← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 190

Sashe 35

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 7 min read

Hajiya na nan kasa zaune inda alhaji ya barta taci kuka ta koshi har idanuwanta basu buduwa sosai saboda kuka, ta nan har bacci ya dauketa bata sani ba Don yanda taga rana haka taga dare.  Bayan baba rabi ta gama shirya Kayan ta cikin bag su murja suka Kama suka saka bayan motar da alhaji ya zo daita, ita kuma Maryam Tana zaune bakin gadon sai hawaye take at the same time bata kaiwa minti biyu bata firgita ba saboda trauma. Bayan an saka Kaya mota alhaji yasa baba rabi ya kirata su tafi, Tana tafiya kaman kazar da aka tsoma aruwa ta tsakar gidan, duk ilahirin jikinta babu abinda yake sai azaba Don ji take kaman an shafawa dukkan ilahirin jikinta pepper. Salman dake zaune yayi saurin daga Kai ya kalleta lokacin da tazo shiga mota, itama daga idanuwa tayi ta sakar mashi murmushin karfin Hali, shi kam kallon ta kawai yake yana tausayi mata Don duk Wanda ya ganta yasan Tana cikin yanayi, yaso ya daga mata hannu amma alhaji yana zaune cikin mota kuma kaman shi yake kallo, sadda Kai kasa yayi itama kuma ta shige cikin motar. Alhaji yaja suka bar gidan.   Akan hanya alhaji ya tsaya ya sayi drugs dinta da wasu abubuwan da yasan zasu bukata cikin gaggawa Sannan suka wuce, suna Isa wannan gidan da suka tab'a zama lokacin da ya fara kawota suka shiga ciki, Mai gadin gidan ya sauko da Kaya ya kaisu ciki, Maryam sai lumshe swollen and tired eyes dinta kawai take. Suna shiga falo alhaji da kanshi ya b'allo magani ya bata tare da ruwa,  amsa tayi Tasha Tana bata fuska,
"Ki hada mata ruwan wanka Mai dumi" inji alhaji, da sauri baba rabi ta shiga ciki shi kuma ya mike yana cewa
"Daughter Bari in tafi...in sa Salman ya kawo maku abinci...zaki zauna nan har new mother dinki ta zo..." Cikin kasala ta daga mashi kai, cheeks dinta ya Kama Sannan yace
"Ki kasa jikinki da kyau ...kinji kou?.." Still Kai ta daga mashi, murmushi ya sakar mata itama ta maida mashi Sannan ya tafi, relaxing tayi Tana tunanin if she can forgive and forget this, da Tana tsoron suhail amma Yanzu tafi tsoron hajiya, abun da ke bata mamaki shine yanda bata San laifinta ba kawai sai duka, hawaye né ya Kara gangarowa daga idanuwanta, gani take da kyau zata iya kwanciya Don tamkar an sokawa skin dinta k'aya haka takeji,
"Taso kiyi wankan..." Baba rabi ta fada mata, ahankali ta mike Tana goge fuskarta,
"Kiyi hakuri Fatima...wallahi Allah kadai yasan dalilin jarabawan nan da kike fuskanta...amma Dan Allah me kikayi mata?." Inji baba rabi, ahankali tace
"Baiyi ...mata....komai ba..." Tafada muryar ta na cracking,
"Oh ni rabi...wato haka nan taso kasheki...Allah ya taimaka suhail yazo da Allah kadai yasan abinda zatayi maki kafin alhaji ya iso..." Baba rabi ta fada mata, Dan kallon ta Maryam tayi Sannan tace
"Ban...gane..ba..." Maryam ta fad'a mata,
"Hmmm yar nan yau naga abun mamaki....wato kuka suhail ya dingayi yana rike dake..." Wannan statement din yasa Maryam Chanza yanayin fuskarta zuwa yanayi Mara fassaruwa,
"Shi ya kwace ki daga hannunta...wallahi ni ban San wannan yaron na da digon Imani ba sai yau...ya bamu mamaki..." Baba rabi tacigaba da fad'a mata, ahankali Maryam ta tabe baki tare dacewa
"Hmmm..." Don ko a mafarki tasan hakan ba Mai faruwa bane, bata Kara cewa komai ba ta shiga bathroom. Tana wanka Tana kuka Don duk inda ta zuba ruwa sai tace washh saboda azaba. A daddafe ta gama ta fito daure da towel. Bata tsaya koina ba sai bedroom din da ta zauna lokacin da aka fara kawota gidan. Kwantawa tayi bayan kaman minti biyar bacci ya dauketa.

Daga hospital suhail bai dawo gida ba, gidan su Yusuf ya wuce, bai shiga part din iyayen ba ya tsaya a part din Yusuf, shima kwanciya yayi amma ko kadan bacci baiyi gigin daukar shi ba, tunanin Maryam kawai yake, har lokacin sallar zuhr bai sake cin komai apart from Dan tea daya kurba a office din sadeeq ba, da kyar ya samu yayi sallah nan cikin dakin ya koma ya kwanta tare da hugging pillow sai lokacin bacci yayi baba dashi. 

The next day

Duk Wanda yasan hajiya in ya ganta karya yake yace zai ganeta Don yayin ta ya sauya fiye da tunanin Mai karatu, tayi baki ta rame ta fita hayyacinta, lokaci daya abubuwa suka juya mata baya, ga alhaji yace ya saketa, ga kishiya sannan ga suhail bai ko piçking call dinta Don dukda halin da take ciki batason bacin ran suhail dinta, she was thinking zai bata hundred percent goyon baya, baisan ranshi zai bace to such an extent ba. Tun lokacin da alhaji yayi mata kishiya bata ko Kara Shan ruwa ba balle abinci and the most annoying part babu Mai rarrashinta Don duk yanda take fushi suhail yana satata sauko har tayi dariya amma gashi Yanzu babu shi
"Wannan yarinyar ta watsa min kan gida....she has kill my joy and happiness...she has ruin everything for me...wallahi sai naga bayanki..." Ta fada cikin muryar da in ba kasa kunne kayi sosai ba bazaka ji ba. Kofa ta bude Don tun lokacin bata bude kofa ba balle ta fita, ahankali ta taka stairs, tsayawa tayi a na uku Tana kokarin kiran masu aiki amma babu Mai jinta saboda muryar ta bai fita, Ida sauka tayi ta shiga kitchen taga babu kowa, baki ta tabe ta hadawa kanta tea sannan ta koma upstairs.

Shi kam alhaji bai Kara bin ta kan hajiya ba yacigaba da harkokinshi Don yana komawa office bayan ya ajiye Maryam ya Kira wani contractor, nan ya fada mashi yana son a gyara mashi 3 bedroom apartment dake nan cikin gidanshi, a maida Mai shi tamkar sabuwa, nan sukayi estimates na aikin. Don haka gari na wayewa suka zo suka fara aikinsu cikin gidan. 

a bangaren suhail gidan su Yusuf ya kwana, amma ko word daya bai hadashi dashi ba har garin Allah ya waye, baici baisha, Yusuf yayi yayi har ya gaji kan yaci abinci amma ko daga Kai baiyi balle ya amsa mashi, haka Yusuf ya hakura ya kyale shi, gari na wayewa am aka kawo breakfast still baici ba, wayanshi bai minti goma batayi ringing ba amma ko kallon wayar baiyi balle ya amsa, Yusuf dai gajiya yayi ya shirya ya tafi office.
Wajen Karfe biyu yaji ya kamata yaga Maryam Don baisan halin da take ciki Yanzu ba, kuma tamkar ya shekara bai ganta ba yake ji, ahankali ya fita daga dakin ya fito ya nufi wajen motar shi, gani yayi yana gani double, dole yasa ya Kira maigadi ya shaida mashi ya samo mashi adaidaita Don Sam bai iya tuki sannan hannunshi nayi mashi wani irin zafi. Da sauri Mai gadin ya fita shi kuma ya taka ahankali ya koma wajen zaman maigadi ya zauna kanshi kasa. Bayan minti goma maigadi ya dawo tare da Mai adaidaita, mikewa yayi ya shiga tare da relaxing ya fada mashi inda  za'a kaishi.

Yana Isa gidansu ya ga Ana ta aiki a abandoned three bedroom flat dake gefe daya na gidan, baki ya tabe ya wuce part din hajiya, yana shiga ya Nufi dakin Maryam gabanshi na faduwa saboda yanayin da ya barta jiya, to his surprise yana bude kofa yaga dakin wayam, tsaya dube2 yayi Don ya tabbatar if she's around amma sai yaga babu komai nata, idanuwa ya zaro ya fita daga dakin  da sauran kuzarin shi, dakin su murja ya bude da karfi har suna firgita, fuska daure yace
"Ina Fatima..."  Ya tambayesu Kai tsaye, murya murja na rawa tace
"sun tafi..." Kara daure fuska suhail yayi yana cewa
"Sun tafi Ina Dan ubanki.." Ya daka mata tsawa amma deep down he knows mommy ta gama dashi,
"Da alhaji..bamu San inda suka tafi ba..."  Ta sake amsa mashi, afusace ya juya yana cewa
"Mommy kin kashe ni...kawai yau u must kill me...Allah sai kin kashe ni..." Ya fada yana Kama hanyar kitchen, yana shiga ciki ya dauko wuka ya Kama hanyan upstairs.
[11/28, 3:19 AM] ‪+234 706 639 9737‬: 15💛💙💚❤️💜
Wulakanci dodone
❤️💜💙💚💛

® zuwairat (ummumaryam)

1️⃣5️⃣
Chapter 35 · 0% Book details