← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 177 OF 190

Sashe 177

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 3 min read

dining suka zauna duk suka ci abinci har da sisters din suhail, kiran dad né ya shigo yana fadawa suhail su shirya ana jiransu airport, suhail kallon Maryam da ko spoon uku batayi ba yayi yace "Ana jiran mu..." Yafada mata, kaman Tana jira ta ajiye spoon din ta Mike ahankali, kanta kasa ko sau daya bata daga Kai ta kalli kowa ba har shi suhail din, upstairs ta hau ta dauki white vail cikin kayanta ta Dora kan red gown dake jikinta Sannan ta sauko Tana jan wata katuwar bag while Tana rike da karamin da hajiya habiba tayi mata huduba Kai, suhail na ganinta yayi saurin mikewa ya amshi both bags daga hannunta, har lokacin bata kalleshi ba, he's feeling something is wrong with her or she's shy, Tana fita ta shiga dakin masu aiki ta yi masu bankwana har da rungume hajiya baba rabi itama baba rabi ta Kara yi mata godiya saboda tasan itace sanadin zuwanta saudiya, fitowa tayi hajiya na rike da hannunta har compound, part din salima ta shiga sai ta fashe da kuka, nan Salima ta dinga rarrashinta, kallon baby Maryam dake giggling tayi tace "Anty...in tayi girma zan dauketa..." Ta fada cikin hawaye, suhail né yayi sallama ya shigo ya tardata Tana kuka, "Wai anty meke damunta né?... Ni Wallahi na kasa gane kanta....she looks dull..." Ya fada sounding disturbed, "Ai amarya ce...dole sai ta yi shagwaba..." Ta fada mashi, zama sukayi itama ta Kara basu nata shawarar Sannan suka fita zuwa part din alhaji, hannunshi rike da hannun Maryam ya bata nashi shawarar kaman dad dinta tare da saka masu albarka suka fita, already an gama saka Kayan su bayan booth, bayan mota suka shiga hajiya da sauran mutanen gida na weaving dinsu goodbye, Maryam dake zaune gefe daya suhail ya kalla, duk face dinta babu walwala kaman yanda ya Santa Sannan duk ta susuce for no good reason, jawota yayi jikinshi yana tambayan ta abinda ke damunta amma sai tace she's having headache, bai ga tashin hankali ba sai da sukaje yiwa alhaji Mahmoud bankwana a estate dinshi Maryam ta dinga kuka kaman da akwai abinda yayi mata, sai ya dinga aduar kar ayi tunanin something happened last night, zaunar dasu alhaji Mahmoud yayi ya basu shawara sosai inda ya nuna masu dole su hada Kai saboda su zasuyi inheriting duk Abunda ya mallaka a rayuwa, da kyar Maryam ta yarda aka kaisu airport, suna shiga jet Tana kuka kaman ranta sai fita, sai da suka shiga suhail yaje wajen da take zaune yace "Wai baby is there anything I don't know?.." Ya tambayeta face dinshi kaman bai taba dariya ba, banza tayi dashi tacigaba da kuka abinta.
Chapter 177 · 0% Book details