← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 190

Sashe 33

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 6 min read

Maryam kam har lokacin Tana kwance bata San inda take ba Don tunda aka haifeta bata tabajin irin azabar da ta ji lokacin da hajiya ta sakar nata wannan sarkar a jikinta ba.
Ana kiran alhaji ya dauki motar company ya Kama hanyar gida, dukda ac sake cikin motan babu abinda yake sai zufa, Doctor yakira ya shaida mashi abinda ke faruwa, yana zuwa bakin gate ya saki horn da karfi, da gudu Salman dake zaune baki gate yayi tagumi ya mike ya bude mashi gate, motar shi na shiga na Doctor na shigowa, da gudu alhaji ya fita daga cikin mota adaidai lokacin da suhail ya fito babu Riga jikinshi sannan hannunshi sai zubar jikin kawai yake, kallo alhaji da doctor tare da Salman dake tsaye bakin gate suka bishi dashi, amma ko kallon inda suke baiyi ba ya wuce,
"Dan ubanka me kuka yiwa yar mutane?.." Alhaji ya tambayeshi, bai daga Kai ba ya wuce kawai shi kuma alhaji ya wuce falo jikinshi na rawa shi kuma Doctor na biye dashi,   Dakin Maryam suka wuce, Han gado alhaji ya tarda Maryam, sai su baba rabi dake taaye gefen gadon,
"Inna lillahi waina ilaihi rajuun!!!" Alhaji ya furta yana kallon yanda tsawun bulala ke kwance kan farar fatar Maryam, Doctor kam bai bata lokacin ba ya Kama hannunta yana duba vital signs, shi Kam alhaji zama yayi bakin gado ya hada Kai da gwiwa yana karkada Kai ahankali, yasan wannan Karin asiri shi ba zai taba rufuwa wajen alhaji Mahmoud ba, inshort gani yake he has loose  everything already Don yasan babu abinda zai Hana alhaji Mahmoud daukar mummunar mataki kan abinda ya faru Don he will do the same. Doctor kallon su baba rabi yayi ya umarce su da su samo mashi ruwa,
"Is she going to be ok?..." Alhaji ya tambayi Doctor muryar shi na rawa,
"Yes she's just traumatized...she will be alright." Doctor ya shaida mashi, ahankali alhaji a mike ya fita daga dakin,
Upstairs ya hau  ya shiga dakin hajiya, Tana zaune kan kujera Tana hawaye, alhaji karewa dakin kallo yayi Itakuma ko daga Kai batayi ba balle ta kalleshi, jinin dake kasa ya kalla sannan ya kalli hajiya yace
"Sumayya na sakeki saki daya..." Ya fada atakaice.
[11/28, 3:16 AM] ‪+234 706 639 9737‬: 14💜💚💙❤️💛
Wulakanci dodone
💛💙❤️💜💚

®zuwairat (ummumaryam)

1️⃣4️⃣

Jiki na rawa hajiya ta mike tsaye Tana cewa
My alhaji...what did you...say?..." Ta fada muryar ta na rawa, fuskar alhaji daure yace
"In na Maimaita ya zama biyu kenan...ko in Maimaita?..." Ya tambayeta Kai tsaye, da sauri hajiya ta rike gaban rigar shi Tana cewa
"Inna lillahi waina ilaihi rajuun!.. My alhaji this is not us...yau ni kake furtawa irin wannan kalaman...ni sumayya kake cewa ka saka...sai Yanzu na gane mission din yarinyan nan gidan nan...she came to ruin my joy and happiness...ta mallakemin d'a sannan Kaima ta mallakeka...wake up..." Ta fada Tana girgiza shi da karfi, alhaji tsayawa kawai yayi yana kallon ta, deep down he's not happy yanda ta koma daga Daren jiya zuwa yau amma ya zama Dali ya hukunta ta kan abinda ta aikata,
"It not because of her...it because of your character...wallahi ko d'ana kika yiwa haka ba zan kyale ki ba balle yarinyar da take amana wajena..." Bai idaba hajiya ta katse shi dacewa
"I don't care...I don't care .!!" Ta fada da karfi Tana Kara rike gaban rigar shi, hannu yasa ya Kama hannunta Don kwace rigar yana cewa
"Am not going back on my words....zan nemeki..." Ya fada yana fixge rigar shi daga hannunta, Kara kamawa tayi Sannan tace
"Bazai taba yuwa kayi disgracing Dina at my age ba..."
"Age dinki na banza!..you don't act according to ur age Don in da kina amfani da shekarunki wasu abubuwan bazaki taba aikata su ba..." Alhaji ya fada sounding very angry,
"Ni kake cewa haka....me your hajiya .." Ta fada cikin matsanacin kuka, sake fixge Kayan shi yayi ya Kama hanyan fita yana cewa
"Just go...I will contact u..." Ya fada mata, cikin kuka tace
"Wallahi babu inda zani...at my age zakace in tafi,...Ina zani?... Tou sai dai Kai da wannan shegiyar yarinyar ku bar gidan nan..." Hajiya ta fada Tana durkusawa Sannan Tana kuka. Banza alhaji yayi daita ya koma downstairs, yana shiga dakin yaga har Maryam ta farka Tana zaune bakin gado ta saka riga sai sauke ajiyan zuciya kawai take yayin da hawaye na zubowa daga idanuwanta, alhaji na shigowa tayi sauri mikewa Ta fada jikinshi Tana kuka tare dacewa
"pls sir....what's my ..offense..." Shine tambayan data yi mashi muryar ta na rawa da duk ilahirin jikinta, ahankali Alhaji ya tallabo fuskar ta ya yana kallon yace
"Daughter am so sorry....baki da laifin komai...kawai zulunci ne...." , cikin kuka Maryam tace
"Sir I don't want to stay here...pls I want to go...Dan Allah ka fadawa dadina ya maidani gida...am not use to violence...I might die plsss.." Ta shaida mashi cikin matsanacin kuka, hawayen fuskar ta yasa hannu ya goge sannan yace
"Don't worry...I will take u way daga nan gidan...is that ok by you?.." Ya tambayeta, ahankali ta girgiza Kai
"No...I want to go to my dad...pls sir..." Ta amsa mashi still crying, hannu ya Dora kan shoulder dinta tayi saurin cewa
"Washhhh...." Da sauri alhaji ya sauke hannunshi,
"Pls daughter give me a last chance....let me take you out of here...saboda  ke zan auro sabuwar mata...kawai Don ta kula dake...Dan Allah daughter ki rufamin asiri kaman ya da Allah ya rufa maki....in har dad dinki Yaji wannan abun na shiga uku...Dan Allah kiyi hakuri..." Alhaji ya karasa maganar kaman zaiyi kuka, ahankali Maryam ta dan share hawayen ta Sannan tace
"Ok...you're a good person...but I don't want to stay here.....pls take me away.." Da sauri alhaji ya gyad'a mata Kai,
"That's my daughter....thank you..nagode da yanda kike rufamin asiri...Allah ya biyaki..." Ya fada, Doctor dake zaune yana sauraron su ya mikawa alhaji prescription script tare dacewa
"Ta sha Don kar sawun bulalar su koma ciwo Don fatar ta bashi da kwari..." Ya shaidawa alhaji deep down yana tunanin hirar Maryam da alhaji, yana mamakin ko ita wacece da alhaji ke néman ta rufa mashi asiri amma bai ce komai ba ya mike, Maryam Tana tafiya kaman wacce akayiwa targade ta koma ta zauna amma bat bar hawaye ba, Doctor fita yayi shima alhaji yabi bayanshi. Yana zuwa falo ya kwalawa baba rabi Kira kasancewan sun bar dakin, da gudu ta fito duk jikinta babu kwari saboda abinda taga hajiya tayiwa Maryam, Tana zuwa ta Dan runtsuna Sannan tace
"Gani alhaji..."
"Kije dakin Fatima ki tattara kayanta da naki zaku koma chan gidan...Sannan kar ki fadawa kowa inda zaku...." Ya fada mata Don Yanzu yana son tsaron Maryam saboda gani yake hajiya Tana iya Sa a kashe ta saboda kishi,
"Tou rankashi dade..." Ta fada Sannan ta shiga dakin Maryam.
Chapter 33 · 0% Book details