Sashe 89
Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 8 min read
ba. Hajiya kam tayi matukar mamakin abinda ke faruwa Don ita Sam bata yarda alhaji Mahmoud ya bawa Salman kudi ba, gani take mikinta ya bashi yake cewa alhaji Mahmoud, bataga tashin hankali ba sai da taji baba rabi da salima zasu hajj da umrah, rufe idanuwa tayi kan dole sai ya sake biya mata itama tunda shi ya biya masu yake fakewa da alhaji Mahmoud, shi ma alhaji tufe idanuwa yayi yace bai San wannan zancen ba, haka suka dinga rigima sosai, amma alhaji yaki saurara mata tunda yasan bai da hakkinta. Baba rabi kam baki har kunne sai godiya kawai take zubawa saboda farin ciki, itama salima abun ba'a magana Don bata taba tunanin zuwa hajj ba sai gashi har da umra. Duk surprise din sauran mutanen daban né Dana aliyu as he's thinking why alhaji Mahmoud zai biya Mashi hajj bayan ko haduwa or wani Abu bai taba hadasu ba, yana murna amma har da tsoro saboda yayi tunani har ya gaji ya rasa abinda yasa aka baki wannan daman, yaso yayi magana da suhail amma bai da international number dinshi Cikin tsananin farin ciki Maryam ta Isa gida, Tana parking ta fito Tana wakar Becky g Mai taken singing in the shower ta dinga rerawa Tana rawa ta shiga ciki, tunda ta dawo sai yau taji farin ciki mara misaltuwa, bata da gurin da ya wuce ta ga suhail jage jage cikin hawaye and duk efforts dinta bai taba aikin daya sata farin ciki kaman na yau ba, she can still see the look of disappointment a face dinshi, "What was he thinking?.." Ta fada Tana dariya "Oh..wait..yayi tunani da gaske nake when I hugged him?... Arrrhhh Kai banza né...uban me zai sa ni hada jiki da mugu irin ka if not for my own benefit..." Ta fada sounding so happy, hawan upstairs tayi sai waka take, Tana shiga dakinta ta dauki pillow ta rungume sannan ta fara ball dance dashi kaman mutum, happiness is written all over her, sai da tayi rawa ta gaji sannan ta wulla kanta kan kujera ta dauki wayarta ta Kira dad dinta ta sanar dashi she's back Don kar yayi tunanin taje wani wajen, wani sabon murmushi ta saki datayi tunanin wannan ma ya isa yayi ruining relationships dake tsakanin shi da dad dinta Don ko,kadan dad dinta baya tolerating rubbish, ajiyan zuciya ta saki tare da relaxing with both eyes closed. Suhail kam yana cikin kuka har suka isa station da za'a kaishi, abun mamakin shine yanda suke turashi ciki kaman wani hardened criminal, kanshi kasa sai hawaye kawai ke zuba, duk Wanda ya ganshi sai ya sake kallon shi for the second time suna tunanin why is a grown up man crying like a baby, wani waje aka ajiyeshi amma bai saga Kai ba balle yaga ya yanayin wajen yake, kawai yana tunanin Ashe haka Maryam ta tsaneshi, he can remember calling her thief, then gani yake in har Maryam will go to such lengths Don ta bata mashi just for maltreating her then in ta samu dama Tana iya kashe shi, he can still remember the joy da happiness dake face dinta, ya ga kallon resentment a idonta which makes him think she hates him to the moon and back, the most annoying part shine duk abinda tayi yau bai Chanza mashi komai game daita ba, he still feels for her, he wished yana iya cire sonta completely daga zuciyar shi da ba karamin dadi zaiji ba saboda gani yake shi kadai zai cigaba da Shan wahala tunda babu ko alamun likeness dinshi a idanuwanta balle so, ji yayi Ana tambayan shi amma ya kasa daga Kai balle ya amsa, duk tambayoyin da cop din keyi Mashi bai bada amsa ba, kawai shi tunanin shi shine ya alhaji Mahmoud zai kalleshi, Sannan bakin cikin shi shine tunda aka haifeshi bai taba zuwa police station ba amma yau gashi a station, station din ma na turawa and yasa ko,kadan turawa basu Kaunar bakar fata dukda he's not black. Yana ji akace "Take him to cell since he wants to make it hard on himself.." Yaji wani Yafada, wani irin fixga yaji anyi mashi kaman za'a yaga mashi riga, tafiya aka danyi dashi kadan sanna aka bude inda wasu detainees suke aka wulla shi ciki, gefe daya ya koma ya zauna kasa ya cigaba da kuka, yan sanda dake waje kallon shi kawai suke, wani daga cikin su da bai San abi da ya faru ba ya kura mashi Ido yana kallon Kayan dake jikinshi sanna ya kalli wayanda suka kamoshi ya tambayesu abinda yayi, nan aka fada mashi cewa shop lifter né, mutumin shuru yayi yana kallon yanda suhail ya hada Kai da gwiwa yana kuka Sannan ya sake kallon designer expensive clothes dake jikinshi yace "Are you sure about that?.." Ya tambayi Wanda suke magana, "He was caught rend handed..." Mutumin ya amsa mashi, shidai mutumin shuru yayi ya mike ya sake umarta a fito da suhail, fitowa yayi kanshi kasa, cikin natsuwa mutumin ya sake tambayan suhail ya fada mashi exactly what happened amma ko kadan suhail bai iya magana, mutumin kura mashi Ido yayi for a moment Sannan yace "It's obvious you're innocent but you don't want to vindicate yourself...we're going to let you go only if you tell us what happened..." Mutumin ya fada sounding so friendly amma suhail kasa daga Kai yayi, Banda goge face da bayan hannunshi babu abinda yake, Jin shurun yayi yawa yasa mutumin cewa "Then tell e why you have been crying..." Ya sake tambayan shi, ahankali suhail ya daga wet face dinshi ya kalleshi zai bude baki yayi magana sai kuma ya kasa, mutumin bai Kara forcing dinshi yayi magana ba yasa aka maidashi cikin cell, ji yake Kaman ya sallameshi ya tafi amma he can't do that without a statement from him. Haka sai ya mike ya bar wajen ya cigaba da wasu harkokinshi amma bai cikakken minti biyar bai zo ya gani ko suhail ya daina zubda hawaye ba. Maryam kadai yayi lunch kasancewan dad dinta bai dawo ba, hankalin ta kwance taci abincintq ta koshi ta koma dakinta tayi kwanciyar ta, ko kadan zancen tasan yanda zatayi game da situations data saka suhail bai dameta ba. Duk an gama duk wata arrangement na party dinta, an jera well decorated chairs a bayan gidansu, wajen Karfe biyar gown dinta ya iso, daman duk year dad dinta yakansa ayi mata special dress for her birthday, na wannan year din ma was fabulous, she loves so much, tsayawa tayi Tana kallon Kayan "Kai yau dadin yayi min yawa..."Ta fada cikin farin ciki. Karfe shida aka jera dinner lokacin dad dinta ya dawo, suna zaune kan dining suna cin abinci "Wannan yaron sai bai son cin abinci..." Inji alhaji Mahmoud, Maryam shuru tayi kaman bata ji abinda yace ba tacigaba da cin abincinta, bayan kaman minti biyu alhaji yasa aka Kira Mai sanar da lokacin cin abinci, nan alhaji ya tambayeta in ta shiga part din suhail ta kirashi, duk maganar da ake kan Maryam kasa Tana cin abincinta Don gurin ya kwana wajen kafin ya dawo gida bayan an gama birthday dinta, "He's not around.." Ta fadawa alhaji Mahmoud, da sauri Maryam ta kalli dad dinta Sannan tace "Dad waye?" Ta tambaya kaman batasan hirar da suke ba "Suhail mana...you mean duk maganar da nake baki ji ba?.." Alhaji ya tambayeta a little bit angry "Oh sorry dad...kawai abinda ya faru dazun né ya daure min Kai...Ta fada ciki sanyinmurya, da sauri alhaji yace "Me ya faru?.." "Dazun tare muka fita da suhail zuwa supermarket..." Tayi shuru tare da sadda Kai kasa Sannan ta karasa da cewa "Kawai sai aka kamashi yana shop lifting.." Bata idaba alhaji ya zaro idanuwa, "You mean suhail yayi shop lifting?.." Alhaji Mahmoud ya tambayeta Cikin matsanacin tashin hankali, Kai Maryam ta daga mashi "Subhanallahi...I don't believe that...Kai it's impossible.." Alhaji ya fada atakaice, Dan bata fuska Maryam tayi Sannan tace "Daddy gabana akayi..it happened just before my eyes..." Ta fada mashi, shuru alhaji Mahmoud yayi looking restless, bat rai yayi Sannan yace "Yanzu yana Ina?.." Ya tambayeta, Dan daga Kai tayi ta kalleshi Sannan ta sadda Kai kasa tace "Yan sanda sun tafi dashi,.." Idanuwa alhaji ya zaro tare dacewa "Kina hauka?..you mean police sun tafi dashi and you didn't bother to tell me?.." Ya fada cikin tsananin bacin rai, raurau Maryam tayi da idanuwa kaman zatayi kuka tace "Dads..what he did was wrong...so ka Bari ayi punishing dinshi,.." "Baki da hankali?... Baki ganin anything can happen?..ko kin manta inda muke né" ya tambayeta cike da bakin ciki, da sauri yasa aka dauko mashi waya, "Wane supermarket kukaje?.." Ya tambayeta, nan Ta fada mashi inda sukaje, yasan suhail will be near by police station, wani ya Kira ya fada mashi abinda ke faruwa, Maryam dake zaune bata rai tayi, marairacewa tayi tace "Dad ka Bari ayi punishing dinshi..it's a bad attitude to shop lift...at age dinshi.." Tafada sounding restless, ajiye waya alhaji yayi ya kalleta tare dacewa "Why zaki fadi hakan kaman you don't care?."" Ya tambayeta yana kallon idanuwanta, da sauri tace "Dad ba wai I don't care ba..amma ni abun kunyar da yayi fa?.. Am even ashamed to admit I know him right now..." Ta fada kanta kasa, alhaji kura mata Ido yayi yana mamakin me yasa take irin wannan maganar, abunda bata sani ba shine yasan duk abubuwan da ke faruwa tsakanin su which is yanda take shiga part dinshi da kuma yanda shima yake shiga part dinta kullum da safe, gani yake ko basu kwanciya tare da ba zasu rasa wani Dan Abu ba, at first yaso Jin haushin hakan amma sai yaga surveillance cameras ya nuna cewa wace gari da suhail yazo kasar ita ta fara zuwa part dinshi very early in the morning amma now she's sitting just in front of him showing she don't care, bai Kara cewa komai ba ya mike amma face dinshi Sam babu walwala. Sai da suhail ya gaji da hawaye Sannan suka daina fitowa Don kansu, nan I da yake zaune bacci ya fara daukar shi, wajen Karfe shida yaga har wannan lokacin nobody comes for him, dan daga idanuwanshi