← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 190

Sashe 14

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 5 min read

Bayan sallan ishai abokan shi suka tafi, zama yayi kafan shi daya kan daya yana maida numfashi ahankali tare da lumshe eyes, ahankali ya daga Ido yana kalli wani latest American movie Mai suna the rich Italians, ganin yanda ake da kudi cikin film din yasa ya fara tunanin yar boss din baban shi, abinda ke bashi mamaki shine yanda ko sau daya bai taba ganinta ba amma he always think about her, at times in ya zauna sai yace in ba Don kar a ce ya fara hauka ba da sai yace in ba Maryam ba bai taba yin aure amma yasan hakan ba karamin zagi zai janyo mashi wajen dad dinshi ba sannan dariya wajen abokan shi, remote ya dauka ya kashe kallon tare da sakin short tsoki ya juya Kai one side, yarinyan main palour din su ta fado mashi a rai, tsoki ya sake ja tare dacewa
"Mayya sai dai kici kanki...." Ya fada yana mikewa, kallon plates da food warmers dake kan dining dinshi yayi yana fita daga part dinshi. Hasken compound din kaman rana, cikin kasaita ya taka ya shiga falon mom dinshi, gani yayi ba kowa falo, ko wasting of time baiyi ba ya nufi dakin masu aiki, ba knocking ya bude kaman yanda ya sabayi at times, asabe dake daure da towel tayi saurin durkusawa kasa while Maryam dake kwance kan katifan da murja tace suyi sharing tayi saurin duba Kofan saboda yanda aka budeta da karfi, kallon asabe data durkusa kasa yayi tare da tsakin tsoki before saying
"Ko uban me zan kalla da har kike wani nonnoke Kai?... Oho...." Ya fada face dinshi yamutse kaman Mai kyaman wani abu, ya Kara dacewa
"Ni kukeson in kwace plates kou?..." Ya daka masu tsawa, da sauri suka amsa mashi da
"Aa..." Amma Banda Maryam da tunda ya bude kofa ta ya shine ta juya kwanciyan ta tare da bawa Kofan baya, kallon Maryam yayi kaman zai wata magana amma sai yayi shuru
"It's too early for that..." Ya fada kasan makoshinshi, sannan yayi banging Kofan ya bar wajen murja tayi saurin mikewa taje part dinshi ta dauko plates din sannan ta dawo ta kwanta, Maryam kam kasa bacci tayi Tana tunanin wannan awful guy din Don tamkar dodo take ganinshi. Upstairs suhail ya hau ya tarda mom dinshi ta shirya cikin Kayan bacci amma ta daura wrapper sama, kallon shi tayi lokacin da yake zama in doguwar kujera tare dacewa
"Eyeballs bakayi bacci ba?..."
"Yes mom..just tired..." Ya fada yana hamma tare da Dora legs dinshi kan kujeran, Dan dariya hajiya tayi cikin son da kaunar danta tace
"Eyeballs kaman wasa dai you're lazy..,duk yau ko fita bakayi ba amma sai kukan gajiya kake...." Dan dariya shima yayi yana Shafa gashin kanshi tare dacewa
"Ai momcy ko zama cikin su sadeeq is tiring...su sa mutum magana..." Ya fada yana relaxing kan kujeran tare da rufe eyes kaman Mai Jin bacci,
"Sun tafi kou?.." Hajiya ta tambayeshi
"Yes mommy..."
"Hope sun ci abinci kafin su tafi?"
"Yes .." Ya sake amsa mata idanwanshi biyu lumshe sai hand dinshi daya kan goshinshi, agogon dake hannunshi sai walkiya kawai take,
"Mommy am so tired da abinda dad yake min gidan nan...he hates me so much..." Suhail ya fada yana tunanin yanda dad yayi downgrading dinshi gaban su sadeeq,
"What did he do again?..." Ta tambayeshi Tana kallon shi tare da maida dukkan hankalinta kanshi
"Wai he's Insisting ko in fara aiki kaman friends Dina ko kuma yayi min aure...ni wallahi mom banga yarinyan data yi min ba kuma am not ready to work now..." Ya fada cikin shagwaba kaman Dan three years, hajiya sai kallon shi take cikin Kauna Don tamkar ta maida danta cikin ciki take ji saboda so, at times Tana Jin son da takewa suhail yafi son da takewa kanta, gani take she can't survive without him, kwantar da murya tayi sannan tace
"Eyeballs gaskiya I will not hide this from you...Nima I want you to start working..." Da sauri suhail ya kalleta,
"Yes...am serious..." Ta fada calmly,
"Yanzu mom ke da dad zamuyi teaming against ni kadai?..." Ya fada kaman zaiyi kuka, da sauri hajiya ta Baro inda take zaune ta dawo kusa dashi legs dinshi dake kan kujeran ta cire ta maida kan laps dinta sannan tace
"Baby am not teaming against you...banason baki na tabamin Kai...so pls ka fara aiki kafin ka samu Wanda kake so...pls sweetest..." Ta fada Tana rike da Palm dinshi biyu cikin hannunta, suhail sai turo baki yake,
"Mom pls I don't want to work in Nigeria...ni nafison aiki abroad...na fadawa dad ya fadawa boss dinshi ya nema min aiki a abroad amma Yaki fada mashi...indai in na fara aiki dariya friends Dina zasuyi min...." Ya fada Kaman zaiyi kuka, mom dinshi shuru tayi Tana kallon shi bata ce komai ba,
"Ni dai help me talk to dad...pls momcy...." Ya fada kaman zaiyi kuka, nan take ya juyawa mom dinshi raayinta
"Ok son....naji...I will talk to him again...dukda nasan it's a lost cause I will still try it for you my love..." Tayi assuring dinshi, Dan murmushi ya saki tare da mikewa zaune,
"Thanks momcy..." Ya fada yana mikewa tsaye, kaman zai tafi sai kuma yace
"Momcy wai wacece dazun dad ya zo daita?..." Ya tambayeta, nan hajiya ta fada mashi exactly abinda alhaji ya fada mata, baki ya tabe yana cewa
"Ashe rainon jos ce...shiyasa dazun ta kura min Ido babu ko kiftawa....kaman wata mayya "
"What!!!.. To duk ranar da ta Kara ka kifa mata Mari...banason a shanye mani Kai..." Ta fada babu wasa
"Trust me mom...ai ban daukan raini...." Ya fada ya Kara dacewa
"Good night momcy..."
"Good night my eyeballs...." Fita yayi daga dakin ya Kama hanyan part dinshi.

❤💙💜💛💚one love.....
7💙❤❤💚💜
Wulakanci dodone...
💙💜💛❤💚

® zuwairat (ummumaryam)

0⃣7⃣
Chapter 14 · 0% Book details