← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 161 OF 190

Sashe 161

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 4 min read

Hajiya dakin ta tayi ta zauna Tana kallon suhail da yana bacci amma bai good 5 minutes sai ya saki ajiyan zuciya, ahankali ta Dora hannunta kan goshinshi Sannan ta maida kan heart dinshi  taji yana bugawa da karfi. Bayan kaman minti talatin ya bude idanuwa, kallonta yayi ya sakar mata murmushin karfi Hali,
"Mommy zanyi sallah..." Ya fada yana kokarin mikewa, ahankali ta Kama mashi hannu ya mike, Tana rike dashi har cikin bathroom, bayan ya fito ta shimfida mashi carpet, ahankali yayi sallah  ya koma ya kwanta nan kan carpet, sallama akayi bakin kofa hajiya ta amsa, murja ce tsaye tace
"Anty ce ta ce in kawowa suhail abinci..." Ta fadawa hajiya,
"Ki fada mata ta kawomin baby..." Inji suhail dake kwance, hajiya amsan Abincin tayi ta kawo kusa da in suhail yake kwance tace
"Eyeballs tashi kace abinci..." Ta fada mashi, ahankali yace
"Mommy I can't eat....I can't even try it...," ya amsa mata, da sauri ya girgiza tace
"Pls ka rufa min asiri kaci ko kadan né ...pls my love..." Ta fada mashi, idanuwa ya lumshe,
"Mommy I can't..." Ya sake amsa mata, sallama akayi bakin kofa hajiya ta amsa, salima ce rike da baby, ahankali ta shigo shi kuma suhail ya mike zaune wearing a smile, idanuwa Salima ta zaro Tana mamakin wane irin ciwo ya maida suhail haka,
"Anty..." Ya fada ahankali yana mika mata hannu, kasa magana  tayi ta taka ahankali ta mika mashi baby ya Dora a chest dinshi tare da lumshe idanuwa
"Meke damunka haka?.." Salima ta tambayeshi cikin karfin Hali, murmushi ya Dan saki yana cewa
"Anty rashin lafiya nayi..." Ya fada mata, 
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun...wane irin rashin lafiya kayi kuma mu bamu sani ba?.. Na shiga uku..." Salima ta fada cikin tsananin tashin hankali, shuru suhail yayi yana kallon baby dake hannunshi,
"Anty ya sunanta..." Ya tambayeta,
"Maryam..." Salima ta amsa mashi, shuru yayi yana kallon baby kaman bai taba ganin new born ba, ajiyan zuciya ya saki yace
"Allah ya raya..." Ya fada cikin sanyinmurya, Sannan ya mikawa Salima baban yana cewa
"Anty ya Maryam take...naji ance ta tafi..."bai karasa ba ya fara tari da karfi, da sauri hajiya ta mike ta daukoruwa amma kasa masa yayi yana tari, baki ya gumke kaman zaiyi amai hajiya tayi saurin tarba hannunta bakinshi Tana Shafa mashi baya, gudajin jini ya zuba mata cikin tafin hannunta, ihu hajiya ta saki Tana kallon hannunta, ha lokacin train bai sakeshi ba ya cigaba dayi da karfi, hannunshi kan heart dinshi, da sauri Salima ta sauka downstairs ta wuce dakin alhaji da gudu har baby dake hannunta Tana néman faduwa,
"Alhaji..ka zo...suhail nachan yana aman jini..." Ta fada mashi cikin tashin hankali, da gudu alhaji ya fita yana kiran masu gadi su taimaka mashi, suma upstairs sukayi da gudu kafin su iso suhail na kwance jini na fita daga cikin bakinshi ko nishi baiyi, hajiya sai ihu take, masu gadi da alhaji suka kama shi kaman gawa suka kaishi waje, babu abinda alhaji yake sai kuka, hajiya fita tayi daga part dinta ta fito waje taje wajen salima dake tsaye Tana kuka tace
"Dan Allah ki taimaka min da address din Maryam..." Ta fada cikin matsanacin kuka, mota alhaji ya shiga ya ja yana kiran Doctor, har suka isa hospital suhail bai numfashi sai jini dake fita daga bakin shi, emergency room aka wuce dashi, ko bata lokacin Doctor baiyi ba ya saka mashi oxygen,

"Anty Dan Allah ki Bari gobe mu tafi...Yanzu maraice yayi...kuma maiduguri da nisa..." Salima take fadawa hajiya bayan ta Kira Maryam ta fada mata address dinta,
"Ai ko Karfe biyun darene dole in tafi...banga ta zama ba..." Hajiya ta fada Tana tafiya da sauri, part dinta ta shiga Salima na biye daita,
"Nidai anty kiyi hakuri Dan Allah ...Yanzu suhail yana bukatar ki a asibiti...muje asibiti gobe da safe sai muje maiduguri..." Salima ta fadawa hajiya cikin rarrashi, da kyar Salima ta shawo kanta ta amince ta Bari sai da safe taje maiduguri. A hospital kam har dare suhail bai bude Ido ba Sannan baiyi numfashi ba, hajiya sai tambayan doctors take halin da yaje ciki kasancewan ba'a bar kowa ya shiga ba, alhaji me kawai zaune rike da hannunshi yana kuka, wayar alhaji né yayi ringing ya duba yaga alhaji Mahmoud, da sauri yayi piçking tare da sallama, alhaji Mahmoud najin voice dinshi yace
"Me ya sameka?.." Ya tambayeshi cikin tashin hankali saboda yanda alhaji Ismail yayi sallama yana kuka,
"It's suhail..." Alhaji Ismail ya fada yana kuka, cikin tashin hankali shugaba yace
"Suhail kuma?... What happened to him..." Ya tambayeshi,
" he came back today...he's seriously sick...Yanzu ma muna nan emergency unit ko numfashi baiyi...he's vomiting blood..." Ya fada mashi crying like a woman
"Subhanallah!!! Wane hospital kenan?..." Alhaji Mahmoud ya tambayeshi, nan alhaji Ismail ya fada mashi inda suke, bai Kara cewa komai ba ya katse wayarshi.

Vote wisely, let your vote count. May the best man wins.
52💚💙💛💜❤️
Wulakanci dodone...
❤️💜💚💛💙

® zuwairat (ummumaryam)

5️⃣2️⃣

Don't read if you didn't pay....
Chapter 161 · 0% Book details