← Book details A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 197

Sashe 27

A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ai har can ma na je amman ba su nan, part ɗin ma a kulle ya ke fa." Jimm mom ta ɗan yi, lokaci guda zuciyarta ta ayyana mata ko dai hasashenta na jiya ya tabbata ran shi ya 6aci ya yi tafiyar shi har da Fahad ɗin! Da sauri ta ajiye cup ɗin hannunta har sai da ya yi ƙara, kallon dad ta yi ta ce, "Ko ka san in da Deen ya ke?" ɗan ɗage ido ya yi alamar tunani, "ehumm..tare dai muka je masallaci da su, bayan mun dawo ne suka wuce part ɗin Deen nima na wuce nawa." Wata zabura da ta yi kamar wadda shock ɗin lantarki ya ja, da sauri ta fita daga cikin kujerar da take ta nufi cikin falo tana tafiya jikinta na amsawa dama rigar jikinta irin abayar nan ce mai fidda shape, a tsiyace take taka matattakalar benen gabanta har ɗan faɗuwa ya ke, ita bawai ma in komawar ya yi ba ce tafi ɗaga mata hankali, tunanin tare ya koma da Fahad ne ya sa ta wannan ruɗewar, da ƙarfi ta bangaza ƙofar part ɗin shi ta shige, kamar yadda Leemarh ta iske shi haka itama ta iske wayam, cikin ɗakin ta kutsa tana faman ƙwala masa kira, "Deen! Deen...!!" Ba in da bata duba ba amman babu alamar su, tsaye ta yi tare da ruƙe ƙugu tama rasa tunanin da zata yi na inda suka tafi, walk-in closet ɗin shi ta sake shiga tana ƙara dudduba kayan ciki, lokacin da ta fahimci ba wasu daga cikin akwatunan da ya zo da su jiya wani irin tsinkewa zuciyarta ta yi, har wani duhu-duhu take gani lokacin da ta fito ta nufi sauka ƙasa da sauri kaman za ta tashi sama, ko kallon in da su Leemarh suke bata yi ba bayan ta saukko kai tsaye ta nufi hanyar fita daga cikin falon, duk da ta san falon na su yana da girma amman sai take ganin kaman ya ƙara girma ganin ta ƙi kaiwa kofar duk da saurin da take zubawa, a cikin entryhall ta ja tunga ta fara ƙwala kira cikin tsananin ɗaga murya tana faɗin "Officer, officer at the gate! Call the officer at the gate!!" Ta ba wani jami'i dake tsaye gefen jibgegiyar baƙar jeep umarni, da sauri ya amsa mata da ok ya nufi hanyar gate, ba a ɗau lokaci ba wani jami'i jikinsa sanye da uniform yana riƙe da hularsa a hannu ya tunkaro ta yana tafiya da sauri, yana zuwa cikin girmamawa ya ce, "Good morning ma,"

"Did you see Deen go out of the house???

Ta jefa mashi tambayar ba tare da ta amsa gaisuwar da ya yi mata ba,

"Yes, sun fita lately tare da brother na shi." Wani mugun kallo ta watsa masa, "Wane brother É—in?" Sai ka ce bata san wa yake nufi ba,

"I mean, his cousin brother Fahad." Wani gauron numfashi ta saki ta É—an cije baki, "Sun faÉ—i maka ina suka tafi?"

"Yes, da na gan su har da kaya shine na tambaye su za su yi tafiya ne suka ce za su je Funtua." Da tsananin mamaki ta maimaita, "Funtua...?" Amsa mata ya yi da yes can Deen ya faÉ—i mashi za su tafi, har za ta juya ta dakata ta tambaye shi Deen ya tafi da jami'ai ya amsa mata da a'a su biyu kawai suka tafi, wata irin juyawa ta yi tamkar zakanya ta durfafi komawa cikin gidan, officer dake tsaye ya bi jikinta dake amsawa da kallo baki a buÉ—e har ta shige, a cikin falon ta haÉ—e da su Leemarh sun taho har da dad É—insu ya saka babbar rigar shi yana tafiya yana gyara zaman hular shi,

"Ka ga irin abun da nike faɗi maka ko! Yanzu Deen har ya kai ya yi tafiya ba tare da ya sanar mana ba! Rashin amfanin mu har ya kai haka a wurin shi? Ko da yake nasan wannan duk aikin ƙanin ubansa ne wanda ya riga ya gama mallake shi sai yadda ya yi da shi!" Shiru dad ya yi yana kallon ta yadda take zazzaga masifa har rufe ido take, sarai ya san da su Deen ɗin sun tafi Funtua, bayan dawowar su daga sallar asuba ne ya faɗi mashi zai bi Fahad, anan har yake mashi magana kan abun da mom ɗinsu ta sanar da shi, Deen ya kwashe komai ya faɗi mashi har lokacin da 6acin rai a tattare da shi, ya ce ma dad din ya yi tunanin in ya zo zai samu kwanciyar hankali tun da ya daɗe bai zo ba amman tun yanzu mom dinsa ta fara ɗaga mashi hankali shiyasa gara kawai ya tafi Funtua ya san zai fi samun kwanciyar hankali a can, jin hakan ya sa dad ɗin nashi goya mashi bayan hakan, amman saida ya yi mashi magana kan yakamata su tafi da security saboda tsaro, Deen ɗin ya nuna mashi ba sai ya tafi da jami'ai ba in sha Allahu za su je lafiya, anan suka yi bankwana har da Fahad, ya ce mashi ya faɗi ma yayansa Alhaji Sa'ad wato mahaifin Fahad ɗin yana nan zuwa bada daɗewa ba.

Da alamun kamar bai san komai ba ya tambaye ta ina suka tafi ne, a hasale ta faÉ—i mashi in da aka ce sun tafi,

"Tohh..Funtua suka tafi ke nan, kuma tun da sassafe kamar waɗanda aka kora, maimakon in ma tafiyar za su yi su bari gari ya waye sosai bayan sun yi breakfast sai su tafi." Wata uwar ƙwafa mom ta yi rai a matuƙar 6ace ta ce, "Wannan duk aikin Fahad ne, kuma wllh sai na ɗauki mataki akan hakan, in ba shi da bai da hankali ba ta ya daga zuwan shi zai ja shi su tafi wata Funtua, kuma ya san halin rashin tsaron da ake fama da shi shine zai ja shi ba tare da jami'ai ba, wato komai zai same shi ma ya same shi. Wama ya sani ko wani setup ne shiyasa ya ja shi suka tafi su kaɗai, dama ai an ce makashin ka yana tare da kai, abun da ke faruwa ke nan yanzu da na jikin mutum ake cutar da shi...."

"Subhanallahi! In sha Allahu hakan ma ba zai faru ba, ki rinƙa faɗin alkhairi pls." Dad ne ya faɗa jin irin maganganun da take faɗa mara sa daɗi, fuska a yamutse Leemarh take kallonta, wani 6acin rai take ji a cikin ranta jin yadda mom ɗin ke faɗan maganganu marasa daɗi akan Fahad, ga damuwar ya tafi ba tare da ta gan shi ba, kwantar mata da hankali dad ya shiga yi kan ba abun da zai faru in sha Allahu za su je lafiya, ganin ta wuce ciki ya sa shi tambayar ba taren za su fita ba? tana nufar cikin falon ta ɗan ɗaga masa hannu ta ce su tafi kawai ta fasa fita, ɗakinta ta nufa ta ɗauki wayarta ta shiga kiran wayar Deen sai faman jijjiga jiki take ta kasa tsayuwa a wuri ɗaya,

Zaune suke cikin motar Fahad suna tafiya kan hanya, Fahad ne ke yin driving yayin da Deen ke a kujerar gefen sa, Fahad yana sanye da brown dress suit pant wato dogon wando ruwan ƙasa sai baƙar dress shirt ya yi tucking rigar a cikin wandon ya saka baƙin belt, ƙafafunsa sanye da luxury loafers irin rufaffun takalma marasa igiya, da gani ba sai an fada ba takalman masu tsada ne daga laushin jikin su da yadda suke salƙi, a nutse yake juya sitiyarin motar wutsiyar hannun shi na ɗaure da baƙin agogo shima sai salƙi yake, yayin da shi kuma tauraron ɗan kwallo wato Nuree yake sanye da farar high-end dress shirt tare da farin jeans ya ɗan matse daga ƙasa, a saman rigar ya ɗaura baƙar tailored blazer wato riga mai kaman jacket ta kawo mashi zuwa ƙasan kugunsa, bai saka ma6allan rigan guda biyu dake daga can ƙasa ba hakan yasa ana ganin farar ta ciki da ya yi tucking ɗinta da baƙin ubansun belt da kan shi ke wani irin ƙyalli, shima irin takalman dake ƙafar Fahad ne a tashi kafar iri ɗaya ya siya masu, hannun shi guda na ɗaure da agogo Rolex yayin da baƙar sumarsa ya yi baya da ita ya ɗaure ta daga ƙasa, Ya Allah! Yadda ya yi sai ka rantse hausa baza ta fito daga bakinsa ba, gaba ɗaya kana ganinsu ka san ba ƙananun kaya bane suka saka, yadda kayan suka yi fitting na su so well abun ba a magana sai daddaɗan ƙamshi ke tashi daga jikinsu, gaba ɗaya ya karaɗe cikin motar ya haɗe da sanyayyan iskan A.c, shima Fahad sumar shi ta sha gyara sai salƙi take, daga gaban Deen hular shi ce baseball baƙa ajiye wato irin hular da ake kira da face cap, tana da tambarin premium brand da aka yi ta daga gaba. A hankali sautin ƙira'ar da Fahad ya kunna ke tashi, dama shi haka yake da wuya ka ga yana driving ya kunna waƙa, duk da wani lokacin yana kunna music idan yana tafiya ba mai nisa ba ko cikin gari haka, Deen na zaune ya ɗan zamo jikinsa kaɗan ta yadda ya kwantar da kanshi a jikin seat ya lumshe idanunsa, idan ka gan shi zaka yi tunanin bacci yake, saidai ba haka bane yana bin ƙira'ar da ke tashi ne a cikin zuciyarsa, jefi-jefi suke yin magana tsakanin su sa6anin lokacin da suka taso hira suke sosai, yanzu da suka yi nisa ne suka rage yin magana ba kamar Deen da ya fara gajiya da zaman motan, har magana Fahad ya yi mashi na ko ya kwantar da seat ɗin ya ji daɗin zaman ya ce mashi a'a yadda yake ma lafiya lau. Tun da suka taho basu tsaya ba sai a checkpoint biyu da aka tsayar da su gaba ɗaya kuma da suka tsaya jami'an sun san fuskan Deen kuma dama suna da labarin zuwan shi, don akwai masu supporting team ɗinsa, hakan ya sa sun ɗan 6ata lokaci kaɗan a wurin gaisawa da su har da waɗanda suka yi hotuna da shi,
Chapter 27 · 0% Book details