← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 190

Sashe 27

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 7 min read

In silence suka isa gida kowanne su da tunanin dayake, suhail yana tunanin Maryam while ita kuma hajiya Tana  tunanin maganar da alhaji ya fada mata. Yau data dawo bata tsaya kiran masu aiki ba ta wuce dakinta, wayanta ta dauka tayi dailing number Alhaji, har wayan ta gama ringing ba'a dauka ba. Jiki ba kwari  ta ajiye wayan Tana cewa
"Wacece wannan yarinyan da alhaji ke yi min haka saboda ita?" Ta tambayi kanta Tana shiga bathroom.

Da yamma aliyu né ya shigo da motanshi cikin gidan, suhail dake zaune yayi saurin mikewa Don ganin Wanda ke shigowa Don already alhaji ya dawo, motan aliyu ya gani, haka nan sai yaji wani Abu nayi mashi yawo cikin ranshi, ko,kadan baison ganin aliyu, yana kallonshi ta window ya ga ya fito rike da leather a hannunshi. Hanyan part din suhail yayi aikam da sauri suhail ya maida kofa ya kulle, knocking yayi Amman ko mikewa baiyi ba balle ya bude mashi, juyawa aliyu yayi ya Kama hanyan part din hajiya. Ba kowa falo sai da yayi sallama da karfi sannan Binto ta fito tare da amsa mashi, gaidashi tayi ya amsa sannan yace
"Dan Allah Fatima Tana nan?..." Ya tambayeta,
"Eh Bari in kirawota..." Ta amsa mashi sannan ta juya ta Kama hanyan dakin Maryam, lokacin Maryam tayi wanka tayi sallah asar Tana zaune bakin gado, bayan minti biyar sai ta kalli fingers dinta, the more ta kalla the more Tana Jin haushin suhail. Shigowan binto yasa ta daga kanta,
"Wani na néman ki..." Binto ta shaida mata,
"Wa...ye..." Ta tambayeta cikin sanyinmurya,
"Abokin suhail né...amma ban San sunanshi ba...." Binto ta amsa mata, ahankali ta mike sanye da skirt da Riga, kanta babu dankwali, Tana tafiya cikin kasaita ta isa falo, aliyu ta gani tsaye, murmushi ta sakar mashi tare dacewa
"U should have called ai..." Ta fada mashi, shima murmushi ya sakar mata yana cewa
"Ai nazo kusa da nan né sai nace Bari in sayi ice cream in kawo maki Don kiji dadin licking..." Ya karasa maganar in a naughty way, Dan kura mashi Ido Maryam tayi Tana sauraron yanda yayi maganar, ledan hannunshi ya mika mata, ahankali ta mika hannu ta karba' tare da cewa
"Na..go..de..." Ta fada ahankali, murmushi ya Kara saki sannan yace
"Hope zaki sha da yawa Don gobe ma sai na karo maki..." Ya shaida mata
"Don't worry...wannan...ya...isa..." Ta fada mashi. Shuru né ya Dan biyo baya duk suna tsaye babu Mai cewa komai, bayan kaman minti daya aliyu yace
"Bari in tafi..tunda ko zama baki cewa Inyi..." Ya fada cikin zolaya, bata ce komai ba sai murmushi kawai da take, juyawa yayi yana cewa
"Na tafi...hope dai zakiyi min rakiya?..." Kai ta daga mashitana biye dashi, har lokacin Tana rike da ledan ice cream dake hannunta, suna fita daga cikin falon suhail yayi saurin komawa bakin window, daman tunda aliyu ya shiga bai zauna ba, sai Kai kawo kawai yake cikin dakin, ganin Maryam babu dankwali ko vail tattare daita yasa yaji kaman ya mutu saboda kishi da bakin ciki, hannu yasa zai bude Kofan yayi saurin cire hannunshi yana cewa
"Wai ni Ina ruwana...ya rabbi kar ka Bari wannan yarinyan ta samu nasara Kaina...na shiga uku..." Ya fada yana zama kan kujera, ji yayi yana son ganin abinda ke faruwa, Kara mikewa yayi ya koma bakin window, yana kallo Maryam ta raka aliyu har bakin Kofar motan shi ya bude ya shiga ya tafi, shima Salman yana zaune kusa da baba maigadi yana kallonta, sai yau ya Kara tabbatar da kyauwunta Don bai taba ganinta babu dankwali ba, aliyu na fita ta juya da niyyan komawa Ciki kawai sai taji Ana cewa
"Friend how far..." Salman ya fada mata, juyowa tayi ahankali ta kalleshi tare da sakar mashi murmushi,
"Duk yau...bamu...hadu...ba" Ta fada mashi, mikewa yayi daga inda yake zaune ya nufota yana cewa
"Yau munyi tafiya da alhaji..bamu dade da dawowa ba...yakike..." Ya tambayeta yana karasowa inda take tsaye. Suhail dake tsaye bak'in window yana kallon abinda ke faruwa ya ja tsoki yanacewa
"Ko me wannan banzan ke nufi?... " Yafada sounding very bitter. Kofa ya bude ya fita ya nufi inda Salman da Maryam ke tsaye. Maryam na ganinshi ta sha jininta , Fuskanshi daddaure yace
"Last time shine nace kayimin wanki kak'i kou..." Yafada yana nuna Salman da Dan yatsa, Maryam kallon Salman tayi Tana cewa
"Later...." Tadata mashi sannan ta juya ta barsu nan tsaye, bayanta suhail yabi da kallo, shima Salman juyawa yayi Don ya ga irin kallon da suhail yayiwa Maryam, sai Yanzu ya gane dalilin dayasa yakeson ci mashi mutunci a gabanta
"Kai kana haukane...inayi maka magana kuma kana tafiya?... Are you mad?.." Suhail ya fada a fusace, ahankali Salman ya juya tare dacewa
"Pls na rokeka...ka rabu dani...ba Kai ka daukeni aiki ba..." Gani yayi suhail ya nufoshi, da sauri yaja baya
"Who do you think you are da Ina magana kana magana...wato Kai kaga yarinya shine you have grown wings kou...." Ya fada har muryar shi na rawa saboda yanda yake magana. Salman dai ya gano abinda ke damunshi, still tafiya yayi ya barshi nan tsaye,
"Wallahi sai nayi maganinka..." Inji suhail, baki Salman ya tabe amma suhail bai gani ba. Juyawa suhail yayi ya Kama hanyan part din mom. Maryam na shiga ta mikawa baba rabi ledan da aliyu ya kawo batare data bude taga abinda ke ciki ba ta shige dakinta, kawai sai taji an bude kofa da karfi Tana daga Kai ta ga suhail tsaye
"Ke Dan ubanki daga yau na Kara gani kina magana da wani sai na ballaki...kinji kou sai na Maimaita?..." Ya fada sounding very harsh, banza tayi dashi tana mamakin why he cares, daga Kai tayi ta watsa mashi harara batare data ce komai Don gani take bazata taba Jin haushin wani kaman yanda take Jin haushin shi ba, kallon yanda take hararanshi yayi Amman sai yaji ko kadan he's not angry
"Zaki ci ubanki né...." Yafada yana barin dakin.

Bayan sati uku

Suhail ya Riga ya gane ya kamu da son Maryam, kuma irin over so yake mata amma saboda Hali irin nashi ya rasa ya zaiyi ya fada mata, har yau ita ke gyara mashi part, itace serving abincin shi Don in har ta tafi islamiyya baiyi breakfast ba to bazai ci komai ba har sai ta dawo, atakaice har inner wears yake bata ta wanke, kuma bata taba complain ba, in har ya Kai hour daya bai ganta ba kaman zai mutu yakeji, kullum yana rokan Allah ya cire mashi ita daga zuciyar shi Amman tamkar yana Kara sonta, hajiya ta gane da akwai abinda ke damunshi amma in Ta tambayeshi sai yace mata babu abinda ke damunshi, mostly Yanzu bai baccin dare sai tunani har friends dinshi  avoiding dinsu yake, babu abinda yake so sai yaga Maryam kusa dashi.

Shima Salman ya shaku da Maryam sosai Don Yanzu in zai kaita islamiyya sai sufi minti talatin a hanya suna labari, wani lokacin ma sai tace ya kaita yawo cikin gari, haka zasu shiga gari dashi har lokacin tashi daga islamiyya yayi ya maida ta gida. Har yau bai furta yana sonta ba ita kuma bata daukeshi amatsayin masoyi ba, kawai Tana daukanshi as friend wanda take Jin d'adin zama dashi.

Shima dai aliyu yana zuwa gidan time to time Amman ya rage zuwa saboda yanda suhail ke behaving Don yasan already sonta yake Amman bakin halin shi ya hanashi fad'a mata.

Shikam alhaji har an tsaida ranar auren shi da salima amma hajiya bata sani ba kuma bai nuna mata komai ba, ita kuma bata gane duk shirye2 da ake ba. Yau bayan ya dawo daga office yaci abinci ya Kira suhail, hajiya na zaune gefenshi. Da sallama ya shigo duk ya rame ya Dan rage haske, zama yayi kusa da kafan mom dinshi, hannu hajiya tasa ta Dan Shafa kanshi kaman wani karamin yaro, Kai ya daga ya kalleta tare da sakin murmushi karfin Hali, gyaran murya alhaji yayi before saying
"Hope Baka mance abinda nace maka game da aiki ko aure ba...wallahi am serious...ko ka fara aiki ko kuma kayi aure...wannan shine last time da zanyi maka wannan maganar...kana jina?.." Alhaji ya fadawa suhail, ahankali ya daga weak eyes dinshi ya kalleshi sannan ya sadda kanshi kasa,
"Wai bakajin abinda nace?.." Alhaji ya daka mashi tsawa, da sauri yace
"Dad...ni aure...nakeso..." Yafada atakaice, kallon mamaki hajiya tayi mashi Don ko sau daya bai taba yi mata maganar yarinya ba,amma dad wasn't surprised, shuru né ya Dan biyo baya for like 10 seconds sannan alhaji yace
"Shikenan..ka fadawa yarinyan zaka turo..." Ya fada mashi yana kwantar da murya Don babu abinda alhaji ke so kaman yaga suhail yayi aure yasan dole ya yi aiki in dai yayi aure.
"Ai...daddy...Fatima...nakeso..." Ya fada kanshi kasa.

See you in next page. Love you
[11/27, 11:07 PM] ‪+234 706 639 9737‬: 12💜💙❤️💛💚
Wulakanci dodone...
❤️💛💙💚💜

®zuwairat (ummumaryam)

1️⃣2️⃣
Chapter 27 · 0% Book details