← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 190

Sashe 106

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 4 min read

Yau Wednesday and har lokacin suhail yana hospital, friends sai zuwa suke Sannan har lokacin dai suhail bai fada masu ga abinda ya faru ba because yasan babu Mai magance mashi problem dinshi, baiyi wa kowa magana sai tunani dukda Doctor yace he should becareful kar ya sa samu heart problems.  Maryam kam itama she's thinking Akan ayya tayi daidai kenan? Saboda yanda suhail yace he loves he Sannan ta barshi hospital ko sau daya bataje ba and she knows he's sick because of what happened, Tana zaune falo taga salima ta fito da ruwan tea cikin flask da wasu abubuwan, Dan kallon ta tayi tace
"Anty hospital zaki?.."
" eh.." Ta amsa Mata Kai tsaye saboda haushin taurin Kan Maryam take ji,
"Ina zuwa..." Ta fada cikin sanyinmurya,
"Tou shikenan..ke ki tafi da ruwan shayin...dukda nasan ba sha zaiyi ba..,anjuma in na gama abincin rana sai inzo.." Salima ta fada mata, itadai ba haka taso ba amma bata ce komai ba ta mike ta shiga ciki ta fito sanye da long hijab ta amshi Kayan hannunta, daman driver na jiran, Tana fitowa ta shiga mota gabanta sai faduwa kawai yake.

Suhail na zaune sanye da singlet sa three quarters, ya rame sosai Sannan yayi duhu, hajiya na zaune sai kokarin bashi lemo take amma babu abinda yake sai kauda Kai,  kofa aka bude driver ya shigo rike da basket sai Maryam biye dashi, ahankali suhail ya daga Kai yaga Maryam tsaye, tambayanshi driver yake ya jikin amma ko kadan bai ji balle ya amsa mashi, ganin irin kallon da yake wa kofa yasa hajiya juyowa nan taga Maryam tsaye, baki ta tabe ta mike tsaye  ta fita daga dakin Don kunya suhail ke bata saboda irin kallon da yakewa Maryam, gaidata Maryam tayi amma ko kallon inda take batayi ba ta fice daga dakin, ahankali taka zuwa kusa dashi Tana kallon yanda ya koma
"Hey..." Ta fada cikin sanyinmurya,
"Hey...! Ya amsa mata yana kallon ta,  driver ajiye basket din hannunshi yayi Sannan ya kalli Maryam yace
"In tafi ko in jiraki!.." Ya tambayeta,
"Ka jira.." Ta fada Tana zama kan kujerar masu jinya, Bata idaba suhail yace
"Ka tafi.." Ya fada mashi atakaice, Maryam zata bude baki tayi magana suhail ya sake cewa
"Ka tafi.." Yayi commanding dinshi, bai tsaya ba yayi wajen, sai da ya fita ya kalli Maryam yace
"Hope you're happy...Don kin kusa kashe min zuciya.." Ya fada mata, daga Kai tayi ta kalleshi wearing a friendly smile tace
"Sorry..zaka wuce wajen..." Ta fada hankalin ta kwace, wani irin kallon takaici yayi mata yace
"Allah kou...let's see if you will get over what I have in mind for you..." Ya fada atakaice, kallon shi tayi tace
"Ban gane ba...what do you have in mind for me?.." Ta tambayeshi gabanta na faduwa,
"Ban sani ba... Hope dai kina baccin dare Yanzu da baki Jin voice Dina?.. Hope you're glad?.." Ya tambayeta, shuru tayi Tana wasa da yatsun ta,
"Ko Dan Allah ki taimaka ki hada min tea?.." Ya tambayeta, bata ce komai ba ta mike ta bude baskets data kawo ta hada tea ta taka zuwa inda, idanuwa ya lumshe yana shakan kamshin ta, ahankali ya bude ya mashi tea din yashanye duka, komawa tayi ta zauna, sai binta yake da kallo,
"Pls can I ask for a favor?.." Ya tambayeta cikin sanyinmurya, ahankali ya daga Kai ta kalleshi tare dacewa
"Na me?.."
"Kawai so nake Dan Allah ki dinga kawo min abinci...Wallahi tun shekaran jiya ban ci komai ba sai wannan tea da kika bani da hannunki...at least nasan bazaki so kiga na mutu ba..." Ya fada cikin magiya, shuru tayi bata ce komai ba,
"pls happiness...don't say no again...I know I can only eat something that comes out of your hand...pls ki taimaka min har in samu lafiya..." Ya sake rokarta, Dan kallon shi tayi Sannan tace
"Ok..." Da sauri suhail ya lumshe idanuwa yana cewa
"Then zan koma gida yau...hope a gida ma zaki kawo min?.." Ya tambayeta, still shuru tayi,
"Pls happiness..kinsan I will travel soon, so nake in dan maida jikina kafin in tafi...if you can just help for this few days...that's all...bazan sake néman wata alfarma daga gareki ba...pls kinji " ya roketa, idanuwa tayi rolling tace
"Naji....but pls inason ka sani cewa ba wai I mean anything da rashin amincewa da Kai ba...kawai banason fara relationship Yanzu.." Bata karasa ba ya katse ta dacew
,"Dani kou?.." Ya tambayeta, shuru tayi batace komai ba, Dan ajiyan zuciya ya saki Sannan yace
"Ba komai Ai...Allah na gani I love you...amm if am not good enough to be loved by you ba matsala..." Ya fada cikin sanyinmurya, empty cup ya mika mata ta tashi Ta amsa. Wayan ta né yayi kara ta duba taga Salman, murmushi ta saki cikin ranta Tana cewa
"Har na mance da Kai..." Suhail kallon ta kawai yake yana imagining waye yake Kira that makes her brighten up haka, picking tayi Tana cewa
"  Salman ka tuna da ni yau kenan.." Ta fada Tana dariya, suhail dafa heart dinshi yayi saboda yanda yaji kaman zata fito saboda kishi.
35💚❤️💙💜💛
Wulakanci dodone...
💜💛💚💙❤️

®zuwairat (ummumaryam)

3️⃣5️⃣
Chapter 106 · 0% Book details