← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 197

Sashe 17

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Cikin washe baki Sagir ya ce, "Ai kyaun fuska dai babu ma, kuma Nuree akwai physique, he is strong, powerful and fast, in ya kama ƙwallo ba kyau, Allah dai ya haɗa mashi komai wllh, gashi yanzu shima yana cikin jerin ƴan ƙwallo masu samun kuɗi sosai, kuma ba laifi yana da alkhairi, tun da ko da ba anan yake zaune ba yana tallafa ma mutane musamman matasa ta gidauniyarsa. In sha Allahu wannan karon sai na yi yadda na yi na samu na yi magana da shi tun da na san tabbas sai ya zo nan garin, ina son ya bamu shawarwarin yadda zamu inganta harkar ƙwallon mu ya kuma taimaka mana yadda za mu ci gaba." Amsa mashi Auwalu ya yi da Allah Ya bashi iko, ya ɗaura da faɗin amman dai hakan da wuya don ya san dole ya kasance cikin tsaro sosai, ita dai innarsu murmushi kawai take in ya yi addu'a ta amsa mashi da Amin, ita kuwa Salma tuni har hirar tasu ma ta fara gundurar ta ta fara yamutsa fuska, ƙarshe ma miƙewa ta yi bayan ta gama cin tuwon ta tafi wanko hannu.

Abuja.

Mutane ne tsaitsaye cikin harabar katafaren tsadaddan hotel ɗin sun kewaye Deen bayan da suka isa, kowa ka gani fuskar sa a washe suna ta gaisawa da shi, ba wasu mutane sosai don dinner din private ce iya masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallo da manyan masu muƙamai ne za su halarta sai makusantan su kamar iyalansu da sauran su, duk wanda ka ga ya samu zuwa to yana da hanya da wani babba a harkar ƙwallo ko kuma shima wani babban ne a ƙasa. Bayan sun gama tarbar shi suna niyyar shiga cikin hotel ɗin ƙarar jiniya ta dakatar da su kowa ya kai idanun shi kan babban gate ɗin hotel din wanda daga nan ƙarar jiniyar ke fitowa, kai tsaye jerin wasu motoci na gani na faɗa gaba ɗayan su baƙaƙe ne suka shigo, wadataccen hasken wurin ya haske su sai sheƙi suke yi, motocin jami'ai ne a farko sai wasu manyan jeep guda ukku a ƙarshe wata motar jami'ain ce ta rufo masu baya, suna tsayawa jami'an suka shiga dirowa suna nufar ɗaya daga cikin jeep ɗin, yayin da wasu jami'an masu ƙirar ƙarfi suka ja layi tun daga farko har zuwa ƙarshen motocin gaba ɗaya jikinsu na sanye da kaki sun riƙe bindigu, idanun minista akan motocin tun kafin wanda aka buɗe mawa ya fito ya gane ko waye sakamakon ya san da sun kai mashi katin gayyata kasantuwar shi masoyin ƙwallon ƙafa ne sosai kuma yana yin Deen,

"It's vice-president." Minista ya faɗa tare da ɗan kallon Deen yana murmushi, kai ya jinjina mashi shima da ɗan murmushin, bayan an buɗe ma mataimakin shugaban ƙasan ya fito jikinsa sanye da baƙaƙen suit, gaba ɗaya manyan mutanen wurin har da Deen suka matsa don su tarbe shi, cike da girmamawa suka shiga gaishe da shi tare da yi mashi sannu da zuwa fuskarsa da murmushi yake amsa masu, daga baya ya maida idanunsa kan Deen bayan ya dafa kafaɗarsa ya yi mashi sannu da zuwa ƙasar tare da yabonsa, bayan gama gaishe- gaishe kai tsaye suka nufi shiga cikin hotel ɗin, jami'ai ne a gaba sai Deen da Minister da VP na a biye, daga bayan su dad ɗin Deen ne tare da wasu abokansa ƴan majalisa, daga bayan su wasu daga cikin masu ruwa da tsaki ne a harkar ƙwallo sannan su mom ɗin Deen, Leemah na jere da Fahad sauran mutane suka rufa masu baya, yayin da ƴan jarida ke ta aikin ɗaukar rahoto, wani abun burgewa tun daga in da aka tarbo Deen din har zuwa ƙopar shiga cikin hotel din red carpet ne aka shimfida suke tafiya a sama wanda hakan ke nuna Deen wani mai muhimmanci ne.

Wurin da za a yi dinner ɗin ballroom ne wato babban ɗaki kamar hall da akan yi a manyan tsadaddun hotels, saidai irin wurin ya fi tsaruwa fiye da irin hall da aka saba yin hidindimu, ɗakin an kawata shi don yin taruka na musamman, kana shiga wani irin ni'imtaccen sanyin Ac ne zai tarbe ka, tun daga kan ginin ɗakin zuwa kan yadda aka tsara shi da decoration abun kallo ne ga wanda bai saba tsintar kansa a irin wurin ba, adon da aka yi a ciki mai aji ne ba mai hayaniya ba kalar na taron waɗanda suka jiƙu da kuɗi, suna shiga sauran mutanen da ke a cikin wurin gaba ɗaya suka maido idanuwansu kan hanyar shigowar suna masu mararin ganin tauraron ɗan kwallon, lokacin da ya shigo wasu har da miƙewa fuskokinsu ɗauke da murmushin farin cikin ganin sa, nan fa aka shiga ɗaukar shi hotuna da vedio, a nutse yake ɗaga ma mutane hannu yayin da suke nufar cikin wurin, jami'an dake tsaron su na biye da su wasu daga gaban su wasu a gefe da gefe yayin da suke nufar wuri na musamman da aka ware ma manya, irin tsarin zaman cin abinci aka yi ma kujerun wurin wato tebur a tsakiya sai kujeru a zagaye da shi gaba ɗaya an lullu6e su da yadi kalar decoration din wurin, daga saman kowanne tebur an yi ado da fulawoyi masu kyau saman ɗan stand da aka yi ma adon wasu sarƙoƙi masu ƙayatarwa, wurin da aka ware ma su Deen za su zauna na daga gaba. A can babban gate ɗin shigowa hotel din jami'ai ne sun kasa sun tsare suna bincike mutanen dake shigowa cikin hotel ɗin, koda baka daga cikin waɗanda za a gudanar da dinner din sai an bincika ka, a bakin kopar shiga ɗakin da za a yi taron nan ma wasu samudawan jami'ai ne jikinsu da hannuwansu ɗauke da manyan makamai yayin da rabin fuskarsu ke a rufe iya idanuwansu ne ake iya gani wanda ko haɗa ido da su ka yi sai ka shiga taitayinka, duk wanda zai shiga wurin sai an bincike shi tun daga sama har ƙasa saboda tsaro.

Ba tare da 6ata lokaci ba bayan dinner guests ɗin kowa ya zauna an natsu mai girma ministan wasanni ya fara jawabi bayan ya miƙe an bashi lasifika, cikin harshen turanci ya fara bayanin dalilin taruwar su,"Ladies and gentlemen, distinguished guests, it is our pleasure to welcome home our very own football superstar, DEEN JR.!" Ya ƙare maganar tare da dafa kafaɗar Deen hakan ya sa shi miƙewa tsaye fuskarsa cike da annuri, gaba ɗaya ɗakin ya ɗauka da ƙarar tafin mutane. Ministan ya ci gaba da cewa, "Your achievements on the pitch have brought joy and pride to our nation. Tonight we gather to celebrate your success and express our gratitude for being an inspiration to our youth." Ya ƙare maganar idon shi akan Deen yana yi mashi murmushi.
Chapter 17 · 0% Book details