka." ta ce, "To amman wace buƙatan kuɗi ce da kai? ina bada daɗewa ba ka zo ka ce in cika maka kuɗi zaka siya sababbin kayan ƙwallo da takalma na ɗauka na baka? Bayan su wace buƙata ce kake da ita? Koda ka ga ina bata itama na daɗe rabon da in bata kuɗi ta siya abun buƙata kuma ba tambaya ta take ba." Ɗan sosa kai ya shiga yi ya ce mata shi dai don Allah ta bashi ba sai ta ji buƙatan ba, Salma ta ce, "Innarmu kar ki bashi, yanzun haka wannan Fa'izar zai kashe ma su, kuma wllh wahalar banza kake yi don wannan yarinyar ba samunta zaka yi ba, su da suna gama makaranta gidansu ake yi masu aure, kuma mate ɗita ce nan da shekara ɗaya zata gama, ko kana tunanin zaka iya aurenta zuwa lokacin?" Hannu ya ɗaga zai make ta innarsu ta dakatar da shi cikin ɗaga murya ta ce kada ya sake ya ta6a ta ai gaskiya ta faɗa, "Ni dai innarmu ki bani don Allah, ƙarya take mani don ni wannan yarinyar tuni ma na rabu da ita." Ta6e baki ta yi ta ciro dubu biyu ta miƙo masa ya amsa yana faɗin duka dubu biyu za a bashi, ta miƙo hannu tana faɗin, "Idan baka so to ka bani abu na, duk kuɗin ba a hidiman gida za su ƙare ba, babanku ma na bashi wasu a ciki." Tura kuɗin ya yi cikin aljihun wandonsa, ya kalli Salma cikin ɗaure fuska ya ce, "Munafuka yar hana ruwa gudu kawai, wllh saboda mugun halin ki har na fara ji na ƙosa ki yi aure ki bar gidan nan." Tana dariya ta ce, "Ka sha kuruminka man Sagir, bada jimawa ba ma ai zan tafi makaranta Kaduna." Yana hararanta ya ce, "Ai wannan still ba hutawa muka yi ba tun da za a rinka yi maki buƙatu kuma za ki rinƙa dawowa, amman idan kika yi aure shike nan ba ruwan mu da ke, duk nauyin ki ya koma kan mijinki sai kuma in kin kawo ziyara." Ɗan girgiza kai Salma ta shiga yi tana ɗan murmushi ta ce, "Allah Sarki Sagir, ka ga ni har zullumin abun da zai saka in rabu da ku nike yi, ba komai, amman ka rubuta ka ajiye wallahi duk ranar da na bar gidan nan da sunan aure sai ka yi kuka da idanunka." Tsoki ya buga ya nufi hanyar banɗaki yana faɗin Allah ya kyauta ya yi kuka don sun rabu da ƙaya, innarsu dake murmushi ta ce mata ta rabu da shi, da ƙyar Salma ta amsa kuɗin amman sai da ta rage ta mayar mata da wasu suka yi sallama ta tafi.