← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 190

Sashe 39

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 3 min read

Bangaren suhail karfen goma na dare yaji hannunshi ya hanashi sukuni saboda azaba, ahankali ya shiga bathroom ya hada heater, bayan kaman minti goma ya hada hot water ya saka towel dinshi a ciki ya matse ya dora kan ciwon, ahankali ya saki Dan Kara tare da biting lips dinshi, yafi minti biyar yana gasa hannun sannan ya koma bedroom dinshi, system dinshi ya dauka ya saka wakar the one na Rick Ross yayi relaxing yana ji yana sauke ajiya zuciya, he's feeling so bored, babu abinda ke yi mashi dadi, kawai dai gashi nan, he wish yana iya komawa normal life dinshi when he cares about nobody except his mother,  Amman Yanzu a girl from nowhere is ruining his perfect little life. Bai samu bacci ba sai kusan 1am. Da asuba ya mike yayi wanka ya fito sanye da pure white jallabiya adaidai lokacin shima dad ya fito daga part din hajiya, he was surprised
"Kun jone kenan..." Shine abinda ya fada cikin ranshi, tare sukaje suka dawo still bin alhaji suhail yayi ya sake maganar Maryam amma bai barshi ya karasa ba ya mike ya barshi nan zaune, zama suhail yayi yana cika kaman zai fashe saboda bakin ciki, mikewa yayi ya shiga part din mommy shi, Tana zaune kan praying mat, Tana ganinshi tayi sauri mika mashi hannu amma. Sai bai amshi hannunta ba ya samu kujera ya zauna tare da gaidata da Jin yanda ta kwana, bayan nan yace
"Yanzu mum bazaki tausaya min a nemamin auren Fatima ba?... Wallahi mommy mutuwa zanyi...am dying inside,,,ko sai kunga na mutu hankalinku zai kwanta?.." Ya karasa maganar sounding so fed up, kallon shi kawai hajiya take Tana kallon yanda yake magana ciki class da kasaita and she can be happier she's a mother to this handsome guy, mikewa tayi daga kan praying mat ta koma kusa dashi ta tallabo face dis hi tare dacewa
"Baby babu abinda zai sameka sai alkhairi..." Bata idaba ya mike yana cewa
"Stop saying that mom.. Wane irin babu abinda zai sameni sai akhairi...mommy am dying..bana samun bacci..I don't eat...kullum my heart feels wounded..and sai kice babu abinda zai sameni sai alkhairi...wallahi mutuwa zanyi mommy...pls ki fadawa dad ya fada maki Inda take..pls mommy..." Ya fada kaman zai fashe da kuka, ahankali hajiya ta mike ta dafa shoulder dinshi,
"Don't worry..zan tambayi dad Dinka inda take...so ka kwantar da hankalinka..." Hajiya ta fada mashi in calm Manner, da sauri ya juyo ya rungume ta tare da jera mata kisses a goshi yana cewa I love you mommy.
Tare sukayi breakfast inda ya danci abinci amma ba sosai ba shima saida hajiya tayi feeding dinshi. Bayan sun gama ya koma part dinshi ya kwanta feeling a little bit relieved.

Itama Maryam yau she's feeling better kan jiya din wannan sourness ya ragu sosai, taci abinci ba laifi sannan she's feeling happy Don Yanzu hankalinta kwance no nagging, ba zagi sannan babu takura kuma babu fargaba Don ganin suhail da uwarshi na mugun tada mata hankali,
"Especially him..." Ta fada cikin  sanyinmurya, Kai baba rabi ta daga Ta kalleta tare dacewa
"Me kika ce?.." Ta tambayeta, ahankali ta girgiza mata Kai Tana cewa
"Ba komai..." Ta amsa mata.
Chapter 39 · 0% Book details