← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 190

Sashe 103

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 5 min read

Inji suhail, dadi salima taji saboda yanda yake girmama ta Yanzu, "Ba komai..me kuke shaawan ci?.." Salima ta tambayeshi, "Ai anty anything is ok.....kawai in an gama a kiramu sai mu zo nan muci..." Suhail ya amsa mata. Bayan sun gama Shan drinks din suka mike, har bakin kofa Maryam ta rako aliyu sannan ta koma ciki, "Kam kuma drama...ni kam am wondering ya zata Kaya in tasan kaine Mai kiranta..." Inji sadeeq, "Ni kuma gani nake kaman she loves him kawai attitude dinshi né bataso"Inji Yusuf "Nidai ku tayani adua...Allah gabana faduwa yake..." Inji suhail, part dinshi suka Koma suka Fiddo bag da ya dawo da ita duk suka hau Jan Kayan kaman Kayan kwanjo, har shoes da perfumes sai da kowa ya dauki rabonshi, zama suhail yayi yana kallon su Don shi abinda ke damunshi daman Sannan yasan Kaya bazasu zama matsala ba, sai da suka gama kowa ya nustu suka kalli suhail daya rafkatagumi "Why meye ke damunka né?.." Sadeeq ya tambayeshi, Dan ajiyan zuciya suhail ya saki Sannan yace "Ni Abu biyu kawai ke damuna duk duniya..nafarko haduwan mu da Fatima Sannan na biyu..." Sai ya basu labarin abinda ya faru tsakanin shi da Salman ya Kara da cewa "Kuma gashi in two days zan bar kasar..." Ya karasa maganar cikin sanyinmurya, wani irin zagi aliyu ya saki Sannan yace "Wallahi yanda ni aliyu hydar na hakura da Fatima dole kowanne shege ya bar maka Wallahi..ba'a wani banufe da zai ja damu a cikin garin Kano ba Wallahi...kuma in mutum yaki ji sai in sa ayi mashi wanka da acid..." Ya fada kaman wani Dan daba, dariya sukayi duka har da suhail "Easy mana..." Inji Yusuf, harara aliyu ya balla mashi sannan yace "Dalla chan babu wani easy...kasan Wallahi inason wannan yarinyar na hakura saboda suhail Don haka ba'a haifi wani shege da zai katse mu kanta ba..." Ya fadawa Yusuf Sannan ya kalli suhail yace "Wallahi guy ka kwantar da hankalinka...babu wani shege kaji kou..." Ya fada kaman yasha wani Abu, dariya sadeeq yayi Sannan yace "Kodai matar daddy ta saka maka wani Abu cikin drink Don you sound scary.." Inji sadeeq, idanuwa aliyu ya lumshe yace "Kawai bazaku gane bane..." Yafada yana Shafa face dinshi. Hira sukayi har lokacin sallah magrub sukaje sukayi Sannan aka Kira su Suzo dinner, kan dining daya suka zauna har da salima da Maryam, suna cikin cin abinci suhail ya dauki waya yayi rubuta I love you ya tura mata, Jin wayar yayi Kara yasa ta Kira Baraka ta dauko mata, Tana dubawa ya saki murmushi tare da replying I love you too ta tura mashi, duk yana kallon ta, ita kam batasan da zamanshi ba nan wajen ba. Daga nan sukayi sallah ishai Sannan suka tafi. Wannan dare Maryam da suhail basuyi bacci ba har kusan Karfe uku na safe saboda waya, the following day bai good one hour sai ya tura mata I love you saboda gani yake kaman soon all this will stop if ta gane shine. Yau Monday, suhail ya tsinci kanshi cikin tsananin fargaba haka nan gabanshi ke mugun faduwa, kawai ji yake kaman ya ce mata su bar haduwan sai some other time amma yasan dole the day will come so he feels it's better to get it over with. Itama Maryam haka nan she's scared for no good reason tunda har fada mashi tayi she's scared shima ya amsa mata da so am I. Shirin islamiyya tayi ta fito ta sha tea kadai shima Dan kadan ta tambayi salima ta bata 1k, salima bata nemi Jin abinda zatayi dashi ba ta bata. Cikin bag da Quran dinta ke ciki ta saka ta fito, shi kam suhail ko ruwa kasa sha yayi ya fito ya zauna cikin mota yana jiran ta fito ya kaita islamiyya, yana hangota yayi saurin fitowa ya bude mata gidan gaba, wani irin harara ta watsa mashi ta bude baya ta shige abinta, bai ce komai ba ya shiga ya ja suka bar gidan. Gaban islamiyya ya tsaya ta sauka Tana tafiya cikin kasaita, kallon ta ya dinga yi har ta shige, "Ya rabbi if she becomes my I will be greatful for the rest of my entire life " ya fada yana komawa gida, jiki ba kwari ya shiga falon shi ya kwanta kan kujera sai sauke ajiyan zuciya yake hannunshi biyu kan face up dinshi, sai sauke nishi kawai yake kaman Wanda, yafi hour nan kwance babu abinda yake sai aduar nasara, sai wajen 11 ya shiga wanka ya fito ya shirya cikin farar shadda da black cap my kyau da tsada, fitowa yayi ya nufi Inda motarshi take, shiga yayi ya dauki waya yayi mata text kaman "Baby am heading for the Bristol...da kin isa you call me.." Ya tura mata Sannan ya fito, duk Wanda ya ganshi yasan a tsorace yake, sadeeq da sauran friends sai Kira suke in sun hadu ya shaida masu sai 12 suke tashi daga islamiyya. Yana zuwa wajen ya wuce bakin pool ya zauna kan kujerun da ke wajen. Itama Maryam Tana tashi daga islamiyya ta Kira suhail ta shaida mashi ta tashi, suna ciki waya ta tsaida adaidata ta bawa Mai keke waya suhail ya fada mashi inda zai kawota Sannan Ta shiga, 12:30 ta iso wajen, kiran shi tayi yace ta shigo ciki, this time bai makale voice ba ya fada mata in his normal voice, shuru tayi Tana sauraron voice din, ahankali ta shigo tabi inda ya kwatanta mata, daga Dan nesa ta hangi bayan mutum zaune da white shadda, number tayi daiiling taga yayi piçking nan take tambayan shi if he's the one with white shadda ya amsa mata da eh, ahankali ta taka tazo wajen ta zauna zauna opposite to him, suhail daga weak eyes dinshi yayi itama ta daga nata ta zuba cikin nashi, da sauri ta mike har Tana kokarin faduwa Saboda tsoro.
Chapter 103 · 0% Book details