← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 190

Sashe 113

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 11 min read

Bacci suhail yasha har lokacin sallah zuhr Sannan ya mike yayi wanka yaje masjid yayi sallah a dawo, ji yayi yana Jin yunwa kuma yasan ko ya Kira number Maryam ba daga wa take ba, part din salima yaje ya gaisheta yana cewa
"Anty Ina Fatima,,,Wallahi yunwa nakeji..." Yafada mata, salima murmushi tayi tace
"Bari in dauko maka abincin,,..ta fita kuma har yanzu bata dawo ba.." Nan da nan suhail yaji kaman numfashinshi zai dauke,
"Anty Ina taje?" Ya tambayeta kaman he's not boiling Don babu abinda yake tunanin sai Tana tare da Salman, goshinshi ya dafa ya saki wani nishi kaman Mai asthma yace
"Pls anty ya akayi kika Bari ta fita?..Haba anty,.," ya fada yana jefa kanshi kan kujera,
"Ka kwantar da hankalinka...bata dade da fita ba...nasan ta kusa dawowa..." Salima ta fada mashi cikin taushin murya,
"Anty Dan Allah Ina taje?.." Ya fada numfashinshi sama sama,
"Kai dai Yanzu ka kwantar da hankalinka Kaci abinci..." Bata idaba suhail yace
"Anty abinci fa kika ce?.. Ina ni Ina cin abinci Yanzu...Wallahi duk hankalina tashe take...in dad yasan kina Bari Tana fita sai rasnhi ya bace...anty Dan Allah ki dinga hanata fita..Dan Allah..." Ya karasa maganar cikin tashin hankali,
"Ai yarinyar ce da kafiya..."
"Nidai pls ba fun karfin ki tayi ba...nidai kiyi min alkawarin bazaki sake barin ta ta fita ba..."
"Tou nayi maka...amma Yanzu ka bar damun kanka...Bari in dauko maka abinci"..da sauri ya girgiza Kai yana cewa
"Anty da Salman ta fita kou?.." Ya tambayeta,
"Eh ..! Ta amsa mashi atakaice, wani irin ajiyan zuciya ya saki Sannan yace
"Wayyo Allah my heart...anty Yanzu haka zan zuba Ido Salman ya kwacemin yarinyar da na fi kaun?.." Kai salima ta girgiza mashi tace
"Wannan ba shi zai nuna alaman kwacewa ba...Allah na gani Kai ka nuna kana sonta...zabi ya rage nata..."
"Anty in ta zabi Salman fa?.. Anty mutuwa zanyi...kilan ban ma tafiya Dubai..." Hannu salima ta daga mashi ta katseshi dacewa
"Haba suhail..ka bar fadin hakan...Kai dai kayi adua...Allah ya zubawa kowa abinda yafi alkhairi.." Salima ta fada mashi, shuru suhail yayi yana nishi sama sama, sai shaking kafa kawai suhail yake zuciyar shi na tafasa, kawai gani yake kaman Salman yana Chan yana wani Abu da Maryam Don yasan ba kowanne namiji zai samu irin daman da yake samu da Maryam without taking advantage ba, mikewa salima tayi Tana cewa
"Bari In dauko maka abinci..."
"Ki bar maganar abinci mana..." Ya fada yana kwantawa kan kujera. Har Karfe uku da minti ashirin suhail na nan, yau dai ya dage baiyi kuka ba amma inda zaiyi kukan sai yafi samun sauki Don kukan zuci azaba né, sai sauke ajiyan zuciya kawai yake kaman Mai labor, mikewa yayi ya fara takawa yana Kai kawo. Fita yayi yayi alwallah Don tafiya compound, yana kan hanyar zuwa masjid ya hadu da motar Salman ya taho. Maryam na gani suhail taji yan hanjinta sun tsinke saboda tsoro, shi kam suhail daddaure fuska yayi Sannan yana aduar Allah yasa kar ya kalli inda suke balle ya aiwatar da bai da yake aiyanawa a ranshi, ahankali Salman yazo wuceshi da mota, suna wucewa Maryam ta saki ajiyan zuciya da yasa Salman kallon ta, shima suhail ajiyan Zuciya ya saki yana cewa
"I don't know I can do this,.,alhamdulillah" ya fadawa kanshi yana tafiya, ko juyowa baiyi ba har ya Kai masjid, ita kam Maryam bata tsaya biyewa maganar Salman ba ta fito ta shiga ciki, Tana shiga salima ta bita da tambayoyi, cikin natsuwa Ta amsa mata Sannan ta shiga ciki tayi alwallah tayi sallah zuhr da asar, sai tunanin abinda suhail zaiyi mata kawai take Don she knows what he's capable of, gabanta na faduwa ta dawo falo ta kalli salima tace
"Anty suhail ya shigo né?.."
"Eh..ya akayine?.." Ta tambayeta, da sauri tace
"Anty yaci abinci?.." Ta tambayeta, baki salima ta tabe Sannan tace
"Nima ban sani ba...ki tambayeshi mana..." Ta fada cike da Jin haushin ta, ahankali Maryam ta shiga kitchen ta ga abincin shi is set kaman yanda aka Saba yi mashi, da sauri ta dauki abincin ta fita daga part din. Sai sauri kawai take, Tana shiga ta tarda suhail kwance yayi folding hannunshi a kirjinshi idanuwanshi sun sauya saboda bakin ciki, da sallama ta shigo voice dinta na cracking, idanuwa ya lumshe ya Dan sauke ajiyan zuciya ya amsa mata without saying another word, kan dining ta nufa amma ears dinta na kanshi ko zai mike unexpectedly or say something amma har ta gama jera abinci baice komai ba, Tana gamawa ta kalleshi da scaring eyes dinta tace
"Na gama..."
"Ok nagode"".ya fada cikin sanyinmurya Sannan ya mike ya nufi dining babu abinda gabanta yake sai faduwa amma to her surprise no words ko daya, haka nan sai kuma taji babu dad because she was expecting suhail to do what suhail does best, yana zama itama ta ja kujera zata zauna sai yace
"Yau na hutar dake...I don't have to wait har in gama cin abinci..." Ya fada calmly yana daukan spoon, murmushi ta saki tare dacewa
"Are you sure?.."
"Yap..." Ya fada kaman babu abinda ke damunshi,
"He has given up kenan." Maryam ta fada cikin ranta,
"Ok..anjuma zan dawo kwace plates..." Ta fada sannan ta fita, Tana fita yayi saurin mikewa yana sauke ajiyan zuciya tare dacewa
"I did it...ya Allah..ya Allah...oh basan I can do it ba...wayyo Allah na..." Ya fada yana dafa zuciyar shi da karfi, abincin dake kan dining ya kalla ya daukosu ya juye cikin dustbin dake nan dakinshi ya maida plates kaman shi ya ci ya koma yayi kwanciyar shi, ita kam Maryam sai tunanin suhail take saboda ya bata wani irin cold attitude da bata sanshi dashi ba, kallon agogo tayi tace
"I will go back in the next twenty minutes.." Ta fadawa kanta. Bayan kaman minti ashirin ta koma part dinshi, da sallama ta shiga ya amsa kaman he's not dying inside, baki ta bude Tana kallon plates babu ko kwara abinci daya sama kaman yanda ya saba barin kusan rabin abinci cikin plate ba, kallon shi tayi tace
"Kam yau kayi kokari...ka cinye duk abincin,..," Ta fada Tana tattare plates,
"Aikam..." Ya amsa mata ba ko kalli inda take ba, plates ta dauka ta fita, juyawa yayi yabi bayanta da harara. Still dinner na baici ba, wajen mom dinshi yaje suka sha labari, Yanzu dai he's learning to solve his problems alone, ko kadan bai fadawa mom komai ba. The following day ya shirya ya fito Don zuwa wajen family dinshi yi masu bankwana, daga part din hajiya ya shiga part din salima, nan ya tarda Maryam Tana breakfast ita kadai,
"Sai Yanzu kike breakfast?.." Ya tambayeta,
"Yes I woke up late tunda babu islamiyya...," Ta amsa mashi Tana cin abincin ta,
"Ina anty?.." Ya tambayeta, yana kallon yanda take Shan tea kaman Tana tausayina cup din,
"She's inside...bata Jin dadi..." Ta amsa mashi,
"Ok...in ta fito ki fada mata na tafi bankwana da sauran families..." Ya fada yana juyawa,
"ok..." Ta amsa mashi atakaice, har ya Kai bakin kofa tace
"Allah da zaka iya jirana na Dana bika...I want to be going out more often...har Yanzu ban San koina nan garin ba..." Ta fada Tana Shan tea kaman ba ita tayi magana ba, juyowa yayi yace
"In kinaso zan jiraki sai ki gama mu tafi tare..amma har katsina zani fa.." Ya shaida mata,
"Kawai ka tafi..am not fast in dressing..."
"Ke dai yi sauri...let me wait for you..." Ya fada yana komawa kan daya daga cikin kujerun,  tea ta gama sha ta mike ta shige ciki, tafi minti talatin bata fito ba, salima ce ta fito suka gaisa ya tambayeta abunda ke damunta, nan take fada mashi fever ke damunta, sannu yayi mata ya zauna yana jiran fitowan Maryam, sai kusan hour guda ta fito, abun mamaki ko kwalliya batayi ba ta fito sanye da long gown sai dankwali da ta yafa kanta kaman vail, hannunta dauke da waya, kallon salima tayi tace
"Anty ya jikin?.."
"Da sauki...Ina zuwa kuma?."salima ta tambayeta,
"Anty zanbi suhail né..."
"To a dawo lafiya...a yo min tsaraba..." Ta fada batare da ta nemi Jin inda zasu ba, mikewa suhail yayi yace
"Anty me za'a kawo maki...." Ya fada yana daukan car keys dinshi,
"Komai ma...nidai in anci a rage min..." Ta fada masu. Waje suka fita ya bude mata mota ta shiga shima ya shiga suka bar gidan, maimakon yaji dadi haushi kawai yake ji wai Salman ya dauketa jiya, bai gama tunani ba sai wayarta ya fara ringing, picking tayi Tana cewa
" the ceo of Salman international appliances how far..." Ta fada hankalin ta kwance, suhail kwantar da hankali yayi ya cigaba da tuki while ita da Salman suna waya, sun kusa hour suna waya, gaban wani gida taga yayi slowing down tare da horn,  sai lokacin tayi sallama da Salman ta kalleshi tare dacewa
"Ina né nan?.." Ta tambayeshi banza yayi kaman baiji ba yana horn da karfi saboda haushi da bakin cikin wayar da ya saurara tsakanin ta da Salman, Kawai he's thinking in yana iya mantawa  da ita zai fi mashi alkhairi, 
"Wai inane nan ...Ina tambayanka kayi banza Dani..." Ta fada cikin Tsiwa, baki ya tabe Sannan yace
"Gidan yankan Kai né..." Ya fada ya yin da maigadi na bude mashi gate, shiga yayi tare da parking, wani irin kallon haushi tayi mashi Tana kallon environment din, wasu yara ta gani  suna wasa, gaida shi sukayi ya amsa yana cewa
"Ina su mommy da ?.." Ya tambayi yaran,
"Anty Aisha Tana ciki mommy kuma taje unguwa..." Daya daga ciki yaran ta amsa mashi, bai Kara cewa komai ba ya shiga ciki Maryam na biye dashi, suna shiga falon wata black beauty ce zaune,  Tana Jin sallama tayi saurin daga kai saboda muryar dataji, da sauri ta mike Tana cewa
"Yaya...sannu da zuwa...,"Ta fada jikinta na rawa, sai lokacin ta ga Maryam sai yanayin ta ya dan sauya, murmushi ya sakar mata tare da cewa
"Yauwa...ya kike ya school..." Cikin sanyinmurya tace
"Lafiya lau yaya..." Wuri ya samu ya zauna itama ta zauna Tana kallon yarinyar, da sauri ta nufi wani waje ta dauko drinks ta ajiye masu, tare da cewa Maryam sannu, sha suhail yayi ya ajiye cup din ya mike ya nufi inda Aisha take ya Kama mata hannu ta mike yana cewa
"Zo muyi wata magana.." Ya fada mata cikin sweet voice, Maryam bin bayansu tayi da kallo har sukayi wani daki, suna shiga ya saki hannunta tare dacewa
"Aisha.." Ya kirata cikin sanyinmurya, Aisha da duk ilahirn jikinta ya mutu Don tunda take bata taba Jin maganar suhail ba balle murmushin shi har ya kaiga Kama mata hannu duk da they're cousins,
"Naam..." Tafada kanta kasa,
"Nasan nayi maki laifi...nayi maki ba daidai ba...kin soni amma babu abinda nake maki sai Wulakanci...Dan Allah ki yafe min...kuma ki San cewa komai sai in Allah ya amince...Allah né bai yarda da relationship din mu ba...so pls ki yafemin...Sannan nasan Allah zai baki Wanda ya ninka ni in any aspect of life..." Ya karasa maganar cikin sanyinmurya, yarinyar daga Kai tayi sai yaga face dinta shrkaf sa hawaye,
"Yaya ni wa zan samu in so shi kaman yanda nake sonka?.. Na yafe maka duk abinda kayi min amma ko yau na mutu i died with you in my heart..." For the very first time ya tausaya mata saboda yasan exactly what she's going through, shoulder dinta ya Kama ya jawota jikinshi yana cewa
"Nima am going through what you have been going through...Inason yarinyar da bata sona...nasan har da alhakinki...I just wish Ina iya switching heart Dina ya dawo gareki..amma hakan ba Mai yuwa bane...pls am sorry...I know you have suffered because of me...kiyi hakuri..." Yafada yana Shafa kanta, rungume shi tayi Tana kuka, Shafa kanta ya dingayi yana cewa
"Let it out...zaki ji sauki..." Yafada yana Jin yanda kirjinta ke danne da nashi, sunfi minti shabiyar ahaka, sai da yaji ta daina kuka Sannan ya daga kanta ya goge mata face yana cewa
"Na samu aiki a Dubai...zan tafi nan da 3 days...in su daddy da mommy su dawo ki fada masu...and pls pray for me..." Yafada wearing a smile, murmushin karfin Hali ta saki Sannan yace
"All the best yaya...,"
"Ameen sis..." Ya fada sannan ya Kama hannunta suka fito, Maryam kam wani Abu taji Wanda Batasan ko meye ba...she feels like strangling both of them, fuskar ta Sam babu walwala, Tana ganin sun fito ta mike tayi waje, bata jira yazo ba ta bude mota ta shige ta harde hannuwanta a chest dinta, hannunshi cikin na Aisha har sukazo wajen motar, budewa yayi ya shiga ya bar gidan ko kallon inda taje baiyi ba balle yaga yanda ta hade rai, kawai she's feeling yanason humiliating dinta né. Har suka Kara isa wani gidan babu word ko daya tsakanin su. Duk saida sukaje gidansu Sadeeq, aliyu da Yusuf yayiwa iyayensu bankwana, Maryam kam ko fita batayi daga cikin motar balle ta Kara ganin abun takaici, shi kuma baiyi forcing dinta ba, wajen Karfe biyu ya Kama hanyar katsina,
"Pls take me back home...na gaji haka nan..." Ta fada lokacin dataga tafiya Kawai ake babu tsayawa, kallon yayi yace
"Tou..." Amma ya cigaba da tafiya abun shi.
Chapter 113 · 0% Book details