Sashe 197
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
mata da za a sake shi a daren nan, suna gama yin magana da shi ta shiga kiran daddy Sa'ad. Mom Jameela zaune a haɗaɗɗan falonta na sabon gidansu, hannunta ɗaya riƙe da glass cup mai ɗauke da ruwan lemu, cike da isa take sipping lemun, ta haɗe rai yayin da take latsa wayarta da hannunta ɗaya tana kallon video ɗinta da aka watsa, sai dai sam bata wani ji ta damu da hakan ba, don a yadda take ji ta shirya ma komai zai faru in dai akan Deen ya auri mai awaran nan, wayarta ce ta fara yin ringing, ta wani yatsina fuska ganin dad ne ke kira, sai da ya yi mata kira kusan ukku ba tare da ta yi picking ba, ƙarar shigowar saƙo ta ji ta kai hannu ta buɗe, dad ɗin ne ya turo mata saƙo da kausasan kalamai kan idan bata ɗauki wayan ba sai ya yi mummunan 6ata mata rai, bayan ɗan lokaci ya sake kiranta, tana cika tana batsewa ta ɗaga kiran, on the other hand a fusace dad ya ce, "What do you think you have done Jameela! Da izinin wa ma kika zo nan! Kuma akan mi zaki saka a kama masu yaro, a tunanin ki zaki je masu har gida ki ci masu mutunci su zuba maki ido? Kin san hakan da kika aikata zubar mana da mutunci ne..kin san kuma mi hakan zai haifar mani!? Ta wani sauke ƙafarta ƙasa a hasale ta ce, "I don't fucking care komai hakan zai haifar Ibraheem! magana ake ta muradina akan ɗana da na haifa, don haka sai in da ƙarfina ya ƙare wllh, ba wanda ya isa ya nuna mani iko akan ɗan da na ɗauki cikin sa na yi naƙudar sa har na kawo shi duniya, na san ai nufin ka hakan zai sa kasa mu matsala a siyasar ka ko, to a wannan ga6ar ban damu ba ko da zaka rasa kowane muƙami ne in dai akan cikar burina ne kan ɗana!" dad ya yi ƙwafa da ƙarfi ya furta, "To mu zuba mu gani, kuma ina mai umurtar ki da ki saka a saki yaron nan yanzun nan, idan ba haka ba zaki ga mummunan matakin da zan ɗauka akan ki, wanda ina mai tabbatar maki da sai kin yi da na sanin komai da kika aikata!" Daga haka ya yanke kiran, mom ta cire wayan tare da bin screen ɗin da kallo ta wani tamke fuska, ji take ai idan ma ta saka aka saki Sageer yanzu ya sha da ita, sannan hakan tamkar buɗe ma wasu ƙofar raina ta ne, sai dai kuma a wani 6angare na zuciyarta ta ɗan ji fargabar maganar dad ta ƙarshe ta kama ta....
A Cikin Rayuwa kashi na 2 ₦500 Regular WhatsApp Group, ₦800 Special Telegram Group. Za a biya ta Sterling Bank (0121797114, Zainab Bature). A tura shaidar biya ta WhatsApp: 08169856268, 09013804524, ko Telegram: 08032811442. Saƙo kawai ban da kira please.*
Labarin na tafe da sabon salo mai matuƙar ban mamaki, kada ku bari a ba ku labari🔥
A Cikin Rayuwa kashi na 2 ₦500 Regular WhatsApp Group, ₦800 Special Telegram Group. Za a biya ta Sterling Bank (0121797114, Zainab Bature). A tura shaidar biya ta WhatsApp: 08169856268, 09013804524, ko Telegram: 08032811442. Saƙo kawai ban da kira please.*
Labarin na tafe da sabon salo mai matuƙar ban mamaki, kada ku bari a ba ku labari🔥