← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 186 OF 197

Sashe 186

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk abun da ke faruwa su Sapna ba su sani ba saboda suna a halin tafiya, washe gari da rana Basma ta tashi daga baccin gajiyan tafiya ta yi wanka, bayan ta gama shiryawa cikin ƙananun kaya ta zauna tana latsa wayarta, a lokacin ne ta yi arba da zancen soyayyar Deen da Salma, tashin hankali sosai ya bayyana a fuskarta, jiki na rawa ta sauka daga saman gadonta ta nufi ƙofar fita, part ɗin Sapna na nan saman bene ta nufa, bata iske ta a falo ba kai tsaye ta wuce bedroom ɗinta, tana shiga ta ganta a kwance saman lafiyayyan gadonta tana bacci, nufar ta Basma ta yi ta rankwafa murya na rawa ta shiga kiran sunanta tana ɗan bubbuga shoulder ɗinta, a hankali Sapna ta buɗe idanuwanta masu ɗauke da bacci ta bita da ido, ganin yanayin fuskarta cikin muryar bacci ta ce, "Baby, what happened?" Kamar jira Basma ke yi ta tambaye ta kawai ta fashe mata da kuka, Sapna ta ɗan wara ido kafin da sauri ta fara yunƙurin tashi zaune, kamo Basma ta yi ta zaunar da ita tare da manna ta jikinta, da alamun tashin hankali ta ce mi yake faruwa ne ta sanar mata, hannu na rawa ta miƙa mata wayarta, Sapna ta kafe screen ɗin wayan da kallo with a little shock, can ta ɗago ta kalli Basma da ke ta kuka a hankali, kan Sapna ne ya ɗaure ta shiga tunanin da gaske ne Deen na soyayya da yarinyar kuma auren ta zai yi kamar yadda ta gani, to mi hakan ke nufi bacin ya san da maganar aure tsakanin shi da Basma? Kamar Basma ta san mi yake yawo a ran mom ɗin nata, tana kallonta cikin kuka ta ce shike nan hakan na nufin ya Deen ya fasa auren ta, ko dai dad ɗinta ne ya ce mashi ba zai aura masa ita ba shine ya samu wata, wannan maganar tata ta ja hankalin Sapna ta fara tunanin ko da sa hannun Maleek a faruwar hakan, rarrashin Basma ta yi ta ce ba lalle idan labarin gaskiya ne, amman bari ta je wurin dad ɗin nata ta ji idan ya san da hakan, ta sauko daga saman gadon itama tana sanye da ƙananun kaya da suka amshi jikinta sosai...kai tsaye 6angaren Maleek dake a nan sama ta nufa, tana shiga ta iske shi zaune a falo yana operating laptop dake a saman table ɗin gaban shi, ya ɗago kai yana kallon ta with a smile yayin da ta nufe shi, daga gefen shi ta zauna ya maida idonsa kan screen yana faɗin, "Har yanzu gajiyan hanyan ce bai sake ki ba, na shiga ai bada jimawa ba na iske kina ta bacci." Ta ɗan yi murmushin da iyakar sa lips ɗinta, jin ta yi shiru ya juyo ya kalle ta suka haɗa ido, cikin nuna kulawa ya ce, "Ya aka yi ne?" ta ɗan gyara zama kafin ta ce, "Ka ga abun da ke trending a social media?" Ya ɗan yi shiru yana mata kallon rashin fahimta, ya ce "Kan mi kike magana?" Wayar Basma da ta taho da ita ta miƙa masa, bin wayar ya yi da kallo kafin ta ga ya yi ɗan murmushi a nutse ya ce, "Na gani tun ɗazu." Sapna da ta kafe shi da ido ta ce, "So...is it true?" Maleek ya miƙo mata wayar yana faɗin, "Ku san hakan, don na ga posting ɗin da Deen ya yi na picture ɗin yarinyar before ya cire." Ya ƙare maganar yana ci gaba da latsa system ɗin gaban shi, fuska a jagule Sapna ta ce, "Amman ta ya zai yi hakan, ya san da maganar aure tsakanin shi da baby...ko kai ne ka goya masa baya?" Ɗan faffaɗan murmushi Maleek ya yi ba tare da ya kalle ta ba ya ce, "Sai na goya masa baya, kuma don akwai maganar aure tsakanin shi da ita shine ya zama bai da right ɗin son wata mace?" Sapna ta yamutsa fuska ta ce, "Amman itama gashi wai auren ta zai yi." Maleek ya ɗan ta6e baki ya ce, "In ma hakan ne a ganina ai ba laifi bane, ko kin manta mata nawa addini ya yardar masa ya aura." Sapna ta yi shiru tana kallon sa duk ranta ba daɗi, don gani take kamar Maleek ya 6oye mata ne amman da sa hannun shi a lamarin, bayan ɗan lokaci Maleek na ci gaba da latsa laptop ya ce, "Ni I'm very happy for him in dai auren yarinyar zai yi, dama haka yakamata ya samu wata nutsattsiya ya aura...tun da ita ta zabi lalata rayuwarta." Kana ganin yadda ya ƙarasa maganar zaka gane da ciwon abun a zuciyarsa, Sapna ta yamutsa fuska kamar zata yi kuka ta ce, "Honey ta bari, baby is a changed person now, ina tare da ita koda yaushe keeping an eye on her, tun da ka ce baza ka amince da auren ta da Deen ba ta daina aikata hakan gaba ɗaya, da kanta ta yi mani rantsuwar tun lokacin bata sake aikatawa ba kuma na yarda da ita." Maleek ya yi shiru idonsa akan screen, kamar ba zai ce komai ba can ya ɗan sauke gajeruwar ajiyar zuciya murya ƙasa ya ce, "Allah Ya sa da gaske ta bari." a hankali Sapna ta ce in sha Allah ta bari, jin ta yi shiru bayan ɗan lokaci ya juyo ya kalle ta, ganin damuwa duk ta bayyana a kan fuskarta ya ɗan yi murmushi ya ce, "Kada ki damu kan ki, tun da Deen ɗin ba cewa ya yi ya fasa auren ta ba, I think zai haɗa su biyun ne ya aura and I'm okay with it." Sapna ta yi zuru tana kallon shi kawai. Bayan sallar la'asar daddy Sa'ad ya zo gidan hajiya kamar yadda ta buƙaci ganinsa, a falo suka zauna ya gaishe da ita cikin ladabi, hajiya na murmushi ta tambaye sa iyalinsa shima da murmushi ya ce mata duk suna lafiya sun ce a gaishe ta ta ce tana amsawa, Balaraba ta sa ta kawo mashi abun sha mai sanyi, bayan ya sha a nutse hajiya ta ce sai ya ji kira tana neman shi, daddy na murmushi ya ce eh Allah Ya sa kiran na alkhairi ne, hajiya ta ɗan yi shiru idonta ƙasa still da murmushi fuskarta, ta ce, "In sha Allah, dama aiki ne ɗan ku Deen ya kawo maku." Daddy ya ɗago yana kallon ta da ɗan alamun rashin fahimta, ta ɗan juyo ta kalle shi ta ce, "Na zuwa nema masa aure." Faffaɗan murmushin da ta ga daddy Sa'ad ya yi, ya sa ta ce, "Ka ma san da maganar ko?" Daddy ya ɗan gyara zama a nutse ya ce mata ya ga maganar dai a kafafen sada zumunta amman bai da tabbacin ko gaske ne, hajiya ta ɗan jinjina kai ta ce mashi da gaske ne, "Ma sha Allah, a ina ita yarinyar take ne?" Daddy ya tambaya, hajiya ta ce, "A nan makwabta suke, ku san a nan gidan ma suka fara haɗuwa da ita, ana aiko ta kawo mani awara, sune masu yin awaran da ake aikawa can gidan." Daddy ya jinjina kai still da murmushi fuskarsa ya ce eh ya ga har da maganar sana'ar da ita yarinyar ke yi aka yaɗa, hajiya ta kai hannu ta kama ha6a da alamun mamaki ta ce, "Yanzu har sana'ar tata aka watsa, ni da yake kwana biyu na rage shiga kafofin sada zumuntan saboda ido." Daddy ya jinjina mata kai ya ce aikuwa har da sana'arta duk an yaɗa, hajiya ta ce, "Kai amman dai mutane kamar basu da aikin yi da komai sai an watsa yanar gizo." Daddy na ƴar dariya ya ce dama in dai mutum ya shahara to kuwa komai da ya shafe shi sai an watsa a idon duniya, hajiya ta ɗan jinjina kai ta ce Allah Ya sa mu dace, daddy ya amsa kafin ya ce, "Yanzu auren ta za a je nema masa, an yi bincike kan yarinyar da iyayen ta ne?" Hajiya ta ce ta ɗan fara yin bincike akan ahalin yarinyar amman ba mai zurfi ba, sannan a sanin da ta yi ma yarinyar tana da halaye masu kyau don ku san ma hakan ne ya sa Deen fara yin hulɗa da ita, sannan suma iyayen yarinyar a ɗan binciken da ta yi an tabbatar mata da mutanen ƙwarai ne, nan ta bashi labarin abun da ya faru game da marigayi Habu wanda har yayi sanadiyyar da Deen ya ba ita yarinyar aiki, daddy Sa'ad ya hau jinjina kai tare da faffaɗan murmushi a kan fuskarsa, daga labarin sai ya ji Salma ta burge shi, hajiya ta ce yanzu abun da ya kamata sai su ƙara yin bincike akan su idan an tabbatar ba wata matsala sai su fidda lokacin zuwa nema masa auren, daddy ya amsa sai kuma ya ce, "To ya maganar ita ɗayar ta can in da yake da aka ce akwai maganar aure a tsakanin su?" Hajiya ta ɗan yi shiru kafin ta ce ya ce duk su biyun zai haɗa ya aura, daddy ya jinjina kai ya ce Allah Ya tabbatar da alkhairi, tambayar game da mahaifin Salma ya yi da in da gidan su yake, hajiya ta kwatanta masa tare da faɗi mashi sunan mahaifin yarinyar Malam Bashir Kafinta wanda ɗa ne ga marigayi Alhaji Maikuɗi Kafinta, daddy ya ce kamar ya so ya san sunan kakan nata, hajiya ta ce ai tsohon babban kafinta ne a garin kafin Allah ya yi masa rasuwa, ta yi masa kwatancen inda garejin su yake daddy ya ce ya gane wurin, daga haka suka aje magana kan daddy zai kara yin bincike akan su kafin a je neman aure. Kwanan Deen biyu a Funtua ya shirya komawa Abuja, sai da ya ji kaman daga nan ya wuce direct Uk don ya san idan ya koma ba za su kwashe ta da daɗi ba da mom, sai dai dole ya koma can kafin ya wuce London...aikuwa abun da yake gudun ne ya faru, yana isa bayan la'asar tun a babban falo mom ta tarbe shi da masifa, ta in da take shiga bata nan take fita ba, tana
Chapter 186 · 0% Book details