← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 190

Sashe 96

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 8 min read

Baya shigar dakaman minti talatin dad dinta ya shigo, tunda suke tare bata taba ganin face dinshi haka ba, da sauri ta mike zaune ta sha jinin jikinta saboda fargaba tasan babu duka babu zagi but he's good in handling people, 
" Inason ki fadamin gaskiya..ke kikayi setting dinshi up?..." Ya tambayeta fuskar shi kaman bai taba dariya ba, Dan ja baya tayi idanuwanta na taruwa da hawaye tace
"Yes..." Da Sauri alhaji ya daga Kai ya kalleta Wanda yasa ta Kara Jin tsoro saboda yanda idanuwanshi suka sauya,
"Wato irin tarbiyar da na kashe millions of naira Don  ki samu kenan?...  Karya?.." Ya fada babu ihu babu dagin murya, da sauri tace
"So nake na rama..abinda.,yayi min..." Ta fada cikin fargaba that is written all over her face, wani irin kallon banza ya watsa mata sanna yace
"Wane irin abune zaki Rama da framing mutum as barawo in a foreign country like wannan ..bayan kinsan halin mutanen nan...wane irin rashin hankali né wannan.." Ya daka mata tsawa, da sauri jikinta ya fara rawa, Kara ja da baya tayi sanna tace
"Dad..shine...yake zaluntata ...." Bata karasa ba ya sake cewa
"Wane irin zalunta zaisa ki yiwa Dan mutane kazafi?... Maryam Sam ba irin tarbiyar Dana baki bane..,Wallahi in dai ban Riga na bude baki nayice next year zakiyi aure ba da yau din nan sai nayi maki aure...amma am a man of my word...and fushi dake bazai sa in chnzan halina ba..but Yanzu ki tashi ki kwashe kayanki...zaki koma Nigeria...Yanzu nan..." Da sauri Maryam ta fara yarfa hannuwa Tana kuka Tana cewa
"Dad kayi hakuri..Wallahi bazan Kara ba...pls daddy forgive me..I promise I will be a good girl...Dan Allah dad..., " ya fada cikin matsanacin kuka, ko kallonta baiyi ba ya fita yana cewa
"Indai har polygamy a iso baki shirya ba then a haka zaki tafi...the choice is yours..." Ya fad'a mata Sannan ya fice daga dakinta. Maryam lika kanta da kasa ta farayi Tana bullayi a kasa, kawai she hate herself and not suhail, ji taka kaman tayi committing sucide ta Huta saboda yanda take Jin zuciyar ta.

Alhaji na fita yasa aka Kira mashi suhail, suhail  na zuwa alhaji ya nuna mashi waje ya zauna Sannan yayi shuru for a moment before saying
"Dalilin dayasa na kiraka shine Don in Baka hakuri...bansan abinda ya hadaku da take cewa she was trying to revenge ba amma kalin sata ba abunyi bane...in Baka yafe ba Allah sai ya saka maka..so Dan Allah kayi hakuri..." Sadda Kai suhail yayi yace
"Ba komai..." Ya fada yana mamakin irin halin wannan bawan Allah,
"Tou nagode..abu ma biyu shine Inason tambaya if you can manage company in Dubai..." Ya tambayeshi Kai tsaye, da sauri suhail ya kalleshi tare da daga mashi kai yana cewa
"Yes sir.." Ya fada duk jikinshi na rawa,
"Good then...zan bar company din a hannunka zuwa shekara daya...bazan duba komai ko insa ayi wata bincike ba sai nan da shekara daya in Allah yasa muna da rai...the result shi zai tabbatar if you're capable of being the manager or mere staff...so congratulations...you're officially the manager of maryama group of Companies Dubai brand..." Ya fada yana mika mashi hannu amma ko kadan face dinshi babu wata walwa, da sauri suhail ya mike ya zo inda alhaji ke zaune ya mika mashi hannu tare da durkusawa,,
"Koma seat Dinka..." Alhaji ya umarce shi, da sauri suhail ya koma ya zauna duk ilahirn jikin shi na rawa, alhaji yacigaba dacewa
"Da zan so daga nan ka wuce chan..but nasan bazaka rasa one or two things da zaka kimsa ba...Don haka yau zaku koma Nigeria...sai ka shirya nan da sati biyu zaka wuce chan.." Inji alhaji Mahmoud, suhail sadda Kai kasa yayi not knowing what to say,
"Ko hakan bai yi maka ba?.." Inji alhaji Mahmoud, da sauri suhail yace
"Yayi sir..."
"Very good...then kaje ka shirya..jet will be here soon...and Abu na karshe...ka rike amanata tamkar yanda dad Dinka ya rikemin amana...banason ka fadwa kowa ko Maryam wacece...keeps this a secret..."
"Ok sir..." Ya fada with cracking voice,
"Good ka tashi ka shirya kayanka..." Ya umarce shi, da sauri sauya  tashi ya bar waje, yana fita ya fara daka tsalle, he can't just believe zaiyi aiki international organizations, yayi filling forms na abroad company yafi a irga amma yau sai gashi a saukake ya samu, tunawa yayi na statement din alhaji da yake cewa zasu koma Nigeria alaman ba shi kadai zai koma ba Tare zasu koma da Maryam, tsayawa yayi chak Kaman ya tuna wani Abu,
"Oh my gosh...ya zanyi da rashin Maryam?... " ya tsaya yana tambayan kanshi kaman he just remembered her
"Dubai dai is not close to home" ya fada yana tafiya,
"Kan ni kam ya zanyi da baby na...kam can't survive without you..." Ya fada, da sauri ya shiga part dinshi ya dauki wata bag na puma ya jera Kayan da alhaji ya siya mashi ciki da su perfumes da sauransu Sannan ya shiga wanka. Itama Maryam Tana kuka tayi wanka Don tasan ko kukan jini zatayi bai hana dad dinta abinda yayi niyya yi, Tana fitowa daga bathroom ta dauki bag ta saka laptop dinta da wayoyinta Don boredom ya kusa kasheta last time, Tana gama wa ta yaye duk Kayan Shafanta da sauran abubuwa, ko daya bata dauki sutura ba, doguwar Riga ta saka ta dauki hijab datazo dashi ta saka,  fuskar ta cike da hawaye ta sauka ta shiga kitchen Tana yiwa masu aiki bankwana. Bayan kaman minti ashirin jet ya iso, babu wasting of time suhail ya fito rike da bag dinshi, ji yake inama yana iya tura part dinshi cikin bag ya tafi daita Nigeria Don he's going to miss the apartment sosai. Yana fitowa itama Maryam tafito kanta kasa Sannan duk masu aikin gidan suna biye daita sai dad dinta daga gefe daya, he can see she's crying, alhaji Mahmoud né ya fito ya mikawa suhail hannu suka gaisa again Sannan ya warewa Maryam hannu ta fada jikinshi, magana ya rada mata a kunne ta daga mashi Kai alaman ok Sannan suka hau jirgi, waving dinta masu aiki suka dingayi har ta bace masu, suhail relaxing yayi yana sauke ajiyan zuciya Sannan yana tunawa da maganar alhaji Mahmoud, Dan daga Kai yayi ya kalli yanda Maryam ta kame waje guda kaman ba ita ba,
"Sawa a daukoka was my biggest mistake..." Ta furta ahankali, Dan murmushi ya saki Sannan yace
"Ni kuma it's the best thing that ever happened to me..." Yafada yana kallon yanda hawaye ke fita idonta, ahankali ya mike ya koma kusa da ita ya zauna seat dake kallon nata ya kamo hannunta da sauri ta fixge Tana hawaye, hannu yasa ya goge dace dinta sai buge mashi hannu take alaman ya daina amma bai saurara mata ba ya dinga gobe duk tears dake fita idonta, hannunta ya sake kamawa ta kwace ya sake kamawa, haka suka dingayi har ta hakura. Few minutes later ya koma kusa daita shima turashi ta dingayi har da cewa
"Ka tashi tunda ba jet din ubanka bane..." Amma ko ajikinshi, daga karshe Dora kanta tayi kan shoulder dinshi Tasha kukanta Sannan bacci yayi gaba daita.

The following day, suhail ne ya fito daga part dins sanye da three quarters na Jean sai polo, da ganin shi bai dade da tashi daga bacci ba, kallon compound dinsu yayi sai yaga gidan kaman gidan kaji compared to gidansu Maryam, ahankali ya taka ya shiga part din mum dinshi kasancewan yau Saturday bata zuwa office sai indai an samu emergency, yana shiga falonta yaga baba rabi na goge because basu kaiga tafiya hajj ba, kusa daita ya zo yace
"Baba ina kwana?.." Ya gaisheta, da sauri baba rabi ta daga Kant Don ko kadan she didn't believe what she just heard, kallon kawai take bata amsa ba Don gani take ba daidai taji na, Dan murmushi ya saki ya sake gaida ta, da sauri ta amsa Tana kallon shi with her eyes out, dariya yayi  yace
"Baba ya dai..." Ya tambayeta yana dariya, da sauri tace
"Ba komai..." Shuru ya danyi yana son yayi mata magana amma ya rasa what to say, tsaye yayi ya magana sanna kuma bai bar wajen ba, murja ce ta fito binto na biye daita, sun nufi dining da manyan food warmer dake hannunsu, da sauri suka durkusa suka gaisheshi,
"Ku tashi tsaye mana...daga yau ku bar durkusa min..kunji kou.." Ya fada masu Kai tsaye, da sauri suka daga mashi Kai alaman eh,  kaman zai hau upstairs sai kuma ya tsaya yana kallon su suna jera abinci kan dining, sai sauri suke ya kuma San duk saboda shi né,
"Ku nawa né ke aiki nan cikin gidan?.." Ya tambayesu, da sauri murja tace
"Mu hudu.." Ta amsa mashi jiki na rawa, kallon kujerun dining yayi yaga takwas,
"To daga yau ku dinga cin abinci kan dining...mu dinga ci tare...kar in kuskura inga mutum yana cin abinci cikin kitchen, kitchen ba wurin cin abinci bane..wurin dafa abinci né ..kunji kou?.." Da sauri suka amsa da eh,
"Ina Dayan take?.." Ya tambayi murja, amsashi  mashi tayi da Tana kitchen
"Ki kirawota..." Ya fada mata, da sauri murta shiga kitchen ta kirawo asabe, hanyar falo yabi ya zauna ya umarce su karaso, suma zuwa sukayi suka zauna kasa ya ce su zauna kan kujera har da baba rabi, duk zama sukayi ya je gaban baba rabi ya durkusa, zai bude baki yayi magana yaga hajiya tsaye bakin stairs fuskar ta kaman bata taba dariya ba.

Manage, am so occupied,
32💜💚💛❤️💙
Wulakanci dodone...
💚💙❤️💛💜

®zuwairat (ummumaryam)

3️⃣2️⃣

Don't read if you didn't pay, strictly for those that paid.
Chapter 96 · 0% Book details