Sashe 165
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Da sauri Salma ta sauke idanunta, ruɗewa ta yi a cikin ranta ta shiga kokonton anya shi ya faɗi abun da ta ji, ko dai kunnuwanta ne suka ji ba daidai ba.., "Kin yi shiru..." Ta ji saukar muryarsa, a hankali ta ɗaga ido ta ga kallonta yake, a ɗan dabarbarce ta ce, "Ba...ban gane abun da kake nufi ba." Gyara kwanciyar shi ya ɗan yi fuskarsa a sake ya ce mata abun da ta ji shi yake nufi, sauke idonta ta yi, ta kasa yarda idan yadda ta fahimci maganar hakan yake nufi, gently ya ce, "Idan nima ban yi maki ba, just tell me I will understand." Motsa baki ta shiga yi ta haɗiyi wani miyau, a hankali ta girgiza masa kai, ya ce mi hakan ke nufi, da ƙyar tana jin kamar zata nutse a wurin ta ce, "A'a..ka yi mani idan da gaske kake." Ɗan murmushi ya yi ya ce idan ba da gaske yake ba why zai yi mata irin maganan, shiru suka ɗan yi kafin ta ji ya ce it seems like she's not ready su yi maganan yanzu bari ya barta sai wani lokacin idan ta shirya, gabanta ne ya ɗan fadi zuciyarta ta kwa6e ta kan bari ta yi ma kanta ya yi tunanin ko bata son shi shike nan ya ki ƙara yi mata maganar, da ɗan sauri ta ce, "A'a ya Deen, kawai dai...ina jin kunya ne." Shiru ya yi still da ɗan murmushi akan fuskarsa, bai yi tunanin zai nuna yana son mace ta nuna masa kunya haka, duk da ita ce mace ta farko da ya fara furta ma magana irin wannan, sai dai shi mata su ce suna son shi, amman duk da haka kunyarta na burge shi, sigh yay ya ce, " I want you to tell me the truth Salmerh, do you love me?" Salma ta ɗan runtse ido ta jinjina masa kai alamar eh, calmly ya ce, "Taya zan yarda kin kasa ko kallo na." Shiru bata ce komai ba kuma bata ɗago kai ba, ya yi kasa da murya ya ce, "Idan kina son in yarda da gaske kina so na...look me in the eyes and say it." Zuciyarta ce ta shiga tunzura ta kan ta yi yadda ya ce kar ta yi ma kanta, da ƙyar ta ɗago kai ta kalli screen ɗin wayan suka haɗa ido da shi, motsa baki ta fara yi tana kikkafta ido, sam ta kasa faɗa masa hakan yayin da take kallon shi, kawai sai ta rufe idanunta muryarta na ɗan rawa ta ce, "I..love you..." Jin ya yi shiru bayan ta faɗi haka gabanta ya ɗan fadi, ta yi tunanin ko ma ya katse kiran tun da bata yi yadda ya ce ba, a hankali ta ɗan buɗe idanunta don ta tabbatar ko hakan ne, haɗa ido suka yi da shi yana ta kallonta, yadda ta runtse idanu ta faɗa masa hakan ba ƙaramin kyau ya ga ta yi masa ba shiyasa yake ta kallonta, ganin kallon da yake mata sai ta yi tunanin ko bai ji daɗi ba da bata yi yadda ya ce ɗin ba, sai da ta tattaro dukkan ƙarfin gwiwarta tana kallon cikin idanun shi a sanyaye ta ce, "I love you ya Deen." Wani kallan murmushi ta ga ya yi kawai ta yi saurin saka hannunta guda ta rufe fuskarta, daga haka ya ce, "Sarkin kunya, bari in bar ki ki yi bacci we will talk later." Ta ɗan ɗaga kai, ya sake cewa, "Make sure you get some sleep, I love u too." A hankali ta ɗan ɗago kai ta kalle shi ya sakar mata wani kallo da sai da duk jikinta ya amsa, daga haka ya yanke kiran, Salma ta kafe screen din wayan da kallo ta ɗan waro ido, ganin abun take kaman ba a gaske ya faru ba, ko dai mafarki take yi? hakan ta raya a zuciyarta, ƙoƙarin gasgata anya ba mafarkin take yi ba ta shiga yi, tunanin tun farkon lokacin da ta kwanta bacci zuwa yanzu ta shiga yi, hannunta ta ɗago ta kai shi gefen fuskarta ta ɗan mammari kanta a hankali, yadda wai in ma mafarkin ne ko zata farka, ganin tana nan dai yadda take ta sake kai hannu ta tsunkuli jikinta ta ji zafin ya ratsa ta, zuciyarta ta shiga tabbatar mata da duk abun da ya faru tsakaninta da Deen da gaske ne ba mafarki ba, faɗawa tayi kan gadon ta kwanta tana sakin faffaɗan murmushin farin ciki, wai ita ya Deen ke so she couldn't believe it! Wayarta ta ɗauka ta shiga Social media tana kallon hotunansa da videos dake ta yawo, wani farin ciki ne ya mamaye mata zuciya, duk da haka ta kasa yarda wai shi ne ke son ta, bayan ta gama kalle kallen hotunan ta ajiye wayan gabanta ta lumshe ido, zuciyarta ta shiga dawo mata da abun da ya wakana a tsakanin su, tana ta faman sakin murmushi a haka har bacci ya yi awon gaba da ita. Saboda rashin baccin da Salma bata yi ba da wuri, sai wuraren ƙarfe takwas saura ta farka, da sauri ta sauka daga kan gado ta nufi banɗaki ta yo alwala, bayan ta gama yin sallan zaune ta yi a wurin ta ɗaura kanta a gefen gado mafarkan Deen da ta yi na dawo mata, sai sakin murmushi take yi, da sauri ta juya jin an buɗe ƙofar ɗakin, aunty Kubra ce ta shigo tana sanye da rigar bacci da ta tsaya mata iya gwiwa kanta ta saka hula, cikin ɗakin ta shigo idanunta akan Salma da ta juya tana kallon ta itama fuskarta da murmushi, "Baby ba dai sai yanzu kika yi salla ba?" Salma ta ce, "Aunty makara na yi, ban daɗe dana tashi ba." Aunty ta gyaɗa kai ta ce, "Ai ban san baki tashi ba da asuba da na zo na tada ki. Halan social media kika shiga kallon abubuwan world cup shiyasa kika makara." Salma ta ɗaga mata kai kawai tana murmushi don bata san ta yadda zata sanar mata abun da ya faru tsakanin ta da Deen ba, juyawa aunty ta yi tana faɗin bari ta je ta haɗa masu breakfast dama ta ga bata fito bane shine ta shigo ta ga ko lafiya, Salma ta ce mata ta bari gata nan fitowa yanzu ta haɗa breakfast ɗin, aunty da ke niyyar fita ta ce ta yi zamanta kawai, bayan fitar aunty ci gaba da tunane-tunanenta ta yi, sai bayan wani lokaci sannan ta miƙe ta cire hijab ɗin da ta yi sallan ta ninke, fita ta yi daga ɗakin ta nufi kitchen. Bayan sun zauna yin breakfast, lokaci lokaci aunty ke kallon Salma da kana kallonta zaka ga alamun farin ciki akan fuskarta, wani lokaci har dakatawa take da cin abincin tana ɗan murmushi, bayan sun yi nisa cikin yin breakfast din, aunty ta dakata tana kallon Salma ta ce, "Baby ya aka yi ne, na ga alamun yau kina cikin farinciki." Salma ta kalle ta tare da sakin faffaɗan murmushi, itama aunty ta yi murmushi ta ce, "Mi ya faru?" Salma ta kasa magana sai murmushi kawai, aunty ta sake cewa, "Bani in sha mana babyna, Allah Ya sa alkhairi ne." Salma ta shiga motsa baki ganin yadda aunty ta kafe ta da ido tana murmushi, cikin jin kunya ta ce, "Dama jiya da daddare ne muka yi vedio call da ya Deen, shine...ya ce...wai yana sona." Ta ƙarasa tana sunne kai, aunty ta yi shiru a cikin ranta ta shiga tunanin waye Deen ɗin, tunanin mai suna Deen da ta sani ta shiga yi, wani Zaharadeen da suke matsayin cousin da ke a Katsina ya faɗo mata a rai, ta ce "Wane Deen? Ko Zaharadden ɗin aunty umma?" Salma ta girgiza mata kai alamar a'a, aunty ta ce wani ne a can Funtua? Salma nata murmushi ta ce, "Yaya Deen fa ɗan kwallo nike nufi." Aunty ta bita da wani kallo ta ɗan saki baki, da alamun mamaki aunty ta ce shi ɗin ne ya ce yana son ta, Salma ta ɗaga mata kai, aunty ta ce, "Amma dai mafarki kika yi ko?" Salma bata san lokacin data kyalkyace da dariya ba,