← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 190

Sashe 154

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaman zai tashi sama ya shiga bath din hajiya, ko masu aiki dake gaidashi bai kalla ba Don rabon dayaji shi so angry kaman haka har ya mance, hajiya kadai tanason ta watsa mashi komai, yasan it's not a small privilege samun irin Maryama shugaba a family amma hajiya kadai wants to ruin everything for him, he has given her so much chance that she has taken him for granted, yana hawan sama yana gudu, da karfi ya bude Kofar dakin hajiya dake zaune tana waya tayi saurin mikewa saboda yanda akayi banging Kofar,
"Alhaji..." Hannu alhaji ya daga mata tare dacewa
"Keep quiet..." Ya fada mata atakaice Sannan ya shigo dakin, kallon shi ta tsaya yayi Don tunda suke tare bata taba ganinshi haka ba, juyawa yayi ya kalleta from head to toe Sannan yace
"Sumayya yau ki zuba ruwa kasa ki sha...you have succeeded in separating your  son with the love of his life...aliyu zata aura..." Ya fada afusace, itama kallon up Anddown  tayi mashi Sannan tace
"Ayiiiirrrr..." Bata karasa ba taji saukar Mari, idanuwa ta zaro not believing yau ita alhaji ya Mara,
"Alhaji..."
"Keep quiet..." Ya daka mata tsawa, da sauri tayi shuru hawaye na taruwa idonta,
"What sort of a mother are you?... Suhail yana yi maki biyayya fiye da ya da yake mani...but I never turn back on what ever he wants...how could you be this heartless..." Ya fada cikin ihu, hajiya sai ja baya take saboda yan da alhaji ke magana kaman zai haukace,
"Wallahi ...Wallahi...Wallahi..if anything happens to suhail as a result of rabuwar shi da Fatima Wallahi bayan sakinki da zanyi sai na nuna maki shuru shuru ba wasa bane...i will handle you in such a way you will never forget..." Ya fada ya juya a fusace zai bar dakin, da sauri hajiya tace
"Wai alhaji are alright?... The last time I check ni na durkusa na haifi suhail...and I have absolute control over what he will do...wai what's so special about that stupid slimy slut...yarinyar da bata da class bata da manner...Kai amma gaskiya banji dadi ba da aliyu zai aureta Don shima Dan gidan girma né...Allah dai ya sauwakedana ya rabu da Allah kakai..." Afusace alhaji ya juyo yana cewa
"So you're still talking..." Ya fAda yana nufota, da sauri ta shige bathroom Tana cewa
"Yes na fada...Wallahi in sai ni na haifi suhail bazai taba auren wannan muguwar, mayyar yarinyar ba...yarinyar da ta kashe farin cikin zuciya ta?... I hate her with passion..." Ta fada Tana mazurai nan cikin bathroom din, da karfi alhaji ya bugi Kofar Sannan yace
"Wannan is your problem..nidai na fada maki in har wani Abu ya samu only son Dina because of your stupid and selfish attitude Wallahi bayan rabuwa na har Abadan da zanyi dake sai na lalata maki  rayuwa..." Yafada yana dukan Kofar sounding so tensed, dariyar rainin hankali hajiya tayi a inda take tsaye tace
"Kanka dai akeji..." Tafada mashi, laughing amma hawaye na fita daga idanuwanta, zama tayi nan cikin bathroom din Tana kuka Jin alhaji ya fita,
"Wallahi sai da kaga laifina amma ba zai yu Dana kwara daya tilo ya auri wacce tayi sanadiyar bakin cikina ba...wacce tasa kayi min kishiya...,wacce sanadiyar ta ka tsinke daya daga cikin igiyan aurenmu....Wallahi ba zai yu ba..." Ta fada crying loudly,
"Kuma nasan babu abinda zai samu Dana sai alkhairi..." Ta fada still crying,
"Babu abinda zai biyo bayan rabuwa da wannan joy killer din sai alkhairi...Ina zaman zama na an kawo wacce ta lalata farin cikina kuma you people are expecting me to take her in as a daughter in law...bazai yu ba...not while am breathing,..never..." Tafada cikin matsanacin kuka, Yanzu wata uku kenan da bata gan suhail ko ji daga gareshi ba amma she don't care because she wants him to learn a lesson, she wants him to understand babu abinda zai sa ta amince da wannan yarinyar as her only daughter inlw.p, the breeder of her grandchildren, kuka ta zauna nan ta sha kaman ranta zai fita Sannan ta watsawa kanta ruwa ta dawo bedroom ta kwanta Tana zage zage,
Maryam na gama waya da dad dinta ta kwanta nan Tana hawaye, kawai bata San abinda ke mata dadi ba, she feels so awkward and restless, aliyu né ya fado mata sai taje tunanin ya amince amma bai kirata ba, he didn't tell her anything, waya ta dauka zata kirashi sai kuma ta ajiye, sake daukan wayar tayi wannan Karin tayi dailing number suhail amma sai taji kashe, ajiye wayar tayi ta fita falo inda duk yawanci family din alhaji Dana salima me suka hadu Ana ta shirye shiryen suna, abinka da family daya, cikin mutane ta bi ta shiga dakin salima looking so weak, mikewa salima dake zaune cikin yan uwa tayi ta Kama hannun Maryam Tana cewa
"Meke damunki kuma?..."Ta tambayeta,
"Ba komai...kawai inason ganin namesake né..." Ta fada cikin sanyinmurya,
" naji...muje in baki abinci...Don na lura kwanan nan in ba tsayawa nayi kanki ba baki cin komai..duk kin rame Wallahi...gaskiya ni banajin dadin hakan..." Ta fada Tana rike da hannunta zuwa kitchen, plate ta dauka ta debo naman kauri sai kuma ta hada mata tea Mai kauri Sannan tace
"Muje dakinki..." Ta fada mata,
"Anty ki rage naman nan...I can't eat half..." Salima bata Bari ta karasa ba tace
"Nidai muje..." Ta fada mata Tana rike da plate da cup din, Maryam bata Kara cewa komai ba ta shige mata taba har bedroom dinta, ajiye mata tayi Sannan ta zauna gabanta tare dacewa
"Bisimillah..." Ta umarceta, ba musu ta zauna ta fara cin Naman Tana kurbawa da tea, Tana ci Tana bata face alaman she don't want to eat anymore amma data kalli face din salima sai kuma ta cigaba daci, ahaka ta cinye most of the meat Sannan ta turasu gefe,
"Yauwa my daughter...ko ke fa..." Salima ta fada sounding excited,
"Anty..." Maryam ta Kira mata
"Naam..." Salima ta amsa Tana kallon ta, gani tayi idanuwanta sun ciko da hawaye,
"anty daddy na yace...cikin gaggawa zaayi komai..." Tafada hawaye na gangarowa daga idanuwanta, tagumi salima tayi Tana kallon ta,
"Anty nasan dad Dina ya kusa zuwa...kuma ba lallai suhail ya dawo kafin lokacin ba...." Tafada Tana shessheka alaman tayi kukan da yawa,
"Anty...dad yace maiduguri za'a komai...zan bar gidan nan in har ya dawo...zai maidani maiduguri..." Tafada kanta kasa sai hawaye kawai Ke fita,
"Anty Dan Allah ki bani izinin zuwa Dubai...ko sau daya né in ga suhail kafin in bar gidan  nan..."Ta fada mata, yanda take magana yasa salima fashewa da kuka,
"Na shiga uku...wannan wane irin jarabawa né....ya Allah ga bayin ka..." Salima ta fada Tana hawaye, da sauri Maryam ta girgiza mata Kai Tana cewa
"Pls anty don't cry....banason a nuna min tausayi...I hate self pity...pls just permit me in je ganin suhail....Wallahi anty in har na bar gidan nan ba gan suhail ba mutuwa zanyi....kawai Ina kokari né saboda kullum Ina tunanin zai dawo in ganshi...amma Yanzu komai ya Chanza..." Kuka né yaci karfinta tayi shuru, salima dai bata daina hawaye ba duk ji tayi Inama da akwai Abunda zatayi iya yiwa wannan yaran da babu Wanda yaisa ya hanata hadasu aure,
"Anty Dan Allah ki amince inje ganinshi kafin ayi auren nan..." Tafada mata, ahankali Salima ta daga wet face dinta ta kalleta Sannan tace
"Hakan ba Mai yuwa bane....hakan ya sabawa addini....kiyi hakuri...irin taku jarabawan kenan..." Salima ta fada crying, ahankali Maryam ta girgiza mata Kai Tana cewa
"Wannan ba jarabawa bane...wannan balai né Wanda zaiyi sanadiyar mutuwata...kilan shi suhail ya samu wata amma ni zuciya ta na tare da suhail..."
"Kiyi hakuri...kar ki je...nasan in har kika yi aure mantawa zakiyi dashi..." Bata karasa ba Maryam tace
"Anty da suhail din zan manta?... Wallahi billahi ban iya manta suhail ko duk duniya zasu taru Kaina....nidai anty zan je Dubai...Dan Allah amincewan ki kawai nake jira..,banason in bijire maki..." Maryam ta fada mata cikin matsanacin kuka, kusa daita salima ta dawo ta jawota jikinta Tana cewa
"Hakan ba daidai bane...Yanzu zaki auri abokinshi Sannan kuma ki Kara Kai kanki gareshi?... Kawai ki yi hakuri ki rungumi kaddara...kinga in kinje ya nuna baki da aji..."
"anty naji bani da ajin...bana son ajin...nasan Kaina...I have nothing to prove to anybody except myself...."
"Naji..." Salima ta fada Tana Shafa kanta,
"Kawai kiyi hakuri...Dan Allah...in kika je komai na na iya faruwa....kawai ki danne zuciyar ki kaman yanda kikayi abaya...kinji kou?..." Salima ta fada cikin rarrashinta,
"Nidai anty Yanzu na kasa dannewa...kawai ban iya dannewa...banason ace baki San inda naje ba...kuma banason bijire maki...amma sai naje Dubai...Wallahi anty sai naje..." Ta fada cikin kuka
"In har kinason Kare martabar mahaifinki kar kije....kiyiwa Allah da manzonsa kar kije...Dan Allah ki rufemin asiri...ke amana ce wajena kuma bazan saka Ido kiyi irin wannan mistakes din ba....kiyi hakuri Dan Allah...Allah na ganin abinda ke faruwa Sannan shi ba azzalumin sarki bane...wata rana komai zai zamo alkhairi..." Salima ta fada mata cikin sanyinmurya, kuka Maryam ta farayi da karfi Tana dirza legs dinta kasa Tana cewa
"Wayyo anty Allah yaisa tsananina da Maman suhail....Allah ka saka min..,,ban yafe mata ba...ta cuceni...ta lalatamin farin cikina..." Da sauri Salima ta dora hannu kan lips dinta Tana cewa
"Shuuusshh...kiyi shuru kar ki sake furta irin wannan kalaman...ita ta haifi danta Tana da iko dashi..tunda danta yayi mata biyayya kema kiyi kokarin Kare martabar ki...kiyi hakuri kinji kou..nasan abinda kike ji...wani lokacin Abu kakeso saye in Baka da halinshi sai kaji babu dadi balle mutum?... " Salima ta fada mata, Maryam Dora kanta tayi kan cinya Salima ta dinga kuka, salima sai Shafa bayanta take itama gama hawaye, tun kuka marn a fita sai ya kasance muryar ta bai fita sai dai hawaye, idanuwanta duk sunyi kumbura sunyi ja, cikin kuka bacci ya dauketa.
Chapter 154 · 0% Book details