Sashe 173
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Deen ɗin ya yi masa magana kan ya shirya auren ta zai amince, sai dai shi Deen bai san dalilin matsawar da Basman ke masa ba kan hakan. Salma ta ji tana son sanin abun da ya tsaya mata a rai, tana kallon Deen ta ce, "Amman ya Deen ya aka yi ka fara so na." Murmushi ta ga ya yi yana ɗan lumshe ido ya ce mata shima bai san yadda aka yi ba, wayarsa ya ɗan lallatsa ya miƙo mata ya ce , "I think daga wannan ne." Salma ta amshi wayan, mamaki ne ya bayyana akan fuskarta ganin hoton ta, taita kallon hoton tana son tuna yaushe ta yi shi, daga yanayin hoton da alama ma ba tare da sanin ta aka yi shi ba, a hoton ta ɗan juyo fuskarta ta yi murmushinta mai burgewa kanta a buɗe, yayin da sumarta ke a sake ta yi ma kanta rumfa, sai daga baya ta lura Sageer ne ya ɗaura hoton a status shine Deen ya yi screenshot, a jikin hoton an yi caption ɗin, "My beautiful sis...son kowa ƙin wanda ya rasa." Har da love emoji a caption din, a ranta ta raya Sageer ke nan, a fili ya bayyana yana son ta ya damu da ita amman kuma yai ta cin zalinta, kallon Deen ta yi tana murmushi tace ita bata ma san lokacin da aka yi hoton ba, "...daga nan sai ka fara so na?" Ta tambaya tana kallon shi, yana murmushi ya ce mata kawai dai hoton ya yi masa kyau shiyasa ya ɗauka, kuma kusan kullum sai ya kalli hoton to daga nan ya fara developing feelings akanta, dama akwai abubuwan da suke burge shi tattare da ita, Salma ta yi murmushi tare da ɗan langa6e kai tana kallon shi, ya ɗage mata gira ya ce ita ya akai ta fara son shi, ta ce, "Kawai kana bayyana mani na ji nima ina son ka, dama nima akwai abubuwan da suke burge ni a tare da kai." Ya yi mata wani kallo ta yi yar dariya....daidai nan wayarta da ke ajiye a jikinta ta fara ringing, dubawa ta yi ta ga aunty ce ta kira ta, bayan ta ɗauka ta kai kunne, daga ɗayan bangaren ta ji muryar aunty ta ce, "Love birds...haka ake yi sai ki riƙe mutum ba zaki shigo da shi ko ruwa ya sha ba." Ƴar dariya Salma ta yi bata ce komai ba, aunty ta ce mata ta shigo da shi ya ci abinci ta amsa da to, bayan ta cire wayan ta juya ta kalli Deen da ya jingina da seat ya ɗan lumshe ido, ta ce, "Auntyna ta ce mu shiga ciki." Slowly ya buɗe idanun shi kanta, ta ce mashi su je ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce ok, tana kai hannu zata buɗe ƙofar ta ji an buɗe mata daga waje, shima Deen ta ɗayan bangaren aka buɗe masa, Salma ta fito tare da kallon mutumin da ya buɗe mata ƙofa, a ranta take raya ashe wai suna nan suna ta tsayuwa su kuma aikin su ke nan, zagayowa Deen ya yi 6angaren da take ya yi mata alamar su je suka fara tafiya a nutse sun jera, duk da Salma na da ɗan tsawo amman data jera da shi sai ta koma gajera don ko kafaɗar shi kanta bai ƙarasa ba, gashi sai ta yi ƴar ƙarama a tare da shi saboda ƙirar jikin shi. da ƴar siririyar sallama ya shigo cikin falon, Salma na gaba bayan sun shiga ta juyo tana murmushi ta nuna mashi kujera ta ce ya zauna bari ta kira auntynta ya ɗaga mata kai, tare suka fito da aunty Kubra tana biye da ita jikinta sanye da doguwar rigar lace, da murmushi ta ƙaraso wurin kujerun idonta akan Deen dake zaune ya ɗaura hannuwansa akan kafafunsa, aunty ta zauna a kujerar dake gefe da tashi fuska a sake ta ce, "Deen, sannu da zuwa." Cikin nutsattsiyar muryarsa ya amsa tare da gaishe da ita, "Ya ka baro familyn ka." aunty ta faɗa tana faffaɗan murmushi, ya amsa mata da duk suna lafiya, ta sake cewa, "Ma sha Allah...sannu." Shiru suka ɗan yi idon aunty akan shi shi kuma har lokacin bai kalle ta ba, ita kanta ganin abun take kamar mafarki mutumin da iya a tv da waya take ganin shi yau shine zaune a gabanta, aunty ta sake cewa, "Mun ga abubuwan alkhairi da suka wakana, Allah Ubangiji Ya ƙara ma rayuwa albarka, Allah kuma Ya ƙara bada sa'a Ya tsare." Sai lokacin ya ɗan ɗago ido ya kalle ta da ɗan murmushi ya ce, "Ameen Ya Rabb. Nagode sosai." Aunty ta ce ba komai, ta kalli Salma suka haɗa ido tana ta yin murmushi, aunty ta maido idonta akan Deen tana murmushi ta ce, "Sai kuma muka ji wani abun farin ciki a kan baby...Allah Ya tabbatar mana da alkhairi." A hankali ya amsa da Amin kafin ya ɗan kalli Salma suka haɗa ido suka ɗan sakar ma juna murmushi, aunty da ke kallon su ta janye idanunta still da murmushi kan fuskarta, juyowa ta yi ta kalli Salma ta ce, "Baby go with him and serve him some food." Salma ta amsa da to tana miƙewa, aunty ta kalli Deen a tausashe ta ce mashi ya je ya ci abinci, slowly ya amsa da ok tare da miƙewa suka nufi dining tare da Salma yana tafiyarsa mai cike da natsuwa, aunty ta bishi da kallo a fili ma sai ta ga ya fi kyau, a cikin rai take raya idan ka ganshi kaman ba zaka ji hausa ta fita daga bakinsa ba, miƙewa aunty ta yi ta nufi komawa bedroom a rai tana faɗin in dai baby ta aure shi lalle ba ƙaramin dace ta yi ba...Salma ta ja masa kujera tana kallon shi da murmushi bayan sun zo dining ɗin, ya yi mata wani kallo da ɗan murmushi kafin ya zauna, bubbuɗe abubuwan abincin masu kyau da aji ta shiga yi, ta ɗago ta kalli Deen tana dan langa6e kai ta ce mi yake so ya fara ci, ya ɗan lumshe mata ido ya ce komai ya yi mata, "Akwai awara ko in fara zuba maka ita?" Ya ɗan yi shiru yana kallon ta sai kuma ya ɗaga mata kai, awaran ta fara zuba mashi a cikin wani haɗaɗdan plate na ƙawa, tana cikin zubawa ta kalle shi ta ce, "Ka ƙara cin ta bayan da ka bar Funtua?" Slowly ya girgiza mata kai alamar a'a, enough ta zuba mashi, ta bude warmer ɗin chicken sauce ta zuba a wani bowl mahaɗin plate ɗin, ta zuba masa coleslaw, bayan duk ta zuba komai ta saka masa fork da kuma spoon ta ajiye komai a gaban shi, calmly ya furta, "Thank you." ta langabe kai tana kallon shi, wani irin son shi take jin yana ratsa zuciyarta, hakan ne ya sa take wasu abubuwan ba tare dama ta san tana yi ba, alamar ta zauna ya yi mata da hannu sannan ta zauna saman kujeran gefen shi, a nutse ya fara cin awaran ita kuma tana ɗan ta6a wayarta, bayan ɗan lokaci ya kalle ta suka haɗa ido ya ce itama ta ci abincin, tana murmushi ta ce ai ta riga ta ci tun kafin ya zo, maida idon shi ya yi kan abincin ta ji ya ce miyasa bata ci kaɗan ba idan ya zo su ci tare, ta yi shiru tana murmushi, bayan ya cinye wanda ya kai bakinsa ya ɗan kalle ta ya ce ko ita acici ce bata iya cin abinci kaɗan, Salma ta ɗan yi dariya ta ce, "Idan ni acici ce ka ga ke nan kai ne ka koya mani, don hajiya ta ta6a faɗin hakan akan ka." Ɗan buɗa ido ya yi sai kuma ya yi murmushi mai dan faɗi don ya so ya tuno lokacin...lokaci lokaci Salma ke ɗaga ido ta kalle shi, wani lokacin su haɗa ido ta sakar masa murmushi, sosai ta ji daɗin yadda ya saki jiki yana ta cin awaran kuma da alama ta yi masa daɗi, ganin ya kusa cinye wadda ta zuba mashi ta miƙe tana faɗin bari ta ƙara masa, da hannu ya dakatar da ita kafin ya ce wannan ta ishe shi ya ƙoshi, a ɗan shagwa6e ta ce, "To ai baka ci sauran abincin ba, kuma duk don kai aka yi." Yana bita da kallo yana cin awara a bakin sa, ta ce, "Bari to ko fried rice ɗin in zuba maka." Ba ta jira abun da zai ce ba ta buɗe warmer ɗin haɗaɗɗar fried rice da ta sha vegetables an yayyanka ƙananun nama sosai a ciki sai uban ƙamshi take, tana zuba kaɗan ya ce mata ya isa, ta ɗan yamutsa fuska tana kallon shi ba ta ce komai ba, yana ɗan murmushi ya ce mata ya ci abinci ne kafin ya zo, a shagwabe ta ɗan tura baki ta ce, "To miyasa zaka ci abinci ka san kuma nan dole za a yi maka." Still ya yi yana kallonta don ba ƙaramin tafiya ta yi da shi ba yadda ta yi maganar, ya ɗan lumshe ido ya ce, "I'm sorry princess....ai na ci awaraan sosai." Salma ta ɗan yi dariya don yadda yake fadin sunan awara na mata daɗi, bayan ta zuba mashi coleslaw ta tura plate ɗin gaban shi....sai da ya cinye awaran da ta zuba mashi duka, sosai ta yi masa daɗi ko don ya daɗe bai ci, fried rice ɗin ya fara ci, yana cikin ci suka haɗa ido da Salma, bayan ya cinye wadda ke a bakinsa ƙasa da murya ta ji ya ce ita ta dafa ta, Salma na murmushi ta ce ta yi mashi daɗi ne, a hankali ya ɗaga mata kai, "Aunty ce ta dafa, amman nima na iya yin irinta." Bayan ya cinye wadda ya kai baki ya ce kar wataran ya sata ta yi mashi irin shi ta kasa yi, ƴar dariya ta yi ta ce, "Wllh na iya girka irin ta." Ya ɗan jinjina kai ya ce zai sa ta yi mashi irin shi sai ya gane in da gaske ta iya, tana kallon shi cikin ido ta ce a ina zata girka