← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 197

Sashe 35

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sam hajiya Binta bata ji tana son al'amarin ba bayan da aka sanar da su sakamakon binciken suka ji asalin Jameela da iyayenta, ba kuma don sun kasance talakawa ba don su basu gudun talaka, kawai daga yadda ta ji asalin na su ne akwai rauni, a hakan ma wai don basu ji halin su ba don Ammin su tasa an yi mata surkulle an rufe bakin mutane, kuma Allah Ya ara masu sa'a don kwata-kwata a binciken ba a faɗi wani abu mara kyau game da halin ƴan gidan ba. Hajiya bata goyi bayan auren ba ta ce ma Ibrahim ya haƙura da yarinyar nan shima ya yi auren zumunci kamar yayanshi, dama akwai ƙanwar Amina matar Sa'ad ita suke son su haɗa su, har ta nuna mashi in don kyawu ne itama tana da shi daidai gwargwado tun da fulanin asali ne, shima Alhaji Nuraddeen ya goyi bayan ra'ayin matar shi ya nuna ya haƙura kawai, aikuwa sun sha ruwan mamaki, don Ibrahim tubure masu ya yi kan shi dai ita yake so har da su kwanciya ciwo ya yi ta koke-koke, cikin lokaci ƙanƙani sai gashi ya rame, a haka lokacin komawar su ya yi suka tafi, ta bangaren Jamila itama hankalinta ya tashi jin iyayen shi basu amince ya aure ta ba, ta shiga damuwa sosai itama har da su kwanciya ciwo saboda ta ƙwallafa rai kan tafiya ƙasar waje, har da ita ke ƙara tayar ma Ibrahim ɗin hankali, in suna waya tai ta yi mashi kuka tana faɗin miye aibunta da iyayen shi za su ƙi amincewa da ita, idan don su talakawa ne ba shi ya ce hakan ba damuwa bane, sai da ta yi nisa a son shi ta rabu da duk samarinta masu son auren ta sai kuma a ce shima ba zai aure ta ba, waɗannan kalaman nata ke ƙara tayar mashi da hankali, sai gashi ciwo sosai ya yi mashi rigis, hankalin su Hajiya ya tashi lokacin da aka tabbatar masu da ya samu high bp, a lokacin likitansu wanda yake bature ya basu shawarar su bashi abun da yake so kada a rasa shi. Ƙarshe dole suka haƙura, wasu daga cikin dangin mahaifin shi dake Funtua aka wakilta su je nema mashi aure, Jameela ta yi farinciki kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha da ta ji zancen, dama sai da Ammin su tai ta ce mata ta kwantar da hankalinta, idan dai ba son su rasa yaron su suke ba to tabbas sai sun amince, don kuwa har da sharrinta ya sa son Jameela ya tsananta a zuciyar Ibrahim.

Watanni kaɗan aka saka na bikin, zuwa bayan babbar salla za a yi, dama duk hutun karshen shekara suke zuwa sai kuma wani lokacin suna yin azumi anan amman duk babbar salla anan suke yin ta saboda sun fi son su yi layya anan, lokacin da aka yi bikin Saleem yayan Maleek har ya haɗu da Jameelar lokacin dama sun zo hutun ƙarshen shekara ne.

A kwana a tashi har lokacin bikin ya yi, gaba ɗaya hidimar bikin a Kano aka yi ta gidan su Maleek suka zauna har aka gama aka ɗauko amarya zuwa Funtua, dama kafin bikin mahaifinshi ya gina mashi flat a cikin gidansu daga baya, wanda da babban fili ne har noma ake masu da damuna a ciki. A ranar da aka kawo Jameela da daddare bayan sallar isha Sapnah ƙanwarta ta fito daga part ɗin da suke na amarya ta nufo bangaren su hajiya, tana tafiya cikin harabar a nutse jikinta sanye da abaya ta ɗaura gyalen rigar a saman kanta, ita kanta bata san ina zata je ba ta dai fito ne kawai har ta iso gaban gidan, a daidai lokacin ango Ibrahim suka dawo daga masallaci tare da Maleek da wasu abokan su ƴan'uwan Ibrahim guda biyu, gaba ɗaya sun sha shadda sun fito a matasan samari yan hutu sai sakin ƙamshi suke, tun da suka shigo Maleek ya hango ta a tsaye daga gefen ginin, suna ƙarasa shigowa ciki ya gane fuskarta, har za su shige ya ce masu su je yana zuwa ya nufo ta, tana ganin ya nufo ta ta shiga yan kame-kame har zata juya ta bar wurin ya ƙaraso,

"Assalamu Alaiikum.." Sautin daddaɗar muryar shi ya sauka a kunnanta, ɗago idanunta tubarkallah ta yi ta ɗan kalle shi kamar tana tsoron amsawa ta amsa ƙasa-ƙasa, haɗa ido suka yi ya sakar mata murmushinsa mai burgewa, dama Maleek ba daga baya ba kyakkyawan saurayi ne sosai gashi dogo mai ɗan kaurin jiki,

"Sannu ko." Kai ta É—aga mashi kawai.

"Zamu wuce ne na hango ki tsaye na yi tunanin ko kina neman wani ne?" Muryar shi ba dai daÉ—i ba, kana jin yadda yake magana kuma zaka fahimci turanci ya zauna mashi, baki ta fara motsawa tana kame-kame sam ta kasa magana saboda yadda ya kafe ta da idanuwa, tun lokacin da ake cikin hidiman bikin ya fara ganin ta, kuma ya fahimci bata da hayaniya sannan tana da natsuwa sosai, don lokacin da aka yi dinner yana ganin yadda ta natsu a wuri É—aya bata tashi ta yi rawa ba kamar sauran Æ´an mata ba, kuma an yi mata É—inkin mutunci a ankon dinner É—in,

"Tell me if you need something." Ya faɗa tare da ɗage mata gira, da ƙyar ta buɗe baki cikin nutsattsiyar muryarta ta ce, "D..dama ina son in saka cajin wayana ne bansan na manto caja na a gida ba." Murmushi ya yi jin muryarta a karon farko,

"Yanzu kina buƙatan caja ke nan?" Shiru ta ɗan yi kafin ta ce eh in akwai inda ake sayarwa,

"Baki son in ara maki nawa?"
Yanayin fuskarta kamar zata yi murmushi ta ce, "To ai bansan ko kaima zaka yi amfani da shi ba ne."

"Ko zan yi amfani da shi sai in haƙura in baki tun da ke baƙuwarmu ce, kuma an ce ka karrama baƙon ka." Dan faffaɗan murmushi ta yi duka kumatun ta suka lotsa, sosai ya ga ta ƙara yi mashi kyau murmushin da ta yi, tambayar ta ina wayar tata ya yi ta ɗago ɗayan hannunta dake riƙe da ita ta miƙa mashi, bin wayar ya yi da kallo bayan ya amsa ba wata babba bace kuma da gani ta ɗan kwana biyu, ɗagowa ya yi ya kalle ta suka haɗa ido, da sauri ta sunkuyar da kanta, haka nan ta ji kunya ta kama ta, murmushi ya yi kamar ya fahimci dalilin sunkuyar da kan nata,

"Charger na ba zai yi ma wayan ba, amman idan ba damuwa mu je sai a siyo irin nata." Ɗagowa ta yi ta kalle shi, da yake tana tsananin buƙatar ta yi cajin saboda karatun jarabawar Jamb da take yi hakan ya sa ta amince, tare suka nufi parking space ya nuna mata ɗayan side ɗin motar da yake ƙoƙarin buɗewa, ita tama yi tunanin a ƙafa ne za su je siyowa, da yake ta san shi tun da aka fara hidiman bikin take ganin shi, hakan ne ya sa bata ji tsoron ta bishi ba,

"Ya sunan malamar ne?" Suna cikin tafiya bayan sun hau hanya ta ji ya tambaya ta ce mashi Sapnah,

"Nice name.." Kallon shi ta É—an yi a hankali ta ce mashi ta gode.

"Ni baki son sanin nawa sunan?" Bayan É—an lokaci ta ji ya tambaya, "Ina so.." Ta faÉ—a,

"No, baki so ai da kin tambaya."

"Da gaske ina so." Ta sake faÉ—a tana kallon shi, shiru ya yi idon shi akan hanya kamar ba zai faÉ—a ba,

"Suna na Maleek Usman Karaɗuwa, ni best friend ɗin ango ne kamar ma dai ƴan'uwa muke da shi, don iyayen mu ma abokai ne sosai." Kai ta ɗan jinjina bata ce komai ba, kallon ta ya ɗan yi ya tambayi ita miye alaƙarta da amaryan, ta ce mashi yayarta ce uwa ɗaya uba ɗaya. Daga haka suka fara sabawa bayan an siyo caja sai da ya ɗan zagaya da ita wai ta ga gari ya siyo mata kayan ƙwalam sannan suka dawo gida, kafin su rabu sai da ya amshi no ɗin ta.

Washe gari bayan an yi walima aka shirya maida dangin amarya, kafin su tafi saida suka yi sallama da juna ya kawo abu a cikin leda ya bata ya ce kyauta ce ya bata sai ta je gida sannan ta buɗe, ya yi mata hakan ne don daga yanayin ta ya fahimci idan ta san ko miye ba lalle ta amsa ba, haka kuwa aka yi sai da suka koma gida sannan ta buɗe ta ga sabuwar haɗaɗɗiyar waya a cikin kwalinta, ita tsoron ma wayar ta ji don wannan ne karo na farko da ta amshi abu irin haka a wurin wani namiji, ko wayar hannunta tsohuwar ta Jamila ce ta bata, aikuwa da ya kira ta sai da ta yi mashi ƙorafin wayar, ta ce wai zata bada a maido mashi ita bazata amsa ba tun da tana da ita, ya ce ya san da tana da itan ya bata kuma ai kyauta ce, da ta kafe kan sai ta maido mashi ya ce mata aikuwa idan ta yi hakan za su 6ata ba zai ƙara kiranta ba, tun da ta nuna mashi bai isa ya bata abu ta amsa ba duk da yanzu su kamar ƴan'uwa suke, jin hakan ya sa ta bashi haƙuri ta nuna mashi ba haka bane kawai ta ga tana da wayan ne, daga baya ta yi mashi godiya. A hankali sabo mai ƙarfi ya shiga tsakanin su, har bayan su Maleek sun bar ƙasar yana kiranta akai-akai suna gaisawa har su yi hira don ta sake da shi, daga baya har kuɗi yake turo mata ya ce ta yi buƙatunta na karatu da za ta fara......

*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*

_By Zainab Bature_

_Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._

Page 13
Chapter 35 · 0% Book details