← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 190

Sashe 54

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 8 min read

Suhail kam yana ajiye mom dinshi bai rakata kaman yanda ya Saba din Tana fita daga cikin motar ya ja ya Kama hanyar gida, kawai he's eager yazo gida yayi waya da Maryam Don su dasa daga inda suka tsaya, yana dab da shiga area dinsu ya hangi motar dad dinshi daga nesa, mamaki né yake Don yasan he left him a da safe' yana Kara zuwa kusa ya gane Salman né dauke da Maryam. Tun kan ya karasa inda suke ya fara horn yanayiwa Salman alaman ya tsaya, babu musu Salman ya koma gefe yayi parking, harara Maryam ta b'alla mashi sannan tace
"Pls lets go am running late..." Ta fada Tana turo baki, bai amsa ba yayi zaune cikin motan, suhail né ya koma gefen titi yana gyaran belt din wandon shi da alaman it's not tight, daga nesa Maryam ta watsa mashi kallon haushi da tsana ta kauda kanta gefe gud'a tare da Jan tsoki, yana karasowa ya kalli Salman da ya kauda Kai gefe gud'a ya saki tsoki sannan ya kalli Maryam, itama head dinta gefe gud'a not looking at him, hannu yasa ya bude motar Sannan yace
"Come let me drop you..." Ya fada sounding calm, tunda Maryam take bata tabi ji yayi magana ahankali ba sai yau, still bata kalleshi ba ta kalli Salman before saying
"Allah am running out of time...nidai mu tafi..." Ta fada kaman babu kowa wajen, maganar ta batawa suhail rai yayi Don har zai bude baki yayi magana sai yaji Salman na cewa
"Ni office zan koma...kije ya kaiki...", idanuwa suhail ya lumshe Don farat sauya sai yaji duk haushin Salman dayakeji ya gushe,
"Nidai Kai zaka kaini..." Ta fada kaman zatayi kuka,
"Pls ki fita alhaji yana jirana..." Inji Salman, suhail juyawa yayi ya taka with his white feet ciki black palm sandals. Wurin motar shi koma, itama Maryam kaman zata tashi sama ta fito daga cikin motan ta nufi motar suhail, suhail juyowa yayi ya kalleta yaga ta hada girar sama d'ana kasa, shima daure fuska yayi Don Yanzu gani yake ta gane yana sonta shiyasa take néman rainashi,shigewa mota yayi, Maryam na zuwa ta bude bayan mota ta shiga, shikam Salman bai tsaya ganin abinda zai biyo baya ba ya ja Mota ya bar wajen.
Haushi suhail ya karaji, zai bude baki yayi magana sai kuma ya fasa, fita yayi daga cikin motar ya bude baya ya fixgota daga cikin motar ya bude gidan gaba ya wulla ta ciki kaman wata doll ya shiga ya juya kan motar, Maryam sai sauke ajiyan zuciya kawai take saboda haushi da nakinciki, sai da ya fita unguwar su ya kalleta tare dacewa
"Inane islamiyyar ku?.." Ya tambayeta kaman baison magana, tanayi tayi banza dashi, shuru yayi ya bai Kara cewa komai ba ya hau titi ya dinga tafiya, Maryam Tana kallo ya wuce islamiyyar amma batace komai ba saboda haushi, yafi minti talatin yana tuki sannan ya kalleta ya sake cewa
"Ina islamiyyar ku.." Ya sake tambayan Kaman baisan ya wuce ba,
"Yana baya..," Ta fada atakaice, yana tuki da hannu daya ya daga daya hannunshi ya Kama kunnenta,
"Am I your mate?.." Shine tambayar dayayi mata yana Jan kunnenta while driving, Tana yarfa hannuwa tace
"Aa..." Ta fada Tana kokarin kuka,
"Then why kikeson Mai Dani mate dinki...wallahi na Kara yi maki magana babu response sai na cire maki kunne...am I clear" ya daka mata tsawa, da sauri ta daga mashi Kai, sai lokacin ya saki kunnenta ya juya kan motar, Maryam fashewa tayi da kuka tare da Kama kunnenta Tana takawa Don ta tabbatar if it's still there. Hada Kai tayi da gwaiwa Tana kuka, kallon yayi sai yaji Sam he's not happy, ahankali ya daga hannunshi ya Dora bayanta in a comforting manner, da karfi Maryam ta daga hannu ta buge hannus aya bayanta, hannu ya Kara dagawa ya fallawa bayanta bugu ta Kara rushewa da kuka da karfi, tafi minti biyar Tana kuka sannan tayi shuru amma bata daga Kai ba, suhail najin tayi shuru yasa hannu yana kokarin daga kanta sai ta Kara fixgewa, hannu ya sake lafta mata a baya ta sake sakin Ihu, dariya suhail yayi Don ko kadan dukan wasn't hard amma yanda take Ihu tamkar an sa mata wuka,
"Uwar son jiki...Abu kadan sai kuka..indai nine sai kin cika buckd a hawaye..." Ya dada yana dariya, Kai Maryam ta daga ta watsa mashi harara, fingers dinshi biyu ya nufi eyes dinta dashi yana cew
"Kika Kara hararata sai na tsone maki idanuwa..." Ya dada yana kokarin tura fingers dinshi cikin idanuwa, da sauri ta kauda kanta tare da share hawayen face dinta, Jin tayi shuru yasa ya Kara daga hannu ya Dora kan shoulder dinta kaman Tana jira ta ture hannun da karfi, keyanta ya sake duka Ta sake fashewa da kuka this time Tana Kira daddy, dariya yayi yace
"Ke you're so funny..you're calling a dead man...." D sauri Maryam ta kalleshi sai lokacin ta tuna da abinda alhaji ya fadawa family dinshi. Atakaice kafin su sake Isa islamiyya sai da ta sha kuka ta koshi sannan' yana zuwa ya tsaya tare dacewa
"Get your skinny self out of my car..." Ya fada yana relaxing, budewa tayi ta fita tare da banging Kofan, dariya yayi yana cewa
"Ina nan zaki dawo ki sameni..." Ya fada yana dariya, banza tayi ta shige ciki islamiyyar. Agogon wayar shi ya kalla yaga 10 saura, Dan relaxing yayi din ya jiran su tashi.

Ganin har after 11 basu tashi ba yasa ya juya kan motar ya bar wajen, cikin gari ya shiga ya sayo snacks da Kayan lashe2 dukda baisan yanda zaiyi ya bata ba,
"Suffering for the girl da bata San wasa ball.ji yanda take kuka Don Ina mata wasa," ya fada yana komawa islamiyyar, yana dawowa Ana tadasu.

Aisha kallon Maryam tayi Tana mamakin dalilin dayasa Idanuwanta suka kumbura,
"Wai babe me ya sameki né?... Kin kwana biyu baki zo ba kuma yau da kika zo your eyes are swollen..." Aisha Ta tambayeta, shuru Maryam tayi Tana tafiya ahankali suna, Tana fita motan suhail tsaye, da sauri taja baya tare da komawa ciki, kalle2 Aisha tayi itama tabi bayanta Tana mamakin what she's afraid of
"Wai meye?.." Aisha Ta tambayeta, gefe daya ta samu ta zauna sannan ta bata labarin suhail da yanda yake treating dinta like trash, dariya Aisha tayi tare dacewa
"Amma kin bani mamaki... At this age kike wannan maganar...har a samu wani kato ya takura ki?.. Lallai ma...am disappointed in you..." Ta fada Tana dariya, daga idanuwa Maryam tayi ta kalleshi Sannan tace
'"Don't you get it...tsoro yake bani...wallahi the guy is mean...like demon mean...kuma gidansu né..." Bata idaba Aisha taja tsoki tare dacewa
"Kawai you're a weak..in ba haka ba sai Ki tsaya wani katon Allah taalah ya maida ki baiwa?...pls tashi mu tafi..." Aisha Ta fada Tana kaman hannunta, da sauri Maryam ta fixge Tana cewa
"Gaskiya am not following him home...zan zauna nan in ya tafi I will fine my way home..." Ta fada mata atakaice, shuru Aisha tayi Tana kallon ta,
"Ki tafi kawai..." Maryam ta fada mata,
"Nope..ki tashi mu tafi...driver na ya ajiyeki gida...there's no way am leaving you behind..." Aisha Ta fada mata, ahankali Maryam ta mike suka Kama hanyar waje.
Suhail kam har ya gaji da tsayuwa Don yana ganin an fara fitowa him a ya fito ya tsaya Yana jiran ya hango ta ta fito amma sai ya ga almost duk mutane sun tafi bata fito ba, hannu Asa cikin aljihunshi looking restless, har zai dauki step zuwa cikin islamiyyar sai gata da wata yarinya, daure fuska yayi ya koma cikin mota yana jiran ta ta shigo, Dan juyawa yayi yaga yard a suke tare da kuma yanda take Shan kamshi, tsoki yaja tare dacewa
"Idiot..." Yana jiranta ta shiga sai yaga ta Kama hanyar wata mota dake tsaye, afusace ya fito tare dacewa
"Fatima kina hauka?... Can't you see am waiting for you?.." Ya tambayeta afusace, Maryam bata juyo ba ta Kara sauri Don ta shiga motar su Aisha, da sauri suhail yabi bayanta, Tana bude mota suhail na Kama mata hannu tare da fixgota, da sauri Aisha Ta juyo ta zubawa suhail idanuwa, she's like
"Wow..." Amma sai tace
"Malam meye haka..." Ta fada afusace, suhail bai ko juyo ba ya jata, sai kokarin kwace kanta take amma kaman she's not doing anything,
"Dalla ka saketa mana kazo ka Kama yarinya kamar matarka..." Aisha Ta daka mashi tsawa, ahankali suhail ya juyo tare da kallonta from head to toe Sannan yace
"Wato you want me to reply you kou?... Well I did...sai ki ji dadi..." Ya fada yanayi mata wulakantantar kallo, tsoki Aisha taja tare dacewa
"Waye wannan kuma?...Ashe in ji dadi...kana treating mace kaman namiji and..." Afusace suhail ya juyo ya nunata da yatsa,
"I don't talk to people anyhow amma don't you ever talk to me like that....am warning you..." Ya fada sannan ya bude mota ya wulla Maryam ciki tare da komawa ya shiga, kallon ta yayi zai bude baki yayi magana sai yaga its of no use since it's not helping matters, Dan guntun tsoki yaja ya figi motar ya bar wajen. In silence suka Isa gida, yana parking ta fito ta barshi nan zaune, kallon ledan Kayan daya tsayo yayi yaja tsoki tare da fita da ledan a hannunshi.

Yana shiga cikin ya dauki waya yayi dailing number ta luckily ya shiga, har ta gama ringing ba'a dauka ba, sai da ya Kira kusan sau biyar ta daga, still abinda ya fada mata jiya ya sake maimaitawa wannan Karin har da kukan karya, shuru kawai tayi Tana sauraron shi, da ya nemi Jin why she's not talking sai cewa tayi she's in bad mood ne, yafi hour yana nanata he loves her, tun batason magana har ta fada bashi amsa. Sai ta nuna she's tired sannan ya kashe waya.
Chapter 54 · 0% Book details