← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 197

Sashe 111

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read

bincike shi, a babban wurin da ake tsayawa da motoci ya tsaya ya ɗan bi cikin makarantar wadda ta yi masa kyau sosai da kallo, juyowa ya yi suka kalli juna tana murmushi ta yi mashi godiya, ya ce bari ya bata kuɗi ta siya abu idan an yi break ta yi ƴar dariya ta ce ai su ba a basu kuɗin break duk a cikin kuɗin makaranta ake sakawa sai dai su je su ci duk abun da suke so, ya ɗan buɗe ido ya ce lalle su ƴan gata ne shi lokacin da suka yi school a nan Abuja shi da Deen da abinci suke tafiya, sallama suka yi ya ce sai sun yi magana ta amsa da to, har ta kama ƙofar sai kuma ta juyo ta kalle shi ta ce, "Allah Ya kiyaye hanya Ya tsare man kai yaya Fahad." Ya lumshe mata ido tare da amsawa da, "Ameen, take care." Ta ɗaga kai daga haka ta buɗe ta fita, ya ɗan bita da kallo ta cikin glass itama tana tafiya tana waiwayen shi.....
Chapter 111 · 0% Book details