← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 190

Sashe 43

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 6 min read

Bayan kwana uku suhail ya Kara rikicewa hajiya tunda alhaji bai yarda ya fada masu inda Maryam take ba, sai ya tisa  hajiya gaba yana kuka yana dukan kirjinshi, hajiya ce zaune kusa da alhaji Tana cewa
"Dan Allah alhaji ka rufa min asiri ka fadamin inda wannan yarinyar take...wallahi banason rasa d'ana....Dan Allah alhaji...." Hajiya ta fada kaman zatayi kuka, 
"My hajiya ai na sha fada maki na maidata wajen iyayen ta..." Ya fada sounding in I don't care manner, 
"Pls ka maidota..." Bata idaba yace
"In maidota ku kasheta kou..aa ku kyale ta ta zauna wurin uwarta..." Inji alhaji, ahankali hajiya ta koma tayi kneeling gabanshi Sannan tace
"Dan Allah my alhaji..ka taimaka min...Allah tun jiya suhail bai ci abinci ba...pls I promise babu abinda zan sake yi mata...I will take care of her..." Ta fada sounding very serious, dariya alhaji yayi Sannan yace
"Ai yarinyar in question is afraid of you...bazata yarda ta zauna daku ba Don kun koya mata hankali...sai dai kawai in Allah ya kaddara anyi bakin nan sai ta dawo ta zauna wurin yaruwarki..." Alhaji ya fada mata, tsoki hajiya taja ta mike ta barshi nan zaune yana shirin office. Part din suhail ta nufa ta tarda shi zaune yayi tagumi Tana shigowa yayi saurin daga kai tare dacewa
"Any progress?.." Ya tambayi hajiya yn mikewa tsaye, ahankali hajiya ta zauna tare dacewa
"Dear babu progress...yaki ya fadamin inda take...." Ta amsa mashi cikin sanyinmurya,
"Ba dai mutuwa ta yake so ba?... Ok shikenan..." Suhail ya fada yana barin dakin, waje ya fita lokacin shima alhaji ya fito daga part dinshi rike da briefcase, suhail baice mashi komai ba ya Kama hanyar gate, shima alhaji bai kalleshi ba ya shiga mota shi kuma Salman ya shiga baba ya tada mota, maigadi na ganin an tada mota yayi saurin bude gate, aikam suhail kwanciya yayi nan Kofar inda za'a bi da mota, da sauri Salman daya taho da mota yaci birki,
"What?.." Alhaji dake zaune baya ya tambayeshi da sauri yace
"It's suhail sir... " Alhaji bai wani damu ya yaga abunda ke faruwa ba yace
" me yayi?.." Alhaji ya tambayeshi Kai tsaye,
"Sir ya tare hanya...he..." Bai idaba alhaji yace
"What!!..." Ya fada yana bude kofa, suhail ya gani kwace hawaye na fita daga idanuwanshi hawaye na fita, afusace alhaji ya nufi inda ya tare masu hanya yana cewa
"Kai Dan ubanka are you mad?... " ya tambayeshi yana karasowainda yake, cikin hawaye suhail ya daga mashi Kai,
"Yes daddy..." Ya fada yana kuka daga inda yake kwance,
"Tashi kafin ranki ya mugun baci..." Alhaji ya daka mashi tsawa, da sauri suhail yace
"No....kawai ka bi ta Kaina...daman you hate me..just kill me so that you will be happy..." Ya fada cikin matsanacin kuka,
"I said ka tashi." Alhaji ya fada yana Kama hannunshi domin yaja shi, da sauri ya dauke hannunshi yana cewa
"Just drive on me...you hate me ..just proof to the world the kind of father you're...wallahi bazan tashi ba sai dai ka kashe..." Ya fada yana Kara relaxing nan kasa, hajiya ce ta fito compound taga suhail kwance bakin gate, da gudu ta isa waje Tana cewa
"Eyeballs what's wrong..na shiga uku..." Ta fada cikin tashin hankali, suhail daga wet face dinshi yayi ya kalli hajiya yana cewa
"Ki Bari ya karasani...wallahi ban tashi sai dai ya bita Kaina tunda my happiness doesn't matter to him...", alhaji tsaye yayi ya rike waist dinshi yana tunanin wane irin jarabawan na wannan, Don sai Yanzu ya tabbatar suhail da gaske yake, har ya hango irin wahalar da zaisha Don yasan bazai yuwu Maryam ta so ko aurenshi ba sannan shi kuma bazai taba Kai shi inda take ba sai dai yayi hakuri, hajiya kallon alhaji tayi da idanuwanta da suka ciko da hawaye tace
"Pls alhaji help me..Dan Allah..." Ta fada kaman itama Zatayi kuka, alhaji bai kalleta ba yace
"Suhail ka tashi kafin in sa securities su daukeka..." Ya daka mashi tsawa, cikin kuka suhail yace
"Kawai kill me,.." Ya fada mashi atakaice. Salman dake zaune cikin mota sai kallon ikon Allah kawai yake, baisan abinda ya haddasa wannan drama ba amma it must something serious ya fadawa kanshi,
"Security!!!." Alhaji ya fada da karfi, sai ga su uku sun iso I da suke, shima Salman kofa ya bude ya fito ya karaso inda suke,
"Bundle him out here..." Alhaji yayi commanding dinsu, da sauri sukayi Kai suhail har da Salman,
"Kar ku sake ku tabani..." Ya daka masu tsawa, amma banza sukayi dashi suka kamashi sai fad'a yake dasu Amma ko gizau suka ajiye shi gefe daya, da sauri ya mike ya Kama kafan alhaji yana cewa
"Pls just tell me where she is..pls daddy zanyi duk abinda kakeso...just tell me  pls..." Ya fada cikin kuka, sai lokacin Salman ya gane abinda ke faruwa, ahankali ya juya ya koma cikin mota tare da relaxing Don gani yake duk yanda yake Jin Maryam cikin jininshi suhail yafishi, idanuwa ya lumshe yana kallon yanda suhail ya kwanta kasa yana rike da kafan alhaji gam yana mashi magiya ya fada mashi inda take, alhaji kokarin kwace kafan shi yayi amma a banza, ahankali yace
"To tashi in fada maka inda take..." Ya fada cikin sanyinmurya Don ba karamin tausayinshi yake ji ba, da sauri suhail ya mike yana shessheka,
"Tana katsina..gidan inna..." Ya fada mashi, da sauri suhail ya juya ya bar wajen yana goge face dinshi, hajiya dake tsaye alhaji ya kalla Sannan yace
"Kinga illar sangartar da yaro...he can can't do anything on his own sannan kullum ga kuka kaman wata mace..kin maida min da kaman mace.." Alhaji ya fada sannan ya juya ya Koma cikin mota. Hajiya batace komai ba ta b'alla mashi harara sannan ta juya ta bi bayan suhail daya shiga part dinshi da gudu. Yana shiga ya shiga bathroom ya watsa ruwa, ko minti biyar baiyi ba ya fito daga bathroom ya tsaya daure da towel yana goge kanshi da daya towel, hajiya ce ta shiga har bedroom din tace
"Son hope in kaje zaka fada mata you love her...no more pretending.." Ta fada mashi. Dan murmushi ya saki Sannan yace
"Mommy let me see her first...Allah yasa in samu courage din fada mata..." Ya fada yana bude wardrobe dinshi, wasu expensive Jean da Riga ya Fiddo ya saka, hajiya fita tayi ta koma falo Tana tunanin Anya suhail zai dinga tunawa daita in ya samu wannan yarinyar a matsayin matar shi?.. Don Tana mamakin yanda zuciyar shi ta karkata kan ita kadai bai gaji komai sai ita, fitowa yayi looking cute and handsome saidai duk ya rame.  Mikewa hajiya tayi daga Inda take zaune ta kalleshi cikin so da Kauna,
"Zaka kwana chan?.." Ta tambayeshi,
"I don't know...kinsan banason zuwa katsina..sai ya zama dole so I ba lallai in kwana ba..." Ya fada yana gyara wuyar rigar shi.
"Hope kana da kudin fuel ..."
"Yes mommy.." Ya amsa mata, hannunshi ta Kama Tana cewa
"Muje kaci abinci kafin ka tafi...banason kaje kaci abinda zaisa kayi costipating.." Ta fada sounding so caring , murmushi ya saki yana cewa
"Mommy I can't eat...zan tafi..." Yafada yana taking steps zuwa bakin kofa, jiki ba kwari itama ta bishi duk ya sauya mata Yanzu she don't feel kaman da suhail dinta take zaune, it feels as she's together with a total stranger. Har bakin mota ta rakashi ya shige,
"Be careful with your hand...." Ta fada mashi yana tada mota
"I will mommy..I love you..."
"Love you more..." Ya fada sannan ya fita da mota aguje kaman yana race.
Chapter 43 · 0% Book details