← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 190

Sashe 99

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 5 min read

"Shima shegen da Mai gadi..." Ya fada yana parking motar shi a parking space dake kusa da sabuwar jeep da Salman ya saya, fitowa yayi ya nufi wajen Mai gadi suka gaisa Sannan suhail ya nemi ganin Salman, da sauri maigadin yaje part din Salman dake zaune yana Shan wani exotic wine kafa daya kan daya ya fada mashi yayi bako, idanuwa Salman ya daga kaman Mai Jin bacci ya kalli maigadin tare da tambaya shi wanene, "Nima ban sani ba.." Maigadin ya amsa mashi cikin girmamawa, Dan bata rai Salman yayi Sannan yace "Bafa gadi kadai na daukeka ba...yana daga cikin aikinka kasan Wanda ya shigo da kuma Wanda zai fita...je ka tambayeshi waye." Ya fadawa maigadin Sannan ya koma yayi relaxing with his eyes closed, maigadin fita yayi ya tambayi suhail koshi waye, nan suhail ya fada mashi, maigadin na juyawa suhail ya saki dariya yana cewa "Imagine this rubbish..." Ya fada yana murmushi, maigadin na shiga ya shaidawa Salman cewa suhail né, da sauri Salman ya leka ta window yaga da gaske suhail né tsaye da hannuwanshi biyu Cikin aljihunshi, idanuwa ya zaro ganin suhail din ko kasan he couldn't believe his eyes, tsayuwa yayi kaman Mai tunans Sannan ya Chanza yanayin tsayuwarshi ya tsaya kaman wani aliko dangote yace a Kira shi, maigadin komawa yayi ya sanar da suhail ya shigo, gira daya ya daga ya taka cikin kasaita kaman yanda ya Saba ya nufi part din, da sallama ya shiga, yana daga Kai ya ga Salman tsaye sai faman daga shoulder kawai yake ya amsa sallamar da ass dinshi instead da bakinshi, Dan murmushi suhail ya saki ya mika mashi hannu Don su gaisa, kallon hannun Salman yayi for a moment kawai sai yace "Pls ka fadi abinda ya kawoka..bani da ishesshan lokaci..." Ya fada face dinshi daddaure, wata yar bazawarar dariya suhail ya saki Sannan yace "Oh sorry fa...banzo Don bata lokacin ka...I just came to apologize for the way I have treated you...pls ka gafarta min and let bygones be bygones..." Inji suhail dake ji tamkar ya shakoshi saboda irin kallon da yake mashi, Aikam wani irin dariya Salman ya fara yi yana clapping hands dinshi, sama ya kalla Sannan yace "Wayyo rabbi ka gama min komai...wai ni Salman ake bawa hakuri Don an San na wuce su.." Dariya suhail ya saki Jin wannan statement din, Salman ya cigaba dacewa "Yau ni Salman ake takowa har inda nake Ana Néman a shirya Dani Don nayi kudi...Kai duniya..." Ya fada sannan ya maido duban shi ha suhail sake tsaye yana dariya, nuna shi yayi da yatsa, suhail yayi saurin cewa "Don't you ever in your miserable life point your finger at me..." Suhail ya daka mashi tsawa tamkar har lokacin yana karkashinshi, sai sa Salman ya razana Don yafa mance he's now rich, sai daga baya ya gane Ashe ba gidansu suhail yake ba yayi saurin cewa "In na nunaka me zakayi?.." Shima ya dakawa suhail tsawa yana sake nuna shi, kauda Kai suhail yayi ya saki murmushi Don yasan in har ya dauki abun da zafi bazai cimma burin shi ba, "Nace in na nunaka what will you do?.. Ohhh zaka mareni?.. Or zaka sani wanki da guga..." Ya sake fada cikin tsananin daga murya, dariya suhail yayi yace "Ohh Ashe anyi min wanki da guga kou?." Ya fada hannunshi kan bakinshi yana dariya, haushi Salman ya sake ji yace "Now ka fitar min a gida..." Bai idaba suhail ya sake kwacewa da dariya da karfi yana cewa "Anyi gida...pls mr new into money ka saurara kaji abinda ke tafe Dani...na daya inason ka sani ba Don chicken change Dinka na zo nan ba because no matter how rich you're..you will be poor to me..." Suhail ya fada yan nuna kanshi, Sannan ya sake cewa "No matter how rich you're you will always be a driver to me...you know why?.." Ya fada yana gyara tsayuwarshi Sannan yace "Because no matter how you wash pigs they will always go back into dirt...mark my words ko Kafi dangote kudi Baka isheni kallo ba balle wani Abu naka ya tsonemin ido..." Dariya Salman yayi yace "Look at this good for nothing.." Bai idaba suhail ya nuna shi yana cewa "Kaiiii!!! Watch you slimmy tongue..Wallahi don't get on my nerves..." Suhail yafada duk idanuwa waje, da sauri Salman yace "Kar ka sake kayi min barking cikin gida..nan ba gidan karnuka bane" Aikam bai idaba suhail ya dauke shi da Mari, shima hannya daga ya rama Marinshi yana cewa "Kana ganin Dane da kake yi min in kyaleka?.." Yafada sounding so tense, suhail rike cheeks dinshi yayi yana imagining me zaiyi mashi ya huce, kawai Dana sanin zuwanshi kawai yake, "Wallahi daga yau ka Kara shigar min gida sai na sa an yi maka mugun duka..yau ma kaci darajan alhaji...da Wallahi Mai rabani da Kai sai kotu..." Salman ya fada feeling ontop of the world, ahankali suhail ya juya da niyyar tafiya, sai yaji Salman yace "And one last thing ka sani babu Mai rabani da Fatima...she's the only girl that I have been slapped because of..kuma nasan you love her..marrying her will be abinda nasan in na yi zan kuntata maka...kuma Wallahi sai na aureta...dukda I know you love her more than I love her..."Nan take face din suhail ya koma kaman jini saboda yanda face dinshi yayi ja, wani irin wulankantancen kallo ya watsawa Salman before saying...
Chapter 99 · 0% Book details