← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 190

Sashe 127

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe biyu suhail ya fito, tafiya kawai yake suit dinshi rataye kan shoulder dinshi, office din humaira ya shiga ya tardata Tana waya amma yana shiga tayi saurin cewa
"Excuse me..." Sannan ta ajiye wayar ta kalleshi tare da mikewa,
"Hi sir..." Ta fadawa suhail, karasowa yayi yace
"Hi...am closing for the day..."
"Ok sir...," Ta amsa mashi cikin sanyinmurya, ficewa yayi bai Kara cew komai ba, yana zuwa gida ya tarda Mai aiki Tana ta aikinta, tambayanshi tayi abinda zaici sai ya amsa da he's eating out. Bedroom ya shiga ya wulla kanshi kan gado, right now he's regretting two things, na farko yin maganar ta jiya sai na biyu Kiran anty salima, Don ji yayi all the memories he's blocking are rushing back, wayar shi  né ya fara ringing, bai duba ba Amman yasan mom dinshi ce, ko daga Kai baiyi ba ya latsa accept,
"My love ya kake,.." Ta tambayeshi
"Fine mommy good afternoon.., " ya fada sounding worried,
"Sweetheart what's wrong with you?.." Ta tambayeshi Don he sounds so worried,
"Am ok mom...kawai gajiyar aiki ce..." Ya fada mata,
"My working class boy...holidays yazo fa...when should I expect you.." Hajiya ta fada mashi, juya kwanciyar shi yayi yace
"Ai mommy da wuya in samu zuwa..." Bai karasa ba hajiya tace
"Me hakan ke nufi?.. You mean after 8 months bazaka zo gida ganina b?.." Ta tambayeshi cikn bacin rai, dariya yayi yace
"Mommy its 6 months...not 8.."
"Six months din ubanka?..tou kwana daya né nace inason ganinka ai ya kamata kazo...balle this holiday season...kowa Hutu zaiyi har kusan two to three weeks...sai kayi zaune nan bazakazo gida ba?.." Ta fada sounding so angry,
"Mommy aiki nake sosai...bani da Hutu..."
"Karya kake...Wallahi you're lying...wait a minute...ubanme kake achan?.. Because I have begin to suspect you..."da sauri yace
"wallahi mommy babu komai...kawai ..." Still Kara katseshi tayi dacewa
"Babu wani nan...kilan ka fara bin mata an am not important to you anymore..." Cikin tashin hankali yace
"Wayyo Allah mommyna...Wallahi it's not like that..alhaji Mahmoud né ya sani wata aiki ta musamman..." Kara katse shi Tayi tana cewa
"Still karya kake,..nasan babu Mai saka aiki during holiday period...kawai let me make one thing clear..tunda Yanzu you're too busy ai shikenan...ni zan zo ganinka...ai shikenan..." Ta fada mashi atakaice, zai bude baki yayi magana sai yaji ya katse wayar, kiranta yayi wayar ta dinga ringing amma bata daga ba, sake Kira yayi sai wannan lokacin ta daga Tana cewa
"What again..." Da sauri yace
"Mommy Wallahi it's not what you think..saboda Fatima né banason zuwa gida..."
"Wacece Fatima kuma?." Ta tambayeshi Don tunda suhail ya tafi ta mance zance wata Fatima Sannan ko sau daya basu hadu daita gidan ba, kowacce harkar gabanta take,
"Hmmm mommy har kin mance Fatima?.."
"Oh...na tuna..wato it's because of her bazaka zo gida ba?.. Kana haukane zaka bar gidan ubanka saboda wata bare?..."
"Mommy u don't understand..." Katseshi tayi dacewa
"Make me understand Dan ubanka..." Ta umarce shi, ajiyan zuciya ya saki saboda yanda yake sensing tensions din mommy dinshi,
"Mommy remember baki da gurin daya wuce in mance ta..." Ya fada cikin sanyinmurya
"Ina jinka.." Hajiya ta fada atakaice, ahankali yacigaba dacewa
"Yanzu na fara manceta...kuma nasan in nazo gida zan iya sake fadawa tarkon sonta...shiyasa banason zuwa.." Ya karasa maganar hoping she will understand,
"Amman ba San haka kake ba,,,wato saboda wata shegiya zaka yardani kenan...in shekara dari zatayi gidan nan bazaka Kara zuwa gida ba kenan...oh my gosh..am so disappointed in you...rubbish..." Ta fada ta sake katse wayar ta, suhail hada Kai da gwiwa yayi not knowing what to do. Maganar gaskiya yasan he's mom and humaira are right Don yasan he can never run away for ever amma babu abinda yake sai fargaba, yasan seeing her again will hurt him like hell Don maganar da yayi da humaira da kuma voice dinta dayaji yau ya sa shi cikin matsala balle kuma in ya ganta in flesh and blood. Maganar humaira né ya fara fado mashi na he has to be strong and he should prove to her he's over her,  ajiyan zuciya ya saki yana cewa
"Ina Iyawa?.." Ya tambayi kanshi,
"Ya rabbi I have gone through enough for my mistakes...ya rabbi give me free heart...na sha wuya..I want no more..." Ya fada ahankali yana komawa ya kwanta.

Bayan kwana uku Salman né zaune cikin mota da Maryam, hirar ai kawai suke cikin kwanciyar hankali, sai shagwaba kawai take zuba mashi kaman yar jaririya and he's loving it, in ya kalleta sai ya saki ajiyan zuciya Dom babu tunanin da yake sai tunanin mission accomplished, daman gurin shi na farko is ta so shi and it works perfectly, sai second mission which is marriage, shi kanshi Salman ya Chanza sosai Don duk Wanda ya ganshi yasan yana cikin Hutu, ni Kaina da kyar na ganeshi saboda yanda fatar jikinshi ke salki dukda he's black,
"Babu zan wanke Kaina.." Ta fada Tana tura mashi baki kaman zatayi mashi kuka,
"Ni Wallahi I love this your shagwaba...it's killing me..." Ya fada mata, murmushi ta saki Tana lumshe idanuwa
"Yanzu ya zaayi?.. In koma shago sai yarona yazo ya kaiki? Ko yaya?." Ya tambayeta cikin kulawa, marairaice mashi tayi Tana cewa
"Ni nafison ka kaini da kanka..." Ta fada mashi,
"But baby kinsan banason barin shop Yanzu,saboda most Kayan Dana kawo ba'a saukesu ba....kawai nayi missing dinki né sosai yasa nazo Sannan I have a special something for you..." Ya fada yana saka hannunshi cikin aljihunshi, baki ta tale Tana cewa
"Yanzu the shop is more than me kenan?.." Dariya Salman yayi yace
"No way...baki tambayi meye abinda nace zan baki ba..." Yafada yana kokarin zaro hannunshi daga cikin aljihunshi, baki ta turo tace banaso...ka bar ko meye...ni Kai nakeso ka kaini saloon.." Ta fada Tana harde hannunta a kirjinta, dariya yayi tare da Kama cheek dinta da free hand dinshi yace
"Just wait and see..." Bai karasa ba ta murguda mashi baki alaman what's my business,
"Pls close your eyes.." Ya umarceta, harara ta wulla mashi alaman no,
"Pls mana..." ya fada cikin lallami, sai lokacin ta lumshe idanuwanta, hannunshi ya fiddo daga cikin aljihunshi ya bude abin zobe dake hannunshi Sannan yace
"Open your eyes.." Ya umarceta, ahankali ta bude idanuwanta, to her surprise zobe ta gani Mai diamond, baki ta bude tare da rufe bakinta da hannunta tace
"Wow it's beautiful...", murmushi ya sakar mata Sannan yace
"Not as you...you glow more than this diamond...pls will you marry me..." Ya tambayeta Kai tsaye, idanuwa ta sake zaro abunka da tashin turai tasan value din such things, shuru tayi idanuwanta cikin nashi ta rasa abinda zata ce
"Pls remember my marriage proposal is with you...pls choose me...kar Kia zabi wani..." Taji muryar suhail na yawo cikin kanta, da sauri ta lumshe idanuwa trying to do away with the thought,
"Pls don't say no..." Salman ya fada mata cikin Sanyinmurya, sake kallon shi tayi tace
"Pls...can you let me think about it?.."
"Oh my God...Yanzu Fatima after six months of relationship sai kinyi tunani kan proposal dina?... Meye hakan ke nufi?. Does it mean you don't love me?..pls don't do this to me..." Ya fada kaman zaiyi mata kuka, da sauri tace
"Ba haka bane..,kawai I need to think né...pls don't misjudge me..." Ta fada mashi cikin sanyinmurya, Kai ya girgiza Sannan yace
"Ai if really you love me you don't need to think...you should have been waiting for this day...ko dai sa akwai wani ban sani ba?.."Kai ta girgiza mashi tace
"Nobody..."
"Then pls accept my proposal...kar ki watsa min kasa a Ido..." Kallon shi tayi for a moment Sannan ta mika mashi yatsa, da sauri ya Zira mata zoben a engagement finger dinta Sannan ya Kai hannun baki shi yayi kissing dinta,
"I love you..." Ya furta mata,
"Love you too..." Itama ta amsa mashi, wata Leda dake bayan mota ya dauko Sannan ya bude mota ya fita, Maryam kasa fita tayi ta zauna Tana kallon zoben dake hannunta, sai murzawa kawai take ahankali, ji tayi ya bude mota, jiki ba kwari ta fito,
"Baby Ina zuwa shago zansa a zo daukanki...in kin gama sai a kawoki shago in gan kalan da akayi maki...hakan yayi?.." Ya tambayeta, ahankali ta daga Kai ta kalleshi tare dacewa
"A barshi kawai...I don't think zanyi Kaina yau..." Ta amsa mashi kanta kasa,
"Nope...I insist..yau nakeson kiyi..Don haka zan aiko daya daga cikin yarona" Yafada mata sounding so commanding, bata Kara cewa komai ba ta Kama hanyar shiga gida, Leda dake hannunshi ya mika mata Ta amsa ta shige, haka nan she's feeling so down for no good reason. Tana shiga ta gwadawa salima zoben da Salman ya bata,
"Na meye wannan?.." Salima ta tambayeta Tana yatsine fuska,
"Proposal né..." Baki salima ta bude Tana kallon zoben Tana cewa
"Wato kin amince kenan?.." Salima ta tambayeta, shuru Maryam tayi Tana kallon zoben hannunta,
"Tab lallai...naga yanda za'a yi ki aureshi...sai mu jira muga in alhaji zai aurar dake ga wannan tsohon driver...." Ta fada cikin tsananin bacin rai Tana mikewa. Shigewa daki tayi itama Maryam ta shiga dakinta. Karfe biyu aka zo daukar ta, sanye cikin long hijab ta shiga dakin salima tayi mata sallama zata je saloon, ko kallon inda take salima batayi ba balle tayi mata magana, ficewa tayi ta shiga bayan motar Wanda Salman ya turo ya tafi daita.
Chapter 127 · 0% Book details