Sashe 1
A Cikin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*_Bossladieswriters_*
*Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin Ƙai*
Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah (SWT), Mai kowa, Mai komai, wanda Ya bani ikon fara wannan sabon littafi nawa mai suna “A Cikin Rayuwa.â€
Ina roƙon Allah Ya sa littafin nan ya amfane ni da ku gaba ɗaya,
Ya Ubangiji, Ka bani ƙwarin gwiwa da nutsuwa; yadda muka fara lafiya, Ka sa mu kammala a cikin ƙoshin lafiya. Allah Ka kiyaye ni daga rubuta abin da zai cutar da ni ko da al’umma baki ɗaya.
Ameen.
*BAYANI NA MUSAMMAN (Disclaimer)*
Labarin nan ƙirƙirarren labari ne, ba na gaske ba. Duk wani suna, wuri, ko yanayi da ya yi kama da na ainihi, hakan ya faru ne bisa bazata, ba da niyya ba. Na rubuta wannan littafi ne da nufin isar da saƙo game da rayuwa, soyayya, ƙaddara, da darasin da ke tattare da su, ba don nuna wani mutum ko abin da ya faru a zahiri ba. Idan wani ya karanta littafin ya ga wani abu da ya yi kama da shi ko da rayuwarsa, to hakan ba wai na nufin shi ba ne, domin ni ɗan’adam ce, ba ni da ikon sanin yadda rayuwar wani ke gudana sai dai abin da Allah Ya bani damar hasashe a kai. Manufar littafin ita ce bayyana darasi, motsa tunani, da kawo haske cikin tafiyar rayuwa, ba don cin zarafi ko kushe kowa ba.
*Godiya ta Musamman*
Jinjina ta musamman ga ƴan ƙungiyata, Boss Bature, QueenMarh, da Hafsat Amjad.
Nagode da goyon baya da kalaman ƙarfafa gwiwa a koda yaushe. May Allah continue to unite our hearts and raise *BossLadiesWriters* higher. Ameen.
Wannan littafi tukuici ne gare ki, *Mommy Kubrah*.
Allah Ya ƙara miki lafiya da nisan kwana mai albarka, Ya bar mana zumunci har Aljanna.
_Beloved sis, Hafsat Bature, your support means everything to me._
_There are no words enough to express my gratitude, all I can say is, may Allah bless and strengthen you always._
Ya Rabb! Bless and have mercy on all mothers, especially my mother. 🤲â¤ï¸
_My P.A, Munarh Bature, a ɗaura damarar komawa fagen daga, let’s go again!_
*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*
_By Zainab Bature (Zeelaluh)_
CHAPTER ONE
Farkon Tafiya
_A cikin rayuwa, wasu abubuwa ba su faruwa a bisa kuskure, sai don a koya mana darasi._
_Bata san cewa ƙaddararta za ta haɗa ta da wani da duniya ke kallon sa a talabijin ba._
_Amma kafin soyayya ta zamo haske a gare ta, dole ne ta ratsa cikin duhun da rayuwa ta tanadar mata, duhun da ke ɗauke da sirri, hawaye, da ƙaddarar da za ta canza mata rayuwa har abada....._
Kaduna State,
Saturday, 10:00am
Babbar harabar makarantar cike take da mutane, kasantuwar yau ne suke yin bikin yaye ɗalibai da bada kyaututtuka ga waɗanda suka yi ƙwazo (speech and prize giving day). Mahalarta taron sun haɗa da iyaye da ƴan'uwan yaran da suka gama karatu a matakin primary da kuma secondary, saura sun haɗa da manyan baƙi da aka gayyata ciki har da masu manyan muƙamai a gwamnati. Duk da makarantar bata gwamnati bace mai zaman kanta ce (private school) amman kana gani kasan babbar makaranta ce, tana da tsarin gini mai matuƙar kyau da kuma bangarorin karatu ukku, (Nursery, Primary, Secondary). Gaba ɗaya mahalartan suna zaune a cikin manyan rumfuna da aka kafa a bangarorin babban filin makarantar, bangaren da iyaye tare da ƴan'uwa da abokan arziki suke daban, haka manyan baƙi suna a bangare na musamman an tanadar masu da abubuwan ci da sha a saman teburan dake gaban manyan kujerun da suke zaune, daga cikin manyan baƙin akwai matar kwamishinan ilimi na jahar Kaduna mai suna Hajiya Aisha, da wasu daga ma'aikatar ilimi ta jahar. Iyaye da ƴan'uwan ɗaliban da ke karatu a makarantar kowa ya yi shiga ta alfarma wadda kallo daya zai bayyana maka kowa yana da hali daidai da nasa, kasantuwar karatu a makarantar na da kuɗi ba laifi, amman kuma makarantar na bada ilimi sosai. Suma ɗaliban makarantar suna a cikin rumfa daban, gaba ɗayansu suna sanye da kayan makarantar, yayin da ɗaliban da ake yayewa suke zaune daga gaba kowanne na sanye da uniform na makarantar daga sama sun daura rigar da ke nuni da sune suka kammala karatu (graduation gown and cap).
Kowa ya natsu yana kallo da saurar diramar turanci da wasu daga cikin ɗaliban suke gabatarwa kan muhimmancin ilimi, a diramar gidan wani magidanci ne dake da mata ɗaya da kuma yara mata guda biyu Fa'iza da Maryam, sai dai ba uwa ɗaya ta haife su ba su duka, matar gidan ta kasance tana gatanta wadda itace ɗiyarta da ta haifa wato Fa'iza, komi yarinyar take so tana yi mata, yayin da ɗayar da ba a so mai suna Maryam mahaifiyarta ta rasu a wurin haihuwarta take fuskantar tsangwama da ƙyara, sai mahaifinta na gida ne take samun ɗan sassauci don shi yana matuƙar son ta da tausaya mata, duk da shima ba wani katabus gare shi ba a gidan. Haka ake ɗaura ma wadda ba a so talla safe da yamma duk da ta kasance tana matuƙar son yin ilimi amman an hana ta zuwa makaranta, saboda aminiyar matar babanta da ke ruƙonta ta bata shawarar kada ta sake ta bari yarinyar ta yi karatu, a cewar ƙawar tata yadda take tubarkalla kyakkyawa idan ta yi karatu ta goge to ƙarshe ba ƙaramin mutum ne zai aure ta ba. Duk wasu aikace-aikacen gidan ita ce take yin su, idan ka ganta ba wata suturar kirki haka wurin kwanciyarta a ƙasa ta ke kwana saman wani ɗan mataccen zani, duk da cikin gadon kayan mahaifiyarta da ta samu har da katifa amman an hana ta kwanciya a kai. Saboda son karatun da take yi ne yasa duk idan aka ɗaura mata talla da safe ta kai wata makaranta, sai ta je bakin tagar wani aji tana sauraren abubuwan da ake koya masu, wani lokacin idan aka yi tambaya ma ita ce take bada amsa daga waje, wannan dalilin ya sa wani malamin turanci ya rinƙa siye abun da take sayarwa ya raba ma ɗalibai ita kuma sai ya saka ta shiga cikin ajin ta zauna don ta faɗa masa halin da take ciki a gidansu da hana ta karatun da aka yi, daga baya ganin irin ƙoƙarin ta ya sa malamin ya tunkari shugaban makarantar da lamarinta. Da taimakon shugaban makarantar da malamin suka sa ta fara yin karatu kyauta. Saboda ƙwazonta bayan gama karatun ta na primary ta samu tallafin karatu (scholarship) daga gwamnati har zuwa jami'i zata yi karatu kyauta. A ƙarshe ta yi nasarar zama ƙwararriyar likita, yayin da ƴar'uwarta Fa'iza ta saka shiririta da yawon bin maza har ta yi cikin shege wanda mahaifiyarta da ƙawarta suka yi ƙoƙarin zubar da shi kamar yadda suka saba yi mata amman ya ƙi zubewa, ƙarshe ta haɗu da lalura bayan ta haife cikin ba rai, yar'uwarta Maryam da ta zama likita ita ta yi mata aiki har ta samu lafiya, ita ta gina masu gida take kuma tallafa ma rayuwar su. A ƙarshe suka ƙare da yin kukan dana sani.
Bayan gama yin diramar mutane suka shiga tafa ma ɗaliban kan irin ƙoƙarin da suka yi diramar ta tafi daidai ta yi ma'ana sosai, da kuma musamman yadda suka rinƙa yin magana da turanci cikin gwanancewa ba tare da wata tangarɗa ba, ɗalibar da ta fito a matsayin Maryam wato wadda ba a so mai suna SALMA BASHIR, ta fi samun yabo a wurin mutane ganin duk da ƙananun shekarunta don bata wuce shekara sha biyu ba amman ta nuna ƙwazo sosai a diramar. Bayan gama diramar an ci gaba da yin programs daban-daban na ilimi kuma kowanne akwai dalibar nan mai suna Salma Bashir wadda ta kasance kwakkyawar gaske, kanta na sanye da hular rigar kammala karatun jikinta, tana da gashi mai tsawo sosai don kitson da aka yi mata na gaba ya sauko har zuwa ƙirjinta. Abu na ƙarshe da aka yi shine bada kyaututtuka ga ɗalibai masu ƙwazo, Salma Bashir ta samu kyaututtuka da dama ciki akwai ta ɗalibar da ta fi ƙwazo a matakin primary, akwai ta bajinta da ta yi a diramar da aka yi kan ilimi, sannan a bangaren english club ɗin makarantar an bata kyauta cikin daliban primary masu ƙwazo a bangaren debate da quiz, haka a bangaren wasanni wato sport nan ma ta samu kyauta. Kyauta ta ƙarshe da za a bata aka bayyana matar kwamishinan ilimi hajiya Aisha a matsayin wadda zata bata kyautar, bayan Salma ta je gabanta, hajiya Aisha tana murmushi ta fara miƙa mata hannunta da ya sha gold suka yi musabaha ta ce, "Congratulations, Salmat. Keep working hard and stay focused, the sky is your limit." Jinjina mata kai Salma ta yi da faffaɗan murmushi akan fuskarta ta ce, "In sha Allah. Thank you maa." Jinjina mata kai Hajiya Aisha ta yi da murmushi akan fuskarta, bayan ta bata kyautar ta dakatar da ita, ta juya tare da miƙa ma ƙawarta da suka zo tare suke zaune a wuri guda hannu, buɗe jaka matar ta yi ta fiddo rafar kudi yan dubu guda biyu wato dubu ɗari biyu ta miƙa mata, hajiya Aisha ta ɗaura ma Salma a saman kyautar ta ce mata itama ga tata kyautar nan, gaba ɗaya wurin aka saka tafi masu ɗaukar hotuna da vedio suna ta ɗaukar su, godiya Salma ta yi mata ta juya ta koma wurin zaman ta, bayan hajiya Aisha ta koma ta zauna ƙawarta hajiya Zulaihat tana murmushi ta ce, "Yarinyar ta burge ni sosai, ga kyau ga ƙwaƙwalwa. Da ta zo gaban ki sai na ji inama a ce ɗiyar ki ce don har ɗan yanayi na ga kun yi." Murmushi hajiya Aisha ta yi don ta san dalilin yin maganar tata, bai wuce sanin cewa Allah bai bata ɗiya mace ba sai maza, sai dai itama a cikin ranta ba ƙaramin burgeta yarinyar ta yi ba har ta ji sha'awar inama a ce Allah Ya bata ɗiya mace kamar ta.