← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 197

Sashe 64

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Washe gari litinin bayan sallar la'asar su Deen suka gama yin shirin fita don kai ziyarar tallafi a ƙarƙashin charity foundation na Deen, a cikin tawagar har da hajiya da ta sha lifaya idanunta sanye da gilashi da kuma daddyn Fahad wato Alhaji Sa'ad shima ya yi shiga ta manyan mutane da kuma Fahad ɗin, daga nan kai tsaye gidan chairman suka nufa a nan suka haɗe da sauran mutanen da za a kai ziyarar da su ciki har da chirman ɗin, babban asibitin garin suka je inda suka samu kyakkyawar tarba daga manya da ƙananun ma'aikatan asibitin, bayan gaishe gaishe tare da gabatarwa da kuma bayanan da suka danganci asibitin, daga baya suka fara zagayawa suna duba marasa lafiya tare da basu tallafin kuɗi da kaya wanda suka haɗa da abinci da kuma barguna da gidan sauro duk a ƙarƙashin gidauniyar jin ƙai ta Deen, mutane da dama sun samu tallafin har da waɗanda ya biya ma kuɗin aiki da za a yi masu, daga cikin su akwai masu manyan lalurori da za a tura su Katsina a can za a yi masu aikin, haka kuma ya bada gudunmawar kuɗi masu yawa don magance wasu daga cikin matsalolin da asibitin ke fama da su, hatta suma ma'aikatan sun samu na su rabon, haka 6angaren marayu ma sun samu tallafin abinci, kaya da kuma kuɗi, ba ƙananun kuɗi Deen ya 6atar a ziyarar ba sai faman yabo da son barka ake. Tuni hotuna da bidiyon ziyarar suka karaɗe shafukan sada zumunta, haka ma kafafen sadarwar suna ta sanarwa game da ziyarar da kuma tallafin da ya bayar, haka akai ta turo masa da saƙonnin yabo, godiya da kuma fatan alkhairi, mutane suka yi ta ɗaurawa a shafukansu na sada zumunta gami da ambatun Deen ɗin da kuma kalaman yabo da nuna ƙauna a gare sa, mata da dama suka yi ta bayyana ra'ayin su na son Deen, gaba ɗaya social platforms Deen ne ke ta trending mutane na ta faman tambayoyi da bada bayanan da suka danganci rayuwarsa, wasu da dama da basu san komai da ya shafi harkar ƙwallo ba mamaki suke jin cewa shi ɗin asalin ɗan Najeriya ne ganin irin sufar shi da sam bata yi kama da ta ƴan nan ƙasar ba. A ranar Salma bata baro makaranta da wuri ba saboda ta tsaya wata ƙawarta da ta iya ƙunshi sosai ta yi mata zanen lalle baƙi da ratsin ja a hannuwanta, sosai ƙunshin ya yi kyau bayan ya bushe ta wanke suka baro makaranta, har da kuɗi ta ba ƙawar tata da ta yi mata, keke napep guda suka hawo aka ajiye Salma bakin kasuwa ita kuma kawar tata aka wuce da ita gida, wani shagon salon da take gani idan ta zo kasuwa ta je don a wanke mata kai, kusan wannan ne karo na farko da ta zo wankin kai shago a nan, amman idan ta je Kaduna hutu aunty Kubra na kai ta ana yi mata wash and set, cikin sa'a ba layi mai yin salon ɗin wadda bayerabiya ce musulma ta tarbi Salma cikin haba haba ta tambayi abun da za a mata, bayan ta sanar da ita ba 6ata lokaci aka fara shirin yi mata, saman wata kujera mai mazaunin mutum biyu Salma ta zauna ta cire hijabin uniform ɗinta tare da hular kanta, matar na daga wurin bakin kofa tana zuba ruwan da zata wanke mata kai, juyowa ta yi ta kalli Salma ta ce mata ta matso a wanke kan ta amsa mata da to, bayan ta zauna saman kujerar wankin kan matar na ɗan murmushi ta ce gashi da gani gashin nata yana da kyau, Salma ta yi ɗan murmushi ba tare da ta ce komai ba, hannu matar ta kai don ta cire ribbom ɗin da aka naɗe gashin da shi, da ɗan alamun firgici matar ta furta, "Ahh...!" Ganin irin tsawon gashin bayan ta cire mata ribbom, tsaye ta yi da alamun al'ajabi tana kallon gashin Salma da ya tarwatse ya yi mata rumfa tsawon shi har tsakiyar baya, hannu matar ta kai still da al'ajabi a kan fuskarta ta fara ta6a gashin baki buɗe, duk abun da take yi Salma na hango ta ta madubi dake daga can ciki, "Is this all ur hair?" Matar ta tambaya with shock, kai Salma ta ɗaga mata, "Kai ɗan garin nan ne?" Mai salon din ta sake tambaya, ta ƙara ɗaga mata kai, matar ta sake tambayarta wace unguwa, Salma ta faɗa mata, "Amman kai ba hausa ba ko? Are u an arab or an indian?" Har sai da tambayar ta ba Salma ƴar dariya, ta ce mata ita bahaushiya ce, "Ok babanka ko mamanka ne ba hausa ba? I mean you are biracial ba?" Kai Salma ta girgiza mata tana murmushi ganin yadda matar ta ruɗe tana ta faman tatta6a mata gashi ta ce ita iyayenta cikakkun hausawa ne, da yanayin shakku matar ta ce to amman dai a cikin grandparents nata dole akwai wanda ba bahaushe ba, Salma ta ce duk hausawa ne, mai salon dai ta kasa yarda ta ce to su fulani ne amma ba hausa ba, Salma da har ta fara ƙagara da tambayoyin matar ta ce mata kawai eh iyayenta fulani ne duk da ita dai a saninta iyayenta da kakanninta duk cikakkun hausawa ne, har gara ma kakarta ta 6angaren innarsu ita tabbas bafullatana ce sosai, da ƙyar ta samu matar ta fara yi mata wankin kan tana yi tana ci gaba da santin kyawun gashin ta faɗi mata cewa she had never come across hair like that so long and full tun da take sana'ar salon, ta ce duk da akwai masu gashi sosai dake zuwa, wasu gashinsu na da cika sosai amman ba tsawo, wasu kuma yana da tsawo ba cika, wasu kuma suna da yanayin irin gashin Salman amman bai kai nata ba, haka tai ta faman yi ma Salma surutu har bayan ta gama wankewa tana setting nashi, haka shima ƙunshin da aka yi ma Salma da ta gani sai da ta yi ta yaba shi, ita dai Salma murmushi kawai take abun da ya sa bata damu da surutan matar ba ta kan faɗi maa sha Allahu a cikin yabon nata, bayan an gama Salma ta siya lemu da biscuit da matar ke saidawa saboda yunwar da take ɗan ji, a nan ta ci bayan ta gama ta tambayi matar gaba ɗaya kuɗin, kafin ta faɗi mata ta yi mata tallar wasu mayukan gashi ta ce suna da kyau sosai daga Ghana ake kawo mata, Salma ta siya guda biyu ta haɗa da wasu ribbons masu kyau suma guda biyu, bayan ta faɗi mata kuɗin gaba ɗaya ta biya ta har da ƙari ta yi mata, aikuwa matar tai ta faman yi mata godiya tana washe baki, har da roƙon Salma kan ta ci gaba da zuwa nan ta ce tana yin komai na gyaran gashi Salma ta ce to, har da rakiya matar ta yo mata har waje, ita duk a ɗaukar ta Salma ɗiyar masu kuɗi ce ganin yanayin ta ga kuma cinikin da ta yi mata.
Chapter 64 · 0% Book details