Sashe 30
Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 8 min read
Suhail kam tuki yake hawaye suna fita yana gogewa new ones na zubowa, yayi kokarin Hana kanshi zubda hawaye amma Sam eyes dinshi sun ki daina Fiddo su, ya rasa takamaimen abinda yakewa hawaye , yasan dai ba Marin da alhaji yayi mashi bane, Sannan Sam baijin haushin alhaji. Tuki yake in high speed yana over taking wasu motoci, kawai babu abinda yake gani sai Maryam rike da Salman, bai San irin zuciyar dake gareshi ba Don gani yake in aka mika mashi Salman tsaf zai yanke mashi wuya. Tuki kawai yake amma bai San inda zashi ba, wani Mai a daidaita yazo over taking kawai sai motarshi ta gogi adaidaitan, duk Wanda ke wurin Sunga abinda ya faru and suhail né da laifi amma parking motarshi yayi gefen titi ya fito a fusace ya dubi gefen motar daya gurje kad'an, dawowa yayi afusace ya nufi inda Mai adaidaitan Wanda ke Dan karamin yaro da bai wuce shekara 21 zuwa 22 ba,
"Dan ubanka titin na gidanku né da zaka hau tsakiyar titi?..." Suhail ya dakawa yaron tsawa yana nufo inda yaron ke tsaye, kallon mamaki yaron yayi mashi tare dacewa
"Haba malam..kaine fa da laifi....Baka ganin har kusa zubda ni da passengers na kayi..." Inji yaron, suhail Kara fusata yayi abunka da Wanda ya fito daga gida da fushi, nuna goshin yaron yayi da Dan yatsa har yana tura shi baya
"Dan uwarka ni kake fadawa magana?... Ni sa'ar ubanka né?..." Ya fada cikin fushi sosai, kallon banza yaron yayi mashi sannan yace
"Ba dai uwata ba..." Bai idaba suhail ya daukeshi da wani zazzafan Mari, tare da shake shi, da sauri mutane suka fara taruwa wurin, suhail shake yaron yayi yana sakar mashi fushinshi Don babu abinda yake sai Marin yaron, duk yanda mutanen wurin ke kokarin Hana suhail dukan yaron kasawa sukayi, wasu masu adaidaita uku suka zo wucewa suka hangi abinda ke faruwa, nan suka fito, batare da sunji abinda ya wakana ba suka hau suhail da duka, ba su barshi ba sai da suka hada mashi jini da majina,
"Ba a haifi Dan shegiyar da zai ji zarafin dan adaidaita ba..tunda ba gidan ubanka yazo bara ba..." Inji daya daga cikin mutanen da suka daki suhail, shikam suhail baisan inda yake ba Don ji yake duk ilahirin jikinshi nayi mashi ciwo. Ahankali ya Kai hannu saitin hancin shi yaga jini, daga idanuwa yayi Don yaga wayanda sukayi mashi irin wannan cin mutunci cikin garin Kano amma abun mamaki bai gani sosai, duk mutanen dake tsaye bai ganinsu sosai, ji yayi wani mutum ya rike shi yana cewa
"Ai kayi gangancin dukan Dan adaidaita...Don in ba'a cikin mutane bane suna iya kasheka..." Inji mutumin dake rike da suhail,
"Dan..Allah....ka..kaini hospital..." Suhail ya fada cikin wani irin murya kaman ba nashi ba.
"Da akwai asibiti nan kusa..." Inji mutumin,
"Ka kaini..." Suhail ya fada atakaice, yana Jin saliva dake bakin shi ya Chanza, zubdawa yayi yaga jini, da taimakon wasu mutane biyu ya isa hospital, ji yake kaman an Chanza mashi halittar fuskarshi Don Marin da wani ya farayi mashi ya dauke mashi wuta. Yana zuwa Doctor ya duba shi ya tabbatar mashi it's nothing serious amma suhail sai cewa yake a duba mashi jikinshi da kyau Don bai Jin dadin jikinshi, yanda yake magana kaman karamin yaro yasa Doctor sakin dariya tare dacewa
"Kai kana Dan Hutu Mai ya kaika fada da yan napep...ai ba sauki garesu ba..." Doctor ya fada mashi yana dariya, ajiyan zuciya suhail ya saki yana tunanin me ma ya Fiddo shi daga gida in the first place, sai lokacin ya tuna da yar gajeren drama da yayi da Maryam, ahankali ya mike yayi wa Doctor Godiya tare da zuwa wurin reception ya biya kudin treatment da akayi mashi, still bai Jin dadin jikinshi, yana fita wajen gate ya hangi motar shi daga nesa, takawa yayi har wajen ya bude ya shiga yana kallon kanshi ta cikin mirror, he couldn't believe his eyes Don face dinshi ya kumbura sosai sannan kasan idonshi na dama da akwai jini,
"Handsome face dina akayiwa haka?..." Yafada yana tale baki kaman zaiyi kuka, yafi minti goma nan zaune yana fatan Allah ya gamashi da ko mutum daya né cikin wayanda sukayi mashi wannan tozartar da babu abinda zai hanashi kulle dukkan danginsu. Wayanshi dake cikin motar ta fara ringing, yasan mom dinshi ce Don ringing tone dinta daban ne, picking yayi ya Dora kan kunneshi,
"Haba eyeballs...why zakayi min haka gaban mutane?... Inata Baka hakuri amma sai ka disgani ka fita?...now fada min kana Ina?..." Ta tambayeshi cikin lallami,
"Sorry mommy...am coming back now..." Ya fada cikin sanyinmurya,
"Ok dear...me zan ajiye maka?. " Ta tambayeshi kaman ba Yanzu ya bar gidan ba,
"Nothing mom..." Ya amsa mata cikin kasala yana tunanin yanda zatayi acting in ta San abinda ya sameshi,
"Ok then I love you...sai ka dawo..."
"Love you too momcy..." Ya fada yana Dan sakin murmushi, kashe wayar yayi sannan ya tada motar ya koma gida, kafin ya karasa unguwar aka Kira sallar magrib, masjid din unguwar su ya tsaya yayi sallah, bayan ya fito suka hadu da dad dinshi shima ya fito daga masallacin, kallon face dinshi alhaji yayi Fuskanshi dauke da alaman tambaya, shi kuma suhail sadda Kai kasa yayi Don yaga irin kallon da dad dinshi ke yi mashi, baki alhaji ya tabe ya Kama hanyan gida shi kuma suhail ya shiga mota ya karasa gida. Ya so shiga bangaren hajiya amma yana Jin kunyan haduwa da Maryam, gani yake ba aji bane Maryam ta ganshi haka, bangaren shi ya nufa yana kallon inda Maryam ta tsaya rike da kugun Salman, ajiyan zuciya ya saki ya bude kofa ya shiga bangaren shi, bedroom ya shiga ya tsaya gaban madubi yana sake karewa Fuskanshi kallo, Dan guntun tsoki yaja ya zauna bakin gado, kawai gurin shi a Yanzu shine ya fadawa Maryam abinda yake ji game daita amma baisan ta yanda zaiyi approaching dinta ba, Sam bai tunanin Maryam zata ce aa dashi, asalima abinda yake tunani shine zatayi farin ciki in har ya furta mata Kalman so nikam nace naka wasa né eyeballs. Kwanciya yayi Yana kallon ceiling, babu abinda yake sai tunani, he wish yana iya fadawa su sadeeq abinda ke faruwa Don su taimaka mashi da hanyoyin da zai bi amma not after yanda ya dinga cika baki kanta. Ji yayi an bude Kofan falon shi, mikewa yayi zaune, hajiya ce ta shigo bedroom dinshi, Tana shiga ta kurawa suhail Ido shi kuma ya sadda Kai kasa, da sauri ta karasa inda yake zaune a bakin gado ta daga hab'ar shi Tana inspecting fuskar shi,
"My Prince Charming meyasameka?.." Ta tambayeshi cikin tashin hankali tamkar ta ganshi babu Kai,ahankali ya kaman hannunta dake hab'arshi yace
"Mommy its nothing..." Ya fada cikin karfin Hali.
"Ban gane it's nothing ba...ka fada min abinda ya sameka " Ta tambayeshi sounding so restless, hannunshi cikin nata yace
"Mommy wasu yan iska né..." Bai idaba hajiya ta Dora hannu bisa Kai Tana salati, kaman zatayi kuka tace
"Me kayi masu...." Tafad'a Tana duba jikinshi, zama yayi Tana duba nan ta duba chan, bayan wuyan shi ta gani kumbure
"Nace me kayi masu?.." Ta sake tambayan shi, nan ya fada mata abinda ya faru, goya mashi baya tayi ta dinga fada Tana cewa
"Don wannan shine suka tab'a min Kai?... Suka hada kazamar jikinsu da naka?...amma wallahi sun sha Dani..." Tafad'a cike da takaici da bakin Cikin abinda akayi wa danta, zama tayi bakin gadon kusa dashi sannan tace
"Dan Allah next time kar ka Kara Bari su tab'a min Kai....ko me ya faru tsakanin ku kawai ka wuce kayi tafiyar ka..." Ta fad'a mashi, hannunta rike da nashi, ahankali ya gyad'a mata kai, shuru né ya d'an biyo baya sannan hajiya ta sake cewa
"Wai dazun me ya faru?..", daga idanuwa suhail yayi ya kalleta sannan yace
"Mom...wai kawai d'an zanyiwa wannan yarinyar fad'a shine ta gudu ta boye bayan Salman tare da rungume shi...." Ya karasa maganar cike da bakin ciki, baki hajiya ta rike Tana mamakin abinda suhail ya fada mata,
"Rungumewa fa kace....are you sure?.." Ta tambayeshi don tabbatar da gaskiyar maganar, ahankali suhail ya daga mata Kai idanuwanshi suna Kara cikowa da kwalla, ahankali hajiya ta Dora kanshi k'an kafadarta, da Tana ganin suhail dinta as a strong man amma sai Yanzu ta gane he's very weak and vulnerable,
"Ina ruwan Salman da zai tsaya har ta rike shi?.."
"Ai mummy Ina tunanin da akwai relationship tsakanin su...ko yau da ya maidato daga islamiyya tafi minti goma bata fito daga cikin mota ba...suna zaune cikin motar sai labari suke kaman motar ubanshi Itakuma shegiyar ta biye mashi...." Ya karasa maganar tare da jan d'an garejen tsoki, ajiyan zuciya hajiya ta saki tareda cewa
"Hmmm nidai I think ka manta da ita....she's not your class..." Inji hajiya, suhail bai tsaya ya Ida sauraron abinda zata ce ba ya mike ya koma falo kaman zai tashi sama, bayanshi hajiya tabi da kallo Tana mamakin abinda suhail dinta ya gani jikin wannan yarinyar da yakeson kashe kanshi saboda ita Don ita ko kadan yarinyar batayi mata ba. Falo suhail ya koma ya hada Kai da gwiwa looking so restless, falo hajiya ta dawo zatayi magana yayi saurin cewa
"Mommy Yanzu cewa zakiyi in rabu daita?... U think that will be easy for me?... Mommy Santa fa nake...wallahi mommy Ina iya mutuwa saboda rashinta...nidai mommy ki taimaka min da which way forward...amma banda zancen rabuwa daita..." Ya karasa maganar yana turo baki kaman wani karamin yaro.
"Tou dear why not ka bar bata tsoro?... Naga kaman Tana Jin tsoron ka...Don dazun Baka ma doketa ba amma duk hankalinta ya tashi saboda tsoro,..sannan I will suggest Ka dinga kaita islamiyya ..." Da sauri suhail ya kalli mom dinshi
"Wow mom...Sam ban tab'a wannan tunanin ba... But mommy wa zai Kai ki aiki?... Kinsan kafin in dawo daga kaiki sun tafi..." Ya fada yana jiran Amsar ta, sannan yana aduar Allah yasa ta fad'i abinda ke ranshi,
"Don't worry Salman ya kaini Kai kuma ka kaita..." Hajiya ta shaida mashi, da sauri yayi mata kiss a goshi yana lumshe idanuwa. Itama kiss tayi mashi Sannan ta mike,
"Muje kaci abinci..." Hajiya ta fad'a Tana mikewa rike da hannunshi, Dan marairace fuska yayi Sannan yace
"Mommy am ashame su ganni haka..." Bai karasa ba hajiya tace
"Forget about them my Prince Charming...taso muje....ko in goyaka?..." Tafad'a cikin zolaya, mikewa yayi yana murmushi.