← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 197

Sashe 104

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

itama ta ci abincin tana murmushi ta ce duk sun ci tun kafin ya zo, ba wani mai yawa ya ci ba Zarah na roƙonsa ya ƙara ya ce mata shima ya riga ya ci abinci ne kafin ya zo. Cikin falon suka dawo aunty Murja na murmushi ta ce har ya gama Zarah ta ce ai ba wani da yawa ma ya ci ba, zama suka yi Deen ya ce ya hana su kwanta ya yi zuwan dare, Dr na murmushi ya ce kada ya damu dama wani lokacin suna kai wa dare haka musamman idan kowa na da aikin da zai yi a daren, shiru na ƴan wasu daƙiƙu ne ya biyo baya kafin Deen ya kalli su Zarah ya ce masu kowa ya faɗa mashi abun da yake so, ɗan zaro ido suka yi tare da kallon juna suna ɗan murmushi, ya ce Zarah ta fara faɗa tun da ita ce babba, ɗan motsa baki ta shiga yi tana murmushi ta kasa magana, sai bin mutanen cikin falon take da kallo da suma duk idanunsu na akanta kowa yana jira ya ji mi zata ce, sam ta kasa magana Deen da ke kallonta da murmushi ya ce ko glasses za a ƙaro mata, ɗan tura baki ta yi a shagwabe ta ce, "Kai yaya Deen wai mi glass ɗina ya yi maka, ni fa ina gani kawai da dare ne vision na ke raguwa, sai idan zan duba paper especially white paper." Yana ɗan murmushi ya ce ashe dai makauniyan ce ita, a shagwabe ta ce ita wllh ba makauniya ba ce sai dai ko fiancee ɗin shi ce makauniya idan glasses ɗin ya yi masa ne sai ta bashi ya kai mata, iyayen su na ta ƴar dariya, shi Dr har da mamaki ya ke don bai zata Deen ɗin na iya yin wasa haka ba, ce mata ya yi yana jin ta ta faɗa mashi duk abun da take so ai shi ne ya tambaya, ƴan kifce kifcen idanu ta shiga yi tana satar kallon mom da dad ɗin su, da ƙyar ta ce mashi mota take so da zata rinƙa zuwa school, "Zarah! Wani irin mota kuma, ina bani ce ke tafiya da ku ba gaba ɗaya." Aunty Murja ta tari hanzarinta da faɗin hakan, ɗan yamutsa fuska Zarah ta yi ta ce, "Amman mummy wasu lokuttan ai bamu samun tafiya tare idan muna da bambancin lokacin lectures, kina riga na tafiya sai dai in je daga baya ko kuma ni na riga ki tafiya." Tana mata wani kallo mai kaman harara ta ce, "Wani time en ba daddyn ku na kai ku ba, ko kuma idan ba taren zamu tafi ba in saka Shuaibu ya kai ku, duk miye na wani a siya maki mota kuma?" A marairaice ta ce to amman wani lokacin ba sai dai ta hau abun hawa ba, kallon Deen aunty Murja ta yi ta ce, "Son ka rabu da ita ba wani motan da za a siya mata." Shi dai murmushi kawai yake, tambayar Zarah ya sake yi sai mi take so? A sanyaye ta ce ba komai motan ma a bari tun da mummy bata so, dariya Nabeela ta fara yi tana sunne kai lokacin da itama ya tambaye ta abun da take so, tsoron ta ta faɗa itama mummy ta taka mata burki, jin Deen ya ce sai ta faɗa masa abun da take so ta yi ƙarfin halin ce mashi waya iphone take so, aikuwa itama mummy ta daka mata tsawa ta ce, "Shi wayan naki da ya yi mi? ina ce samsung gare ki kuma waya ce mai kyau, ku wai mi yasa baku da tunani da lissafi ne, gaba ɗayan ku unnecessary abubuwa ne kuke faɗa, ce maku akai bashi da abun da zai yi da kuɗi ne ko kuwa injin buga kuɗi ne da shi, wahala yake yi kafin ya samu shima." Juyawa ta yi kan Deen ta ce, "Don't mind them son, ka rabu da su ba wani mai wani kwakkwaran buƙata." Yana murmushi calmly ya ce mata, "Aunty, wannan tsakanin ƴan'uwa ne, would you mind giving us some space?" Ɗan wara ido aunty ta yi jin abun da ya ce Dr ya saka dariya, jinjina kai aunty ta yi ta ce ta ji ɗin amman duk da haka bazata fita a maganan ba ta san duk unserious buƙatu za su faɗa, tambayar Nabeela ya yi sai mi take so tana murmushi ta ce mashi shike nan, ana zuwa kan Nabeel gaba ɗaya suka ga ya juya ta yadda ya ba mummy ɗin su baya yadda kar ma ya kalle ta ta hana shi faɗin buƙatar sa, sun fahimci mi hakan da ya yi ke nufi duk suka yi dariya, aunty Murja ta ce ya yi ya gama in dai ba wani abun kirki bane shima ba bari zata yi ba, abu na farko da ya ce yana so shine ya canza masa PS ɗin sa da ya lalace kuma an gyara amman yana ta bashi matsala Deen ya ce ok, ya ƙara tambayar sa sai mi, ya ce sai mashin mai caji, cikin ɗaga murya mummy ta ce, "Shi mashin ɗin naka da ya yi mi za a canza maka, ku ji fa don Allah! in ba son a yi almubazzaranci ba ga mashin naka lafiyan sa lau ka ce wai kana son a siya maka wani." Juyawa ya yi ya kalle ta a shagwabe ya ce, "Mummy to ai ba iri ɗaya bane ko wannan mai caji ne nike so." Tana hararansa ta ce, "Ina mai cajin da mara cajin duk buƙata ɗaya suke yi?" Tura baki ya yi ya ce to amman dai ai shi ne na yayi wanccan roba roban yanzu duk an daina ya yin shi." A ɗan harzuƙe ta ce, "Yayin banza, kuma ƙarya kake har yanzu an fi amfani da shi irin nakan, idan don ya yi ne shima electric ɗin yayin nasa zai wuce ne." A shagwabe yake faɗin shi dai shi yake so kuma duk friends ɗin sa yanzu duk irin shi gare su sai shi zata hana a siya mashi ba yaya Deen ɗin ne ya ce su faɗi komi suke so ba, shi dai Deen murmushi kawai yake, sai dai sun burge shi ta wani 6angaren yadda komai suka saka hankali a ciki, a wurin shi ba su faɗi wasu buƙatu da suka wuce kima ba amman duk da haka mummynsu sai da ta tsawatar masu, ba kamar yadda ta kasance a gidan su mom ɗin shi ba, wayar sa ya ɗauka ya fara daddanawa bada jimawa ba ya ɗago ya kalli aunty da murmushi ya ce mata ga saƙo nan ya tura a account ɗinta nasu ne ita da Dr, kallon Zarah ya yi ya ce mata za a kawo masu saƙon su zuwa gobe, ta ɗaga masa kai tana murmushi haka ma su Nabeela duk farin ciki ne akan fuskokin su, lokacin da aunty ta duba kuɗin da ya tura ɗagowa ta yi ta kalli Deen ta ɗan waro idanu ganin suna da yawa, da sauri ta ce, "No son, kuɗin nan sun yi yawa gaskiya, su ma kuma kada ka biye masu pls, hidindimun da yawa ai ba su kaɗai bane." Ya ce mata ba wani abu ai dama saboda su yake neman kuɗin kuma basu kaɗai ne ya yi mawa ba kada ta damu, ƙarshe sai dai suka yi masa godiya da addu'oi, daga haka ya yi masu sallama zai tafi, har aunty na ce mashi ya tsaya nan mana kawai ya kwana ya nuna mata akwai abubuwan da zai yi don gobe zai wuce Abuja. Gaba ɗayan su suka rako shi waje yana riƙe da hannun Nabeel da ya kasa rufe bakin sa saboda farin ciki, a bakin mota suka tsaya suna ƙara yin bankwana da shi aunty Murja na faɗin sai kuma Allah Ya sake ƙaddara saduwar su, su Zarah duk suka yi masa godiya, bayan ya shiga cikin mota ya kira Zarah ta je bakin motar tare da ɗan rankwafawa suna yin magana, bayan ɗan lokaci ta ɗago tana murmushi tare da ɗaga masa hannu tana masa bye bye, suna ta ɗaga masa hannu har aka ja motar suka tafi, daidai bakin gate suka ga motar ta tsaya da sauri mai gadin da ya buɗe gate ya nufi bayan mota in da Deen ya ke gilashin ya ɗan sauka, magana suka ɗan yi kafin maigadin ya ɗan ja baya, da alama godiya yake yi har yana ɗan rankwafawa, bayan gilashin ya ɗaga sama aka ja motar mai gadin na ta ɗaga masu hannu har suka fuce....
Chapter 104 · 0% Book details