← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 197

Sashe 145

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

karatun ta lafiya lau. A koda yaushe addu'ar mu ita ce Allah Ya baki abokin rayuwa nagari, Dr Hisham yana da halin kirki hakan nema ya sa har na kawo maki maganarsa, don da na san ba mutumin kirki bane tun lokacin da ya yi mani maganar zan san yadda zan yi in dakatar da abun. A zamanin nan da maza na kirki suke wahala tabbas na san idan kika samu Dr matsayin miji kin dace, kawai inda nike hangen matsala shine da ya kasance yana da mata, to amman ya tabbatar mani da ba za a samu matsala ba da matarsa, ya ma nuna ba haɗa ku zai yi ba in har ya aure ki har gari ma zai iya raba maku, duk da dai hakan bai sa a guje ma sharrin wasu kishiyoyin, to amma dai idan bawa ya dogara da Allah ya isar masa, sai dai kuma idan baki son shi ba wanda zai maki dole." Shiru Salma ta yi kanta a ƙasa, wasu cikin maganganun aunty sun tuno mata da shawarar da hajiyar Ambasada ta ta6a bata, "Baby ke nike sauraro, ki faɗi mani miye ra'ayin ki kan hakan don tun wuri in san abun yi." A hankali Salma ta ɗago kai ta kalle ta, cikin sanyin jiki ta ce, "Duk yadda kika ce aunty zan amince." Aunty Kubra ta yi saurin girgiza kai ta ce, "A'a baby, wannan abu ne da ya shafi rayuwarki bai kamata wai wani ya yanke maki hukunci ba akai, mu iyaka dai mu baki shawarar da muka ga zata maki amfani." Shiru Salma ta yi don ta rasa mi zata ce, aunty ta lura da kanta ya ƙulle hakan ya sa ta dafa kafaɗarta ta ce, "Ina son ki samu lokaci ki natsu ki yi tunani a cikin zuciyarki, duk abun da kika yanke kada ki ji nauyin sanar mani kin ji." Kai Salma ta ɗaga mata duk jikinta ya yi sanyi, sam bata yi tunanin a lokacin nan za a zo mata da maganar aure ba, kiran aunty aka yi a waya ta miƙe ta nufi ɗakinta tana amsawa, itama Salma miƙewa ta yi ta nufi ɗakinta, bayan ta shiga gado ta nufa ta zauna tana kallon wuri guda yayin da zuciyarta ta shiga dawo mata da fuskar Dr Hisham. Bayan kwana biyu da yin maganar su da aunty Kubra, Salma tana zaune a cikin ɗakinta bayan ta gama sallar issha tana latsa wayarta, turo ƙofar ɗakin aka yi ta ɗaga ido tana kallon aunty da ta shigo, nufo ta ta yi ta tsaya daga gabanta tana murmushi ta tambaye ta mi take yi, Salma ta ce mata ba komai kawai tana ɗan duba waya ne, shiru aunty ta ɗan yi kafin still da murmushi ta ce, "To kin yi baƙo." Har saida gaban Salma ya faɗi jin abun da ta ce, "Dr Hisham ne ya zo yana nan ya shigo ki je ki same sa." Kallon ta kawai Salma ke yi ta kasa cewa komai, aunty ta ce, "Koda baki ji ya yi maki ba ki tsaya ki saurare sa, daga baya zan san yadda zan masa bayanin da za a rabu lafiya." A hankali Salma ta ɗaga mata kai, saida aunty ta ce mata ta je ta same sa dare na ƙara yi sannan ta miƙe, dama riga da skirt ne na atamfa a jikinta, wurin kayanta ta nufa ta ɗauko ɗan babban mayafi da ya hau da kayan ta yafa, walking slowly ta nufo ƙofa zata fita, aunty dake kallonta tana ɗan murmushi ta ce, "Haka za a je wurin saurayin ba za a ɗan gyara fuska ba." Salma ta wani ɗan yamutsa fuska har saida ta sa aunty yin dariya ta ce mata ta je, gabanta na ta ɗan faduwa ta fito haraban gidan, hango motarsa da ta yi a wurin gate ya sa bugun da ƙirjinta ke yi ƙaruwa, kamar mai jin tsoro haka ta ƙarasa bakin motar ta yi tsaye, Dr Hisham da tun da ta fito yana kallonta ta cikin motar da yake harabar akwai haske sosai, ganin ta yi tsaye ya sa shi buɗe motar ya fito, yana tafiya a nutse ya zagayo inda take, nan da nan wurin ya karaɗe da ƙamshin turaransa mai daɗin gaske, tsaf da shi kana ganinsa ka ga ɗan gayu, yana sanye da ƙananun kaya da suka amshi jikinsa, idan baka sani ba baza ka yi tunanin ma yana da aure ba, daga gefenta ya tsaya ya jingina da ƙofar gaban motan, idonsa akanta da ɗan murmushi cikin nutsattsiyar muryarsa ya ce, "Baƙuwarmu..." A hankali ta ɗaga ido ta ce masa ina yini, ya amsa mata yana ta kallon ta, bayan ɗan lokaci ya ce, "Sai kika ji saƙona a wurin aunty Kubra ko?" Kai ta ɗaga ba tare da ta kalle sa ba, hannu ya kai ya shafi sumarsa ya ɗan sauke numfashi ya ce, "Haka Allah Ke ikonSa..." ita dai bata ce komai ba kanta na ƙasa, "To ina son in ji na samu shiga ko kuwa sai dai in yi haƙuri in je na yi jinyar zuciyana." Shiru ta yi bata da niyyar yin magana, duk wani iri take ji don wannan ne kusan karo na farko da ta tsaya da namiji haka, duk da akwai samarin da ke zuwa gida da sunan sun zo wurinta suna son ta, sai dai bata ma tsayawa har su yi magana, wani lokacin ma su Imrana take saka wa su je su ce bata nan, "Salmah.." A karon farko da ta ji ya kira sunanta, a hankali ta ce, "Na'am." ya ce, "Kin yi shiru.." a sanyaye ta ce, "To ai ban san mi zan ce ba." Gyara tsayuwarsa ya yi ya ce, "Ina son ki faɗa mani miye ra'ayinki game da ni?" Shiru kamar bazata yi magana ba, da ƙyar ta ce, "Ka yi ma aunty Kubra magana duk abun da ta ce shike nan." Ɗan murmushi mai faɗi ya yi ya lura da yadda ta kasa sakin jiki da shi, amman tuna maganar da aunty Kubra ta faɗa masa na bata kula samari ya sa bai ji komai ba, "Wannan ba hurumin aunty Kubra bane da zata yanke hukunci tun da abu ne da ya shafi rayuwarki, kamar yadda na faɗa mata, zuciyata ta kamu da son ki kuma son aure nake maki, kin ga ke ce zaki yanke ma kan ki hukuncin za6ar wanda zai zamo abokin rayuwarki. Kar ki ji komai, duk abun da kika yanke game da ni zan fahimce ki." Har saida Salma ta ɗan runtse ido, ita gaba ɗaya ta rasa wace shawara zata yanke game da hakan, Dr Hisham dake ta kallonta ya fahimci kanta ya ƙulle, calmly ya ce, "Salmah.." Ta amsa masa idonta a ƙasa, ya ci gaba, "Ko kina buƙatar in baki lokaci ne ki yi shawara da zuciyar ki?" Da sauri ta ɗaga masa kai, yana murmushi ya ce, "Ok, yanzu kamar zuwa yaushe ke nan zan samu jin amsa daga gare ki?" ta ce masa zata dai yi shawaran, "Shike nan zan jira, amman pls kada a wahalar da ni, kin san jiran tsammani kan shi cuta ne." A hankali ta ɗaga ido a karon farko ta kalle shi suka haɗa idanu ta yi saurin janye idonta, "To miye labari?" ta ji ya faɗa, Hannu ta ɗan watsa ta ce babu, Dr ya ce bai yarda ba sai dai in shima labarin rowa za a masa, tana ɗan murmushi ta ce, "Da gaske babu wani labari, ni da kullum ina a cikin gida sai idan mun fita da aunty." Dr ya ce, "To ai labarin ba dole sai na nan ba, ko na can Funtua sai a bani ina so." Ɗaga ido ta yi ta sake kallonsa wannan karon bata janye idanunta ba ta ce to ai babu wani labari na can ɗin ma, Dr ya ce ya za ai ta ce ba wani labari da zata bashi game da garin su in da take yin rayuwa, shiru Salma ta yi don ita bata san wani labari zata bashi ba, "To ki bani labarin gidan ku, I mean na ƴan'uwan ki haka." Ta ji ya faɗa ta ɗago ta kalle shi, shiru ta ɗan yi kafin ta ce, "Ƴan gidanmu duk maza ne ni kaɗai ce mace." Dr ya ɗan buɗe ido ya tambaye ta da gaske ta ɗaga masa kai, tambayar su nawa ne a gidansu ya yi ta ce masa su shidda ta faɗa masa sunayen sauran ƴan'uwan nata, "Lalle ki ce ƙanwar sojoji ce ke, dole in lalla6a ki idan muka yi aure in ba haka ba in fuskanci 6acin ransu, kin san ƙanwar maza ba a taba masu ita su ƙyale fa." Ƴar dariya Salma ta yi ba kowa ya faɗo mata a rai ba sai Sageer, shi zai ci zalinta amman wani na waje da ya mata ba daidai ba sai ya fuskanci fushin sa, Dr ya ce saura ta bashi labarin ƙawayenta, ta ce "Ni ai bani da ƙawaye, kawai sai ƴan makarantar bokon mu da islamiyya, kuma abotar mu a makaranta ne sai idan wani abu ya faru muna zuwa gidan juna, amman bani da ƙawaye na daban, saboda ma ba a can na taso ba duk wanda muke tare a iya secondary school ne muka haɗu." Dr Hisham ya jinjina mata kai, sosai yake jin daɗin yadda ta ɗan saki jiki tana mashi magana yanzu, ya lura kunyar zancen sonta da ya zo da shi take yi shiyasa farko ta ƙi sake masa jiki,
Chapter 145 · 0% Book details