← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 190

Sashe 36

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 4 min read

Da gudu ya hau upstairs yana hawaye, ji yake kaman ya cire zuciyar shi Saboda bakin ciki, he can't believe Yanzu Maryam bata cikin gidan, ganinta kawai gives him joy and happiness, yana zuwa bakin Kofar hajiya ya bude da karfi tare da banging kofan da karfi kaman zai balleta, da sauri hajiya dake kwance ta mike zaune, hankalinta bai tashi ba sai da ta ha hannunshi da wuka ya nufo inda take zaune kan gado, idanuwa ta zaro jikinta na rawa ta fara cewa
"eyeballs meye haka?" Ta tambayeshi cikin tashin Hankali Tana Jan baya Don a tunanin ta kasheta zaiyi sannan yanayin shi says so, suhail baice komai  ba ya karasa inda take zaune Tana ja baya ya ajiye wukan kan kafarta yana cewa
"Mommy in kinayiwa Allah da manzonsa ki karasa ni kawai hankalinki ya kwanta...I have nothing left tunda ki dauke min farincikina...." Ya karasa maganar cikin kuka, Sabon kuka hajiya ta farayi Tana kallon yanda suhail ke mika mata wuya yana hawaye,
"Yanzu eyeballs ni ba farin cikinka bace?..Yanzu suhail ka kalli idanuwana ka nuna min am not your happiness?.. Ni da na durkusa na haifeka...hakan adalcine..." Ta karasa maganar cikin matsanacin kuka, suhail shuru yayi yana hawaye ta cigaba dacewa
" suhail wannan yarinyar ba komai bace illa shaidan...she came to destroy our happiness...." Bata idaba suhail yace
" no mommy....I love her...I have never want anyone the way I want her....why can't you understand...." Ya fada yana kuka, Kai ta girgiza mashi Tana cewa
"Know...enchanting Dinka tayi...can't you see?... Me ta fi duk yan matan dake Sonka?... Nothing...wasu ma sun fita in everything amma just by ganinta ta Kama maka zuciya...pls baby kar mu Bari wannan yarinyar ta yi ruining farin cikinmu...tayi succeeding babanku zaiyi min kishiya...sannan yayi min saki daya..." Bata karasa maganar ba kuka yaci karfinta, duk sai suhail yaji bai ji dadin last statement dinta ba, asalima bai taba ganin misunderstandings tsakanin mom dinshi da dad dinshi ba, 
"Mommy ki bar cewa saboda ita kayi maki kishiya...lokacin né yazo..." Ya fada not crying amma face dinshi is wet da tears,
"No...itace sila...she's the cause of all my misfortunes..she brings sadness to our home..." Babu abinda suhail yake sai girgiza Kai yana nuna mata bai yarda da abinda yake cewa ba,
"Nidai mommy I love her...I can't stop my heart from doing so....kawai ki fadamin inda aka kaita If u want me to survive..." Ya shaida mata atakaice, daure fuska hajiya tayi Tana cewa
"Wai ki bakajin abinda nake cewa?... Nace ka manta daita..." Ta daka mashi tsawa, wukan ya dauko yana tura mata cikin hannunta yana cewa
"Saidai ki kasheni..amma ni wallahi I love her...in babu ita my life is hopeless..." Yafada yana tura mata wukan da karfi ita kuma taki amsa, Dayan hannunta ta dora bisa kanshi Tana shafawa ahankali, ahankali ya zame kanshi daga cikin hannunta ya mike ya bar mata wukan nan. Down stairs ya sauka  ya bude Kofar dakin Maryam,  jiki ba kwari ya shiga dakin, tsayawa yayi yana karewa dakin kallo, bakin gadon ya je ya zauna, babu kamshin abinda yake ji sai man shafawanta wato fair and white exclusive, zamewa yayi ya kwanta kan gadonta ya dauki pillow ya rungume Yana lumshe idanuwanshi, Dan cije lebenshi na kasa yayi yana saki ajiyan zuciya, tunanin Abu daya kawai yake, gurin shi a Yanzu shine ya samu dad dinshi ya fada mashi inda ya Kai Fatima yake chan ya fada mata what he's feeling about her sannan ba zai dawo gidan nan ba sai an sa masu biki Don gani yake since she's family ko dad Dinshi bai je ba za'a bashi ita, Kara rike pillow yayi gam tamkar Maryam ce ya rike. Ahaka bacci yayi gaba dashi.

Ita kam Maryam wacegari jikinta yayi tsami sosai Don ko tafiyar kirki bata iyawa saboda yanda duk joints dinta ke mata ciwo, bayan ta sha tea ta sha maganin ta sannan ta tsaya gaban mirror babu Kaya jikinta Tana kallon irin mark da hajiya ta bar mata a jikinta, Yanzu Tana tunanin in ta koma London bazata iya saka sexy dress kaman yanda ta Saba ba. Ahankali ta koma ta zauna tare da sakin ajiyan zuciya, she can't just wait lokacin birthday dinta yayi Don kullum in suna waya da dad dinta bah abinda take shaida mashi sai maganar zuwan ta kuma sai yace wannan ba wani Abu bane Kawai she should be a good gal. Yanzu sauran wata biyu birthday dinta and she's praying dad dinta yasa a maidata in in the next six weeks.
Chapter 36 · 0% Book details