← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 190

Sashe 121

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 7 min read

Itama Maryam Tana komawa class kawai sai ta fashe da kuka, she don't know why she's crying amma her heart hurt very bad, tambayan Aisha ta hau yi amma ko magana batayi saboda yanda ta hada Kai da table Tana sharara kuka, bayan kaman minti biyar shugaban makarantar ta aiko kiranta, goge face dinta tayi ta mike ta je, wuri ya nuna mata ta zauna kanta kasa,
"Fatima kinsan haramun né taba Wanda ba mijinki ba?.. " malamin ya tambayeta Kai tsaye, wet face dinta ta daga ta kalleshi tare da daga mashi Kai,
"Tou wane dalili yasa kika rungumi kato cikin makarantar nan...salon kija mana zagi a gari..." Da sauri tace
"Wa na né..." Ta fada cikin kuka,
"Wanki me shine zaizo cikin makaranta yana rungume ki?.." Malamin ya tambayeta cikin tsananin fada,
"Tafiya zai yi..." Ta amsa mashi cikin matsanacin kuka, mutum shuru yayi yana kallon yanda take kuka kaman an doketa,
"Wai dukan ki akayi né?.." Ya tambayeta, da sauri ta girgiza mashi Kai tare dacewa
" Kaina me ke ciwo..." T fada mashi,
"Tashi ki tafi dakin Hutu..." Mutumin ya fada mata atakaice, ba karamin fada yayi niyyar yi mata ba amma duk ya kasa saboda yanda take ta sharara kuka,  ahankali ta mike yaje rest room dinsu ta zauna ta hada Kai da gwiwa Tana kuka. She cried and cried and cried Don har aka tashi bata bar kuka ba, kafin driver yazo daukar ta tayi developing fever, ni kam tagumi nayi Ina kallon suhail a jirgi yana kuka amma babu Wanda yasani saboda kafin hawayen ya fito har ya goge, then Maryam zaune bayan mota Tana kuka, idanuwanta sun yi mugun kumburi, kawai Tana sauka daga cikin mota sai taga gidan wani iri kaman ba wannan gidan ba, it seems so dull kaman an cire wata annuri daga cikin gidan, ahaka ta taka ta shiga part din salima, ko inda salima take bata kalla ba ta shige dakinta, kwantawa tayi kan gado Tana kuka, ahankali salima dake fama da jikinta ta mike tabi bayanta, kwance ta tarda Tana kuka, cikin tashin hankali ta fara tambayan ta abinda ke damunta
"Kaina né ke ciwo..." Ta fada cikin kuka, daga Kanta salima tayi Tana kallon yanda idanuwanta suka kumbura Sannan duk jijiyoyin gaban goshinta duk wajen
"Subhanallah...sannu Bari in fadawa alhaji ya Kira Doctor..." Ta fada Tana mikewa, hannunta Maryam ta Kama tace
"Anty..." Ahankali salima ta koma ta zauna tare dacewa
"Naam..."
"Zan sha ruwa..." Ta fada still crying,
"Tou " salima ta amsa mata Sannan ta fita daga dakin, few minutes later ta shigo da robar ruwa da cup, ruwa ta zuba mata Maryam ta mike ta amsa ta jika  throat dinta Sannan ya sake bajewa Tana kuka this time da karfi sosai har da dirza kafa a kasa kaman yanda ta sabawa yi dad dinta, yanda take kuka yasa hankalin salima mugun tashi saboda she's crying kaman ance dad dinta ya mutu, da sauri salima ta fita ta sanar da dad abinda ke faruwa, shima cikin tashin hankali ya Kira Doctor, baya kaman minti goma ya sake Kira ya tambayi salima if she's still crying, salima datayi tagumi ta saka Maryam gabaTana kallon ta Ta amsa  mashi da eh,
"Bata wayar " Alhaji ya umarceta, mikawa Maryam waya tayi
"Haba sarauniyar mata meyafaru haka?.." Alhaji ya tambayeta Cikin lallami, abinka da yar rigima sai cewa tayi
"I want to go back home..." Ta fada har lokacin Tana dirza legs dinta kaman zata ballesu, kunsan Maryam da rigima,😜
"Hajyata wani abun akayi maki?.." Alhaji ya tambayeta cikin tashin hankali, da Sauri tace
"No...I just want to go home..." Ta amsa mashi,
"Ki fada min abinda akayi maki...kinsan zan hukunta duk Wanda ya taba min the boss...ki fada min kinji.." Alhaji ya tambayeta, cikin kuka tace
"Kaina né ke ciwo.."
" na Kira Doctor...Yanzu zai zo..kinji kou" ya fada mata,
"Tou..." Ta amsa  mashi sannan ta mikawa salima data fita hayyacinta waya ta koma ta kwanta. Sai Karfe 6.02 Doctor ya iso gidan, drugs ya rubuta mata a kaje aka sawo mata.

Just in typing mood, see you on Wednesday Don Wallahi typing with enough time is better and sweeter. Thanks for the love, I can feel it.
40💛💜❤💚💙
Wulakanci dodone....
💛💙❤💜💚

® zuwairat (ummumaryam)

4⃣ 0⃣

Har dare bata ci komai ba and so is suhail, kowanne da abinda ke damunshi, shi suhail yasan its Maryam amma ita bata San takamemen abinda ke damunta ba because bata taba Jin abinda take ji ba, she feels so bad, wajen Karfe 8 alhaji ya shigo dakinta da tray of food Don salima ya fada mashi taki cin abinci, da sallama ya shiga ta mike zaune face dinta kaman ba nata ba, alhaji ajiye tray yayi ya zauna kujerar sake kallon ta, sai shessheka take,
"Dan Allah Dan Annabi ki fada min abinda akayi maki.." Alhaji ya fada calmly, ahankali ta girgiza Kai tare dacewa
"Nothing..." Ta amsa mashi cikin shakakar murya,
"kin ce ba komai alhalin tunda da kika dawo islamiyya kike kuka...kinyi bacci ki farka kin kincigaba da kuka...kinki cin abinci..antynki ta shiga damuwa...itama ta kin cin abinci saboda ke...Dan Allah Maryam fadamin abinda akayi maki..." Alhaji ya tambayeta cikin damuwa,
"Kaina né ke ciwo..amma da sauki..." Ta fada mashi, kura mata Ido yayi yace
"Are you sure?.." Ya tambayeta, ahankali ta daga mashi Kai alaman eh,
"To madalla...ki Dan ci abinci.." Y fada yana tura tray din gabanta, Don kar tayi mashi gardama ta Dan ci kadan sannan ta koma ta kwanta,
"Kindai yi sallah kou?.." Ya tambayeta, ahankali ta daga mashi Kai, sai da safe yayi mata  ya fita, kwanciya tayi Tana tunanin suhail, everything about him, haka nan sai ta Dan firgita saboda yanda taji kaman hannunshi a bayan wuyarta. Haka nan sai ta Dan saki murmushi Tana lumshe idanuwa, tunawa tayi da the first time data ganshi, then abubuwan da yayi mata Sannan zuwansu abroad da dawowansu da confession dinshi na sonta sai zuwansu katsina da abubuwan da suka faru, she's hearing his voice cikin  kunnenta, yanda yake kissing dinta, yanda ya ke taba jikinta,
"Bad boy..." Ta fada  Tana hawaye.
"He's a bad guy..." Ta sake fadawa kanta,
"That's why yake tabani..Don in ya tafi in dinga tunashi...so that he will be stuck in my brain..." Ta fada ahankali,
"Mugu..." T sake fadawa kanta still weeping. Pillow ta dauka ta Dora bisa cikinta Tana kuka.

Shima suhail bayan yayi sallah ishai ya kwanta rungume da pillow, he's missing her like hell, gani yake har ya bar duniya he will never misses anything or anyone the way he misses her, gani yake ba zai iya aikin komai inda zashi ba Don ya bar heart dinshi a Nigeria, kallon agogon hotel room daya sauka a Lagos yayi yaga 8:30, wants to call her amma yasan she won't pick and that will break him the most, still ji yayi he needs to try he's luck, wayar shi ya dauka yayi dailing numbar ta, sai adua yake Allah yasa ta daga yaji voice dinta,

Daga chan bangaren Maryam dake kuka taji karar waya, da sauri ta mike ta dauki wayarta sai taga mr I love you, harara ta gallawa wayar Tana cewa
"Don yasan halin da nake ciki...to an ki din.." Ta fada Tana ajiye wayar, har ta gama ringing bata dauka ba, ajiyewwa yayi ya sake ringumar pillow yana cewa
"Pls happiness make it easy for me..." Ya fada yana sake daukar wayar, message ya tura mata yana cewa
"I arrived safely..Yanzu Ina hotel room da zan kwana kafin in wuce gobe....am missing you badly..still thinking about katsina...it's all over me...I love you...pls in bakison magana Dani ki taimaka ki hau whatsapp muyi hira ko na minti biyu né...pls.." Ya tura mata. Maryam najin karar message tayi saurin budewa Tana karantawa da idanuwanta da suka kankance saboda kuka,
"Ba a hawa din.." Ta fada Tana ajiye wayar.
Data  suhail ya kunna yana jiran ko Allah zai sa ya ganta online amma shuru har Karfe tara, message ya sake rubuta mata kamar
"Pls Ina jira mana...Dan Allah babyna.." Ya sake tura mata amma still shuru har goma,
"Shikenan...good night...I love you.." Ya sake tura mata Sannan ya kashe wayar shi bayan sunyi waya da mom dinshi, kwanciya yayi yana sauke ajiyan zuciya. Har kusan ukun dare idonshi biyu, baici komai ba but he's not hungry. Itama Maryam sai wajen twelve ta kwanta. A bangaren Salman abun takaici ya ki karewa saboda yaje gidansu Maryam bai kirata ba because her number is not going, Mai gadi ya shiga kiranta a kace bata nan, lokacin Maigadi salima ya tarda a falo, Salman sake aikawa yayi a tambayo inda taje sai salima ta aika mashi da bata sani ba. Haka ya koma gida da haushi, shi dai he's smelling something is wrong.
Chapter 121 · 0% Book details