← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 190

Sashe 56

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 7 min read

Suhail na shiga part dinshi ya Kira hajiya ya shaida mata bazai iya zuwa piçking dinta ba saboda bai Jin dadin jikinshi, ba ce komai ba amma tayi deciding ta saboda driver dinta saboda her suhail is no longer reliable. K'aya ya cire yayi wanka ya fito da alwallah yaje yayi sallah ya dawo. Kayan jikinshi ya cire ya rage daga shi sai shorts ya kwanta bedroom tare da rufa kanshi da blanket Don da gaske he's feeling weak, waya ya dauka ya Kira Maryam yana fada mata he's really sick wai she should soothe him to sleep, kwantar da murya tayi suka dinga waya har bacci yayi gaba dashi. Salima ce ta shigo Tare da shaida ta zo ta kaiwa suhail pepper soup dinshi, Dan turo baki tayi Sannan tace
"Pls Baraka ta Kai mashi mana...na gaji fa.." Ta fada mata, Dan dariya salima tayi sannan tace
"Ita ma barakar tsoron zuwa take..tace yace zai yanka in Ta sake shiga bangaren shi..Don haka kiyi hakuri kizo ki Kai mashi..." Salima ta fada mata, kaman bata so ta mike ta fita, daukar basket tayi ta fita Tana cewa
"Na kusa hutawa...because when am through with you ko Mai Kama dani bazaka so gani ba..." Ya dada tana fita daga part din salima. Part dinshi ta shiga luckily yau bata ganshi falo ba balle ya ce sai ya gama Sannan ta fito. A kan dining ta ajiye mashi sannan ta fita abinta.

Yau aka saka bikin sadeeq, guys né sunfi su goma zaune a part din sadeeq dake gidansu, wata wakar usher Raymond da Chris brown Mai taken new flame ke tashi, duk Wanda ya gan guys din yasan yan Hutu né Sannan kowanne naji da kanshi, rawa suke daya bayan daya, in wannan yayi sai ya koma ya zaune wani yayi, suhail na zaune yayi relaxing idanuwanshi rufe hankalinshi Sam ba'a jikinshi yake ba, kawai he's wishing shi aka sawa biki Don bai taba bukatar aure kaman yanda yake ba Yanzu, duk sanda zasuyi waya da Fatima sai yaji kaman ya daukota daga cikinwayan yayi romancing dinta to his satisfaction, her voice alone make him horny, bai San irin wannan jaraban ba, Don dai Allah  ya taimakeshi he's strong in prayers da bai San abinda zai biyo baya ba Yanzu, ji yayi Ana
"Suhail!!!suhail!!!..." Sai lokacin ya bude idanuwanshi ahankali,
"Ita your turn..." Yusuf ya dada mashi, Dan  tsoki yaja ya maida idanuwanshi ya rufe,
"Ko sai mu sa ,mashi sorrow song né..tunda baison na ji dadi?.." Inji daya daga cikin guys din, duka dariya suka yi Banda sadeeq speak aliyu,
"Pls don't stop the fun...ka tayi ka taka ko step biyu né..." Inji Yusuf, ahankali suhail ya daga hannu yayi mashi alaman aa,
"Mufamatsalar mu da wannan gayen kenan..duk abinda zaayi sai ya nuna ego and pride..." Inji wani guy dake cikin su, ahankali suhail ya bude idanuwa ya kalli gayen from head to toe bai ce komai ba ya maida idanuwanshi ya sake rufewa cikin ranshi yana cewa
"Bakusan what am going through bane...da kun sani da Baku matsamin ba..." Ya fada cikin ranshi,
"Kun gani kou?... Ko magana ba zaiyi ba because he thinks he's better than us..." Inji wani, suhail zai bude baki yayi magana sai sadeeq yayi saurin cewa
"Ku kyaleshi..he's not feeling well..." Ya tare mashi, dariya wasu guys biyu sukayi Sannan daya daga cikinsu yace
"No wonder wannan gayen yana haka....Ashe ku kuke daure mashi gindin da ko a hanya ya ganka Baka isa magana ta hadaka dashi ba..." Suhail ji yayi in ya tsaya wurin zasu sake bata mashi rai fiye da baccin ran daya  ke ci, ahankali ya mike ya taka yaje kusa da sadeeq ya rada mashi magana a kunne, hannu sadeeq ya daga yayi parting bayanshi ahankali Sannan suhail ya fita daga falon yana kada keys ahankali.

Yau sauran 14 days birthday din Maryam, a bangaren alhaji Mahmoud kam wata irin special arrangements yasa akayi before her arrival, komai na dakinta saida aka Chanza, sannan ya sayi new and latest porches amma baizo daita gida ba aka bar shi nan inda aka saya sai ranar birthday dinta a kawota gida, wata part na gidan alhaji Mahmoud yasa aka zuba new design furniture saboda bakon sa Maryam tace tanaso yaso, alhaji Mahmoud has always promised himself cewa who ever is special to his daughter will be like his son, so Yanzu da Maryam tace tanason wani yazo he's thinking he's special shiyasa and abun farin cikin ma shine he's from Africa a African ma a Nigeria kuma a arewa so he's so super duper happy.
Kiran alhaji Ismail yayi ya sane dashi cewa zai aiko a dauki Maryam gobe and yana so ya kaita airport da kanshi, gaban alhaji mugun faduwa yaji din gani yake Maryam sai Yanzu ta fadawa dad dinta abinda akayi abaya,
"Why sir..." Shine tambayan da alhaji Mahmoud yayi mashi, dariya alhaji Mahmoud yayi Sannan yace
"Kaman kun shaku da princess Dina kou..." Ya tambayeshi, cikin karfin Hali alhaji Ismail yace
"Sosai ma..Tana da shiga rai sosai..." Inji alhaji Ismail, dadi alhaji Mahmoud yaji
"Well ka kwantar da hankalinka...I promise her zatayi celebrating birthday Dinta anan...after that she's coming back to Nigeria..." Ya fada mashi, sai lokacin alhaji Ismail ya samu sukuni,
"Masha Allah..." Alhaji Ismail ya fada hankalinshi kwance,
"So Dan Allah gobe ka kaita airport za'a zo daukanta kuma pls don't tell her...so that she won't disturb you din nasan halin kayana.." Inji alhaji Mahmoud,
"Babu matsala...yanda kakeso haka zaayi..so babu zancen parking kenan..." Inji alhaji Ismail,
"Aa...kawai ko ma meye tazo dashi babu matsala...and nagode da amanata da ka rike...Allah ya rufa maka asiri duniya da lahira...." Alhaji Mahmoud ya fada mashi,
"Ameen boss..thank you for trusting me..it's really a pleasure to have such personality in my house...nagode kwarai din ko ba komai zan iya cewa Maryam Mahmoud shugaba ta zauna gidana for a while..." Alhaji Ismail ya fada, dariya alhaji Mahmoud yayi sounding so happy,
"Yanzu dai zan bawa pilot number ka...da ya Iso zai kiraka sai ka kaita..."
"Ok sir..." Alhaji Ismail ya amsa mashi. Sallama sukayi alhaji Ismail ya ajiye waya yana tunanin halin da suhail zai sake shiga if she left.

Ita kam Maryam tunda taga birthday dinta sauran sati two amma babu bayani hankalinta ya tashi Don gani taje dad dinta have con her. Yau Tana zaune bakin gadon ta sai kuka take ba Don saboda birthday dinta ba sai Don plan dinta on how to handle suhail, gani take in har batayi abinda tayi niyya ba she will never revenge Don she never plan to forgive him for anything in the world, Tana cikin kukan wayarta ta dau Kara, tasan mr I love you né so bata daga ba because she's not in the mood to talk, Kira kawai yake amma bata dagawa, da karshm ma kashe wayar tayi saboda haushi da bakin ciki. Achan bangaren suhail kasa zaune yayi, yasan something is very wrong Don Yanzu ita ke kiran shi in taji shuru amma Yanzu ya jera mata miss calls da yawa bata dauka ba kuma at last her phone was off, mikewa yayi daga kan gado sanye da Kayan bacci Riga da wando, kallo agogon dakin yayi yaga after 8, komawa yayi ya zauna Don bai San ya zaiyi ya ganta ba Sannan he can't go there da dare, rasa abinyi yayi, sake mikewa yayi ya Chanza Kayan jikinshi zuwa three quarters da singlet, fita yayi dagapart dinshi zuwa part din hajiyarshi, yana shiga yaga babu koma falo, hanyar upstairs yayi sai kuma ya tsaya yana cewa
"Wai me zanyi upstairs kuma?.." Ya tambayi kanshi kaman wani Mara hankali, sauka yayi ya Kama hanyar kitchen yana cewa
"Let me see if those kitchen fellows suna ciki..." Yafada yana sh ha kitchen sai ya ha babu kowa, fitowa yayi ya tsaya rike da waist dinshi, ahankali ya juyo ya Kama hanyar dakinsu, unlike before dayake shiga anyhow yau knocking yayi a bakin kofar, ji yayi ance
"waye..." Haushi yaji ya amsa da
"Babanku né..." Ya amsa mata, da gudu binto ta bude kofa Jin muryar suhail, gaidashi sukayi amma bai amsa ba yace
"Cikin ku wacece murja?"" Ya tambayesu atakaice, da sauri murja tace
"Nice..."
"Come..." Ya fada yana juyawa, jikin na rawa murja tabi bayanshi, sai da yazo tsakiyar falo sannan ya tsaya ya juyo ya kalleta before saying
"Yauwa..Dan Allah taimako zakiyi min...inason ki je chan bangaren amaryar dad ki Kira Fatima...amma Dan Allah kar kice ni nike kiranta...kawai kice mata tazo wani Abu zaki nuna mata or better still tell her baba rabi ke kiranta...kinji..." Da sauri ta daga mashi Kai, zata juya yace
"Wait..." Tsayawa tayi shi kuma ya sa hannu cikin aljihunshi yana aduar Allah yasa yana da wani Abu ciki ya bata, luckily yana saka hannu ya samo wata 1k gud'a daya ya mika mata, da sauri ta girgiza Kai Tana cewa
"Barshi..." Bata idaba ya katse ta dacewa
"Dalla amsa banason gulma..." Ya daka mata tsawa, da sauri ta sa hannu Ta amsa sanna ta fita daga part din. Komawa yayi ya zauna yana tunanin
"What have I done ..," din gani yake murja zata fada mata he's the one calling her
"Aikam dana kashe shegiyar".." Ya fadawa kanshi.
Chapter 56 · 0% Book details