Sashe 167
Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 6 min read
ba hankali gareta ba...Tana iya kin. Dawowa...." Ya fada mata yana dariya itama dariya tayi tabi bayan su, har waje alhaji Mahmoud ya rakasu ya umarci driver dinshi ya kaisu hospital, A hospital kam su aliyu basu bar wajen ba sai wajen Karfe uku da rabi bayan sunyi sallah asr, alhaji da ko ruwa ba tunda da safe na zaune yaje an bude kofa, ahankali ya jiyo yaga Maryam, Maryam na shiga ta kalli kan gadon sai tayi saurin juyawa Don gani take ba dakin da Doctor yace su shiga bane because ko kadan batayi recognizing suhail né kwance ba, "Daughter.." Taji alhaji ya kirata, da sauri ta sake juyowa saboda muryar dad dataji because ko kadan bata ganshi ba, idanuwa ta zaro ta taka two step tazo tsakiyar dakin, babu abinda take kallo sai kan gadon, ji take gabanta na mugun faduwa, hajiya da su Salima suka shigo, da sauri hajiya ta karasa bakin gadon ta rike hannun suhail Tana cewa "Eyeballs..ya Maryam Dinka na kawo maka...pls open your eyes..." Ta fada Tana rike da hannunshi da aka saka Karin ruwa, ji kake tim, da sauri hajiya da sauran mutane suka juya, Maryam suka gani kwance kasa bata numfashi, da sauri sukayi kanta, da gudu alhaji ya fita ya Kira Doctor, hajiya rike Maryam tayi Tana girgiza ta tare da kiran sunanta amma shuru ko motsi batayi ba, "Nashiga uku..." Hajiya ta fada cikin tsananin tashin hankali, da sauri habiba ta dauko ruwa dake kan table ta watsa mata, a firgice ta mike zaune Tana kalle kalle, kaman mad person ta mike ta nufi gadon da suhail ke kwance ta fashe da kuka Tana cewa "What happened to you...wayyo Allah na wake up..." Ta fada shaking dinshi da karfi Tana kuka, hajiya habiba tazo riketa tayi saurin fixgewa Tana rike da suhail sai girgiza shi kawai take, hajiya gefe daya ta koma Tana kuka so is Salima, "Wake up..." Ta fada da karfi, ahankali suhail ya Dan juya kanshi, "Wake up.." Ta fada Tana dukanshi da karfi, alhaji né ya dawo da Doctor, da sauri Doctor ya karasa wajen yana cewa "Pls stop...na bashi maganin Hutu né saboda yanda yake complaining...pls don't hit him again..." Doctor ya fada mata, ahankali ta zame ta zauna nan Kasan gaban gadon ta dinga rusa kuka, tasan he has been through hell saboda yanda ya koma says it all, kuka ta dingayi har da dirza kafa kasa, hajiya da sauran mutane suka dinga bata hakuri amma ko kallon inda suke batayi balle Ta amsa masu, suhail sake juyawa yayi this time tare dacewa "Wayyo..." Ya fada yana dafa chest dinshi, da sauri Maryam ta mike, hannunshi ta Kama Tana cewa "Sorry...." Tafada cikin matsanacin kuka, suhail da bai bude Ido ba ya sake sakin Kara yana cewa "Wayyo Allah na..." Ya fada sounding so weak, "Sorry.." Maryam ta sake cewa, Kara juyawa yayi tare da squeezing face dinshi yana cewa "Zafi..." Ya fada kaman zaiyi kuka, alhaji sake fita yayi ya Kira Doctor, hajiya bakin gadon tazo Tana cewa "Eyeballs...pls if you're listening to me am sorry...na kawo maka Maryam..pls don't give up on me..." Ta fada Tana rike da hannun Maryam, ahankali ta saka hannun Maryam cikin nashi, Doctor né ya shigo ya Kira sunan shi bai amsa ba sai juyawa da yake yana dafe da kirjinshi, "Can you hear me?.." Doctor ya fada amshi, shuru yayi yana juye, ahankali Maryam ta Dora kanta kan kirjinshi Tana kuka, da dakatar da juye2 yayi kaman Mai sauraron wani Abu, bai Kara motsi ba ya koma bacci, hannunshi cikin nata sai sakin ajiyan zuciya kawai yake, da kyar taje sukayi sallah ta dawo, suna fita daga inda sukayi sallah hajiya ta kalli Maryam da har lokacin hawayenta bai bushe ba tace "Dear me zan sayo maki kici.." Hajya ta tambayeta sounding so caring, cikin kuka Maryam tace "Ba komai..." Ta fada cikin sanyinmurya, komawa sukayi ciki, sai bayan sallah magrub suhail ya farka, sai sauke ajiyan zuciya kawai yake, da sauri Maryam ta Kama mashi hannu, bai bude Ido ba ya Kama hannunta da two hands dinshi, hannun ya fara shafawa ahankali ya bude baki yace "Happiness..." Ya fada with his eyes closed, murmushi Maryam dake kuka ta saki tare da amsawa, L"Am sorry..." Bai karasa ba ta Dora daya hannunta kan bakinshi "No ...it's all my fault ..." Hannu suhail ya daga yana néman face dinta, dasauri ta Kama hannunshi ta Dora kan wet face dinta, ahankali ya fara Shafa face dinta yana cewa "Wayyo pls kar kiyi kuka..." Ya fada mata, "Open your eyes..." Ta fada cikin kuka, ahankali ya Dan bude idanuwanshi yana cewa "I don't see well..." Kukan hajiya yaji da karfi yace "Mommy..." Ya fada yana ware free hand dinshi, da sauri hajiya ta Kama hannunshi yana kallon yanda idanuwanshi suka Chanza , "Eyeballs na kawo maka Maryama...Dan Allah you should get well for her..pls..." Hajiya ta fada cikin kuka, hannunshi cikin nata ya saki murmushi without saying a word, "Pls get well soon...I can't wait in gan ka samu lafiya...I can't wait to be with you again..." Hajiya ta fada cikin matsanacin kuka, "Mommy pls ki bar kuka,.." Ya fada mata, "Ok na daina..." Ta fada mashi Tana goge face dinta, "You give me your proposal...I have taken it.. I accept I will be with you for eternity..."Maryam ta fada mashi bataji kunyar wayanda ke wajen, ahankali suhail ya girgiza mata Kai yana cewa "Not now..." "Yes now...remember you said zakayi duk abinda nakeso...nidai just get well soon..." Ta fada mashi, ahankali ta Kai bakinta wajen cheek dinshi tayi mashi kiss, Kara moving bakinta tayi sama wajen kunneshi tace 'remember that night a gidan grandma..." Ta fada mashi cikin whisper, alhaji barin dakin yayi ya fita ya Kira alhaji Mahmoud suhail ya farka, hajiya dake kallon su taga suhail ya saki dariya sosai kaman bashi Bane on hospital bed, "Oh haka nan naso kashe Dana da Kaina da son zuciya..." Hajiya ta fada cikin ranta, Tana kallon yanda suhail ke dariya yayi da Maryam nayi mashi magana cikin kunne, "We will get to be together at all times...babu Interruption...I will sleep in your sugar arms..." Ta sake rada mashi, dariya kawai suhail yake, "But no sex..." Ta sake rada mashi, dariya suhail ya sake yi yana rike da chest dinshi "You will change your mind about that..." Ya rada mata, "No way..." Ta sake rada mashi, salima kallon hajiya tayi suka sakarwa juna murmushi. Bakin gadon Maryam ta zauna ta Dora kan suhail kan cinyarta, hajiya habiba rasa inda zata saka kanta tayi saboda kunya, Don tamkar babu kowa dakin haka suke, Shafa kanshi tayi ta sakeyi mashi kiss gaban goshi,