← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 183 OF 197

Sashe 183

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta sanar masa zancen, ya ce mata wannan ba maganar waya bace gashi nan dawowa gidan yanzu. Tun bayan da Deen ya gama yin waya da mom ɗin sa yake zaune ya yi shiru yana kallon wuri ɗaya, kausasan kalamanta ne ke ta masa yawo a kai, dama ba wai yana tunanin zata goyi bayan tsakanin shi da Salma bane, amma duk da haka kalaman da ta yi sun tsaya mashi, wayarsa da ke ajiye gefe ya kai hannu ya ta6a yana duba lokaci, da ya bari sai gobe zai yi ma hajiya maganar da ta kawo shi garin amman yanzu yana jin zai canza ra'ayi ya je ya yi mata magana yanzu tun da ya ga dare bai yi ba sosai, sauka ya yi daga saman gadon ya nufi ƙofa walking slowly, kana ganinsa ka san jikin sa a sanyaye yake, yana zuwa corridor zai nufi ɗakin hajiya ya hango ta zaune a falo, falon ya nufo hajiya da ke zaune saman kujera, da plate ɗin yankakkan kankana a gefenta tana sha ta ɗago kai tana kallon shi, a kujerar gefenta ya zauna fuskarta da ɗan murmushi, "Ai na ɗauka ka yi bacci." Hajiya ta faɗa idonta akan sa, ya ɗan girgiza mata kai alamar a'a, tayin kankanan ta yi masa nan ma kai ya girgiza masa alamar ba zai sha ba, shiru suka ɗan yi hajiya ta maida idonta kan tv, can ta juyo ta kalle shi, ganin kaman akwai alamun wani abu a tattare da fuskarsa ta ce, "Ya aka yi ne?" Sauke idonsa ya ɗan yi, kafin ya ɗago a nutse ya ce, "Ina son zamu yi magana ne." Hajiya ta ɗaga masa kai tare da tattara duk attention ɗinta kan shi, calmly ya shiga yi mata bayani ta natsu tana sauraran sa har ya gama, ɗan murmushi ne ya bayyana akan fuskar hajiya, ta hau ɗan jinjina kai tare da ɗauke idonta daga kansa bayan ta gama sauraran maganar da ya zo da ita, duk da ta san Salma tana yi masa aiki amman ta ɗan yi mamakin yadda har soyayya ta ƙullu a tsakanin su, sai dai ta san hakan ba komai bane a wurin ubangiji, ƴar gajeruwar ajiyar zuciya hajiya ta sauke ta kalle shi ta ce, "To amman ita fa waccan da batun aure ke tsakanin ku?" Deen ya ɗago fararen idanunsa ya kalle ta a hankali ya ce, "Zan aure su tare." Ta ɗan jinjina kai, murmushinta ya ɗan fadaɗa ta ce, "Ka ce zaka kafa tarihi a family, don ba wanda ya ta6a auren mata biyu lokaci ɗaya." Shi dai ya yi shiru tare da sauke idanunsa, jimm hajiya ta ɗan yi sai kuma ta ce, "Yanzu ita Salma kun gama daidaitawa da ita ke nan ?" Ya ɗaga mata kai, "To iyayenta sun san da maganar tsakanin ku?" Ya ce mata auntynta ce ta sani wadda take wurinta yanzu a Kaduna, hajiya ta jinjina kai ta ce ta san tana Kaduna, sauke numfashi ta yi ta ce, "In dai ta yi maka kana son auren nata kuma kun fahimci juna, to mu namu fatan alkhairi ne in dai an yi bincike ba wata matsala, duk da na san Salma tana da halaye nagari, kuma iyayenta ga dukkan alamu mutanen kirki ne. Yanzu zan yi ma babanka na nan magana kan zuwa nema maka auren, kaman yaushe ka shirya kake son a saka auren naku?" Deen ya ce mata zai koma London ya ƙarasa wasu abubuwa, nan da 2 months zai dawo lokacin yake son a ɗaura masu aure, hajiya ta ɗaga kai alamar fahimta idanunta na kallon wuri daban, bayan ɗan lokaci ta juya ta ce, "Amman to su iyayenka sun san da maganar neman auren naka?" Shiru Deen ya ɗan yi kafin ya ce mata bai yi magana da dad ɗinsa kan hakan ba amman mom ɗinsa ta sani, hajiya dake kallon sa ta ce to ita mom ɗin nashi ta amince ma auren nasu, yanayin fuskarsa ne ta ga ya ɗan canza, ya ɗan yi shiru muryar mom ɗinsa ta shiga yi masa amsa kuwwa a cikin kai yayin da take faɗin kausasan kalamai akan auren sa da Salma, "....._Deen! rainin da ka yi mani har ya kai haka...ni kake faɗa ma kana son wata kuma auren ta zaka yi...bacin ka san da maganar aure tsakanin ka da Basma....ba ka isa ka haɗa Basma da wata ba wllh, idan ma mafarki kake to ka farka...wato kai ka isa ka kai tun da kana da kuɗi ko, don haka kake tunanin duk abun da ka ga dama zaka yi, to komai kuɗin ka da isarka dole ne ka bi maganar mu tun da mune muka yi silar zuwan ka duniya, ka bari idan kai ne ka haiho kanka sai ka yi duk abun da ka ga dama, amman yanzu mune iyayenka masu iko akan ka, don haka ban amince da wai kana soyayya da wata zaka aure ta ba, already ka san da kana da wadda zaka aura don haka tun da wuri ka datse duk wata alaƙa da ke tsakaninka da wannan yarinyar, kuma ina umurtar ka da ka cire hoton ta da ka ɗaura yanzun nan_!" Lumshe ido Deen ya yi tare da sauke 6oyayyan ajiyar zuciya, hajiya da ke ta kallon shi ta ce, "Ka yi shiru Deeni." Kallon ta ya yi fuskarsa ta nuna alamun damuwa ya ce, "Bata amince ba." Hajiya ta yi ɗan murmushi na dattako, duk da ana saka ma mutum ran shiryuwa daga hali mara kyau da yake yi, dama bata yi tunanin Jameela zata amince masa game da auren ba, kallon shi ta yi ganin damuwa akan fuskarsa ta ce, "Dama ba lalle ta amince maka ba, duba da matsayin waccan, ita ɗin ɗiya ce a wurinta." Deen dake kallon ta fuskarsa a ɗan yamutse ya ce, "But I told her that I would marry both of them." Hajiya da ke murmushi ta ce, "Ai hakan ba zai saka ta amince maka ba sai ma ta ji zafin hukuncin naka, mu mata ba iya kan mu muke ma kishin abu ba, namu ma muna tayawa kishi." Deen ya yi jimm sai kuma muryarsa da yanayin amo na karyewar zuciya ya ce, "Amman yakamata ta goya mani baya akan abun da nike so, bani na zabi Basma a matsayin wadda zan aura ba, hakan zabinta ne kuma na amince don in faranta mata rai, why yanzu nima bazata mani hakan ba kan abun da raina ke so don ta faranta mani." Yana ƙarasa maganar ya sauke idanunsa, hajiya ta yi shiru tana ta kallon shi jin ya faɗi abun da sam ita bata san haka abun yake ba, duk ɗaukar ta soyayya ce ta shiga tsakanin su har ta kai ga maganar aure, gashi yanzu daga yanayin yadda ya yi maganar ta so ta fahimci kamar ma baya son Basman kawai dai ya amince ma auren ta don biyayya, tirƙashi! Wane irin halin son kai Jameela gare ta da har yaranta na cikinta bata ƙyale ba, a cikin rai hajiya take jin lallai zata yaƙi son kan Jameela wurin goya ma Deen baya kan abun da ransa ke so...nannauyar ajiyar zuciya ta sauke idonta akan Deen da har lokacin kansa na a ƙasa, cikin kwantar da murya ta ce, "Kada ka damu Deeni, idan Salma matarka ce ba wanda ya isa ya hana hakan kasancewa, kuma kana da goyon bayana matuƙar an tabbatar da ba wata matsala a auran ka da ita, amma duk da haka ina so ka yi ƙoƙari wurin shawo kan mahaifiyarka ta amince maka ko don samun albarkar al'amarin." A hankali ya ɗago kai ya kalle ta tare da ɗan jinjina kai, "Shi mahaifin naka ka bari zan yi magana da shi a daren nan ma." Deen ya ɗaga mata kai, ganin still da damuwa akan fuskarsa, cikin wasa a ƙoƙarin ganin ta kawar masa da damuwan ta ce, "Ka kwantar da hankalinka angon Salma, wai ni anya ma ba daɗin awara bane ya kwashe ka har ka fara son ta, ƙarshe ka yanke shawarar auren ta yadda zata rinƙa maka awaran duk lokacin da ka so ko?" Ƴar dariya ya yi har fararen haƙoransa suka ɗan bayyana, hajiya ta ji daɗin ganin dariyar da ya yi, sai kuma ta ce, "In ba ma don ka shanye ni ba, ta ya zaka zo mani da maganar yi mani kishiya ni kuma har da goya maka baya, ƙarshe ta zo ta ƙwace mani kai." Still da ƴar dariya akan fuskarsa ya ce mata saboda tana son shi ne ya sa ta goya masa baya, kuma kada ta damu ita matar shi ce ta ƙarfe ba za a raba su ba, hajiya dake ƴar dariya ta ce da daɗin awara ya kwashe shi zai watsar da ita, jingina ya yi da kujera yana faffaɗan murmushi ya ce mata da ya je Kaduna wurinta ma ta yi mashi awaraan mai daɗi, hajiya ta ɗan zaro ido ta ce ai kuma shike nan an riga ma an ƙwace mata shi ashe har Kaduna ya je, daga yadda yanayin sa ya nuna da suna maganar Salma hajiya ta fahimci yana son ta sosai don gashi damuwar da ta bayyana akan fuskarsa har ta washe, har cikin ranta ta ji itama tana son ya auri Salma don tabbas akwai abubuwan da in ba a tare da Salma ba ba lalle ya samu a wurin Basma ba duba da irin rayuwar da ta taso a cikinta. A cikin daren kan ka ce mi labarin soyayyar Deen da Salma ya karaɗe shafukan sada zumunta, tuni abokan Sageer sun yaɗa har da yadda alaƙar ta su ta samu asali daga aiki da take masa, wasu ma ƴan nan f Funtua musamman ƴan unguwarsu da suka san ta har da sana'ar awaran da take suka bayyana, nan fa al'umma suka shiga tofa albarkacin bakin su, yawanci duk yabon Deen suke kan yadda ya iya yin soyayya da Salma ana faɗin ba lalle a samu mutumin da ya shahara kamar sa ba da zai iya yin hakan, ana ta kuma yabon kyawun Salma da yake har da wasu hotunanta abokan Sageer suka watsa, Allah dai ya taimaka ba a samu wanda ya ɗaura hoton ta a wurin
Chapter 183 · 0% Book details