← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 172 OF 190

Sashe 172

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 6 min read

Murguda baki tayi ta ajiye phone din kan kitchen drawer ta fito gabanta na faduwa, tasan hajiya habiba yar mom dinta ce uwa daya uba daya, she loves her so much amma she's a no nonsense person, tun tun daga nesa ta hangi abincin hajiya habiba sai sheki yake, kallon plate dake hannunta tayi ta Kara kallon na hajiya habiba while walking towards her, hajiya habiba cigaba da cin Abincin ta tayi kaman batasan ta taho ba, sai da ta zo dab daita ta juyo ta kalleta da plate of burnt rice dake hannunta, ji tayi dariya ya kufce mata saboda yanda Maryam ta maraice fuska,
"Gimbiya har kin gama dafa Abincin kenan.." Ta fada idanuwanta kan Abincin, Maryam shuru tayi kanta kasa,
"Ki zauna mana..." Hajiya ta fada mata, ahankali ta ajiye plate of Abincin ta Sannan itama ta zauna, kallon Abincin gaban hajiya tayi ta kalli nata sai taga the difference is clear, sai Yanzu ta gane cooking ba abin wasa bane, she remembered yanda masu aikinsu ke jera mata abinci kala kala, she never feels it's a big deal,
"Kawo Abincin ki Inyi tasting,.." Hajiya ta fada mata, ahankali ta sauka ta dauki Abincin ta Kai mata,
"Mommy it's burn..." Tafada kaman zatayi kuka, shuru hajya tayi bata ce komai ba har saida ta Kai spoon daya bakinta Sannan tayi saurin zubdawa Tana kallon Maryam
"Ya akayi the food taste awful...gashi har gonewa yayi..aikin me kike har abincinki ya kone?... Don't you know it's a bad habit for a woman to allow her food get burnt?.." Hajiya tafada mata cikin bacin rai, Maryam shuru tayi kanta kasa,
"Can you eat this?.." Ta tambayeta, ahankali Maryam ta girgiza mata Kai,
"gaskiya kar hakan ya Kara faruwa... In ba haka ba I will personally call your daddy and tell him a daga ranar auren you're not ready..." Ta fada mata, shuru Maryam tayi without saying a word
"Take this thing away...kizo kici abinci...later zaki sake yin wani...kuma remember this saga yau kowa zaici abinda ya dafa,,,I won't give you my own food from today..kinji kou?.." Ta tambayeta, ahankali Maryam ta daga mata Kai,Sannan ta hau kan dining hajiya ta umarceta tayi serving kanta. Bayan sun gama cin abinci hajiya ta shiga bathroom ta hada mata ruwan wanka da wasu native perfume irin na yan maiduguri Sannan ta fito ta fadawa Maryam ta wanke lungun da sakon jikinta, babu musu Maryam ta shiga tayi wankan, ta Saba da turaren wanka kala kala amma wannan is something else, the scent is so sweet, fitowa tayi daure da towel taga hajya tsaye rike da garwashi a hannunta sai wani kujera Mai hole a middle a gefe daya na dakin, bata taba ganin wannan kujera ba sai yau,
"Kina da pant a jikin ki?.." Ta tambayeta ahankali Maryam ta daga mata Kai,
"Koma ki cireshi..." Ta fada mata atakaice, babu musu ta koma bathroom ta cire pant data saka, Tana tsaye taga hajiya ta zuba wani Abu cikin garwashin taga tayi saurin ajiyewa kasan wannan kujeran tare dacewa
"Yi sauri ki ware legs dinki ki zauna sama..." Ta fada mata, da sauri Maryam taga hayakin dake fita zata bude baki tayi magana saboda gani take roasting dinta zatayi
"Ke don't argue with me...kin San amfanin wannan hayakin kuwa kike Bari yake wasting..be fast ki zauna sama..." Ta fada mata, Maryam bata Kara cewa komai ba ta taka zuwa wajen kujeran jikinta sai rawa yake gabanta na faduwa, cikin fargaba ta ware legs ta zauna kan abun, she can hear yanda hayakin ke shiga jikinta,
"It's not bad..." Tafada cikin ranta Tana lumshe idanuwa, hajiya na nan tsaye har hayakin ya daina fita ta dauki abun garwashin tare da cewa
"Stay right there.."ta umarceta, nodding Maryam tayi without saying a word,
"Wane irin Abu né wannan?.." Maryam ta fada Tana daga towel Don kallon gabanta, tun da take bata taba witnessing such things ba, everything look weird to her, few minutes later hajiya ta sake dawowa da wata garwashin ta zuba Ana perfume ciki, tayi saurin ajiyewa nan kasar kujera Sannan ta dauki wata zanin gado Ta lullube Maryam dashi, wani irin kamshin take ji har cikin system dinta, duk da Tana amfani da designer perfumes kala kala bata taba Jin irin wannan kamshin ba, sai lumshe idanuwa take while kamshin na ratsa duk jikinta, sai bayan kaman minti biyar Sannan hajiya ta yaye zanin gadon sai sweating take kaman tayi racing,
"Ki tashi ki saka Kaya..." Hajiya ta fada Sannan ta dauke garwashin ta fita daga dakin,  Tana fita Maryam ta fara shinshina jikinta taji wani irin sweet scent
"Those African people with wonders..." Tafada wearing a smile, doguwar Riga ta saka ta fito falo taga Tana rubutawa mai aikinta list na abubuwan da zata sayo mata daga kasuwa, side dinta taje ta zauna sai lumshe idanuwa take.
Suhail kam yana gama waya da Maryam ya sake ajiye wayar ya cigaba da bacci,  kaman San a he ya tashi yayi sallar zuhr ya sake komawa, he wonders wane irin mahani yasha haka, yana Shan maganin bacci amma bai taba shanwanda yasa yaji yanda yake ji ba, duk jikinshi kaman ba nashi ba , he feels so weak, wajen three aliyu yazo gidan Wanda yasa ya mike dole, lokacin yaga babu laifi he's seeing amma jinin bai washe daga idanuwanshi completely ba, falo ya bar aliyu ya shiga bathroom yayi wanka ya fito sanye da jallabiya, yana tafiya kaman Ana ingiza shi,
"wai guy da gaske in three weeks zakuyi aure da Maryam?.." Aliyu ya tambayeshi, murmushi suhail ya saki Sannan yace
"yesss...can you believe that?.." Suhail ya fada cikin excitement, dariya aliyu yayi yace
"Kasan Wallahi sai Yanzu na samu kwanciyar hankali...Wallahi we all thought we are going to loose you..."
"ai ni Kaina has given up,on life...nasha ba kar wahala...naji jiki...no body had ever suffered for love the way I did...kasan Wallahi in makaho yata ko Dana yace yana so I won't object..." Dariya aliyu yayi yana cewa
"" mr lazy anyi hankali..." Aliyu ya fada cikin dariya
"All thanks to my happiness da ku gaba daya...you guys have been besides me...nagode  because I don't know what I would have done without friends like you..." Yafada sounding serious, harara aliyu ya watsa mashi yace
"Dalla rufe mana baki...sai kace wani Mutumin kirki..." Yafada cikin dariya, dariya shima suhail yayi yana relaxing tare da yin hamma,
"Am hungry..." Suhail ya fada yana kallon kan dining dake dauke da tray na abinci, mikewa yayi shima aliyu ya Mike, tare suka ci abinci cikin kwanciyar hankali.
Alhaji Ismail sawa yayi aka bugo invitation cards da yawa Don bayan sun baro hospital cikin Daren ya kira wani babban publishing company dake nan Kano ayi masu the most expensive invitation card, the following day aka kawo su carton guda Wanda aka dinga circulating na auren suhail da Maryam, duk Wanda yaga sunan shugaba jikin iv sai yayi mamakin inda suhail ya hadu daita har ya kaiga aure, cikin wayanda ke cikin jimami har da Salman, yana zaune da wani abokinshi a Shago yana kallon iv dake hannunshi sai cije yatsa kawai yake
"Wai meke damunka kake fama cizan yatsa..." Inji Wanda ke zaune yana kallon shi, ahankali Salman ya girgiza Kai yace
"Wallahi wannan yarinyar da ni zan aureta...Wallahi halina yajamin..." Bai karasa ba Mutumin ya kwace da dariya yana cewa
"Kai Wallahi ka iya abun dariya...Ina ka San wannan yarinyar da har zakace Kai kaso aurenta?.." Ya tambayeshi not believing what Salman is saying
"Wallahi guy da gaske nake...munyi soyayya daita..."
"Kai Dan Allah ka bar wannan maganar ..kar ajika a kulleka kana batawa yar mutane suna.."
"Tou na bar maka..." Salman ya fada duk ya rasa Abunda ke damunshi.
Chapter 172 · 0% Book details